36

116 10 0
                                    

*LULLUƁIN BIRI*

*36*
Allah kaɗai ya kaisa lafiya zuwa Asibitin Miyetti saboda irin mahaukacin gudun da yake yi, yana isa asibitin direct office ɗin Dr Yusuf ya faɗa, yanda yake a matuƙar rikice haka shima Dr Yusuf ɗin yake.
yana ta aikin sauke numfashin yake kallon Dr Yusuf idonsa tamkar zai faɗo yace,"tana ina Dr?, a wanne hali ta-ke ciki?".

Dr Yusuf yaja dogon numfashi ya sauke, ya rufe idonsa for a while sannan ya buɗe ya sauke su akan Turaki yace,"an shiga da ita situation room, and she is in critical condition, wanda yake da kamar wuya...".
"da kamar wuya me?". Turaki ya faɗa cikin ɗaga murya a sanda Dr Yusuf yay shiru da maganar da yake, ya zagayo ta gabansa a firgice yana daɗa cewa,"kaci gaba da min bayani Dr, da kamar wuya me?".

Dr Yusuf ya kalli gefe guda tsananin damuwarsa da tashin hankalinsa na ƙara bayyanuwa yace,"da kamar wuya ta rayu".
Turaki get in to a state of shocked, looking at Dr Yusuf with anxiety, like he did'nt understand what he said, ya buɗe baki zai yi magana Dr Yusuf ya dafa kafaɗarsa yace,"abinda yake nan shi nake sanar maka, bance ba zata rayu ba, but da kamar wuya tayi rai".

cikin wani bala'in tashin hankalin da yafi na ɓarawon da aka kama Turaki ya damƙe hannun Dr, sai kuma a hankali kuma cikin mutuwar jiki yace,"Dan Allah Dr ta rayu, na roƙe ka dan Allah, ko menene kayi dan ta rayu ni kuma nayi maka alƙawarin duk abinda ka biɗa daga gare ni muddin bai fi ƙarfina ba zan baka, amma dan darajan Allah karka bari ta mutu".
yanda yayi maganar dole yay mugu mugun baka tausayi.
Dr Yusuf yace,"Allah ne kaɗai me rayawa da kashewa, zamu yi iya kar bakin ƙoƙarinmu wajen ganin mun ceto ranta, saboda gaskiya akwai matsala babba ma kuwa".

Jikin Turaki ya ƙara mutuwa, yaji zuciyarsa na wani irin motsawa yana jin kamar ya mutu ya huta. yace,"wacce matsalace da har zata fi ƙarfin ku Dr?".
Dr Yusuf yace,"a binciken da muka yi akwai abinda ya gigitata ya kuma ɗimautata da har yaja a lokaci ɗaya zuciyarta ta taɓu, kuma ta kai ga matakin ƙarshe na stage d, yana zama da wuya akai wannan matakin kaga an rayu sai dai kuma wani iko na ubangiji. yanzu fatan da zamu yi guda ɗaya shine in har Allah yasa ta farka to karta farka da tunanin wannan abin da ya girgizata ya haddasa taɓa zuciyarta a lokaci ɗaya, idan har hakan kuma ta kasance to tabbas farkarkawarta bugawar zuciyarta gaba ɗaya, daga nan kuma shikenan tata ta ƙare".

ƙwayar idon Turaki ta kaɗai, yaja da baya ya tafi yana neman madafa saboda jinsa da yake yana neman yanke jiki ya faɗi, yay saurin dafe bango yana kifa kansa ajikin bangon yana jin jikinsa gaba ɗaya ya ɗau shaking.
bai san me yake ji ba, bai san ta yanda zai kwantata yanda yake ji ba, haka bai san halin da yake ƙoƙarin shiga ba.
Dr Yusuf yayo tattaki yazo kusa da shi ya tsaya tare da dafa kafaɗarsa yace,"yanzu taimako guda ɗaya ta-ke da buƙata a wurin mu shine jini...".
tun bai ƙarasa bayaninsa ba Turaki ya damƙi hannunsa suka nufi hanyar fita, cikin gaggawa suka fito a tare suka nufa situation room ɗin da Fillo ta-ke.

tana kwance kamar gawa, kallo ɗaya Turaki yayi mata ya kasa dauriyar riƙe hawayen dake cikin idonsa, kawai ya sake su suka sauko, kamar ba namiji ba, kamar ba jarumi ba, hawaye yake sosai kuma masu zafin gaske waɗanda yake jin zafinsu tamkar zasu ƙona fatarsa, gwargwadon irin zafin da yake ji a zuciyarsa wadda shima yake jin tana gab da taɓuwa.
yasa hannu kamar ƙaramin yaro ya shiga goge hawayen sannan ya kwanta akan gadon da Dr Yusuf ya nuna masa, muryarsa ta fito da wani amon sauti da ba nasa ba yace,"in har da buƙata a kwashe duka jinina a saka mata".
Dr Yusuf yay guntun murmushi ganin kamar Turaki ya zauce, yaji tausayinsa matuƙa kamar yanda shima yake tausayin kansa. kuma nan da nan akayi connecting jinin Turaki zuwa jikin Fillo.

tun jonawar ya juyar da fuskarsa zuwa kan gadon da ta-ke, lokacin an samu gogge jinin duk da ya ɓata mata jiki, kallonta yake tayi yana mai matuƙar tausayinta a cikin ransa, yana kuma lissafin cewar da zarar ta farka komai na wahalarta yazo ƙarshe, zai zamar mata bango kuma jigo na madafarta.

LULLUƁIN BIRI completeWhere stories live. Discover now