*LULLUƁIN BIRI*
*51*
sai da aka fara kiran sallar magriba tukunna Turaki ya iya zame Fillo daga jikinsa, sanin cewa ba sallah zata yi ba kawai yaja blanket ya rufeta, yay kissing forehead nata sannan ya fita, yana zuwa ɗakinsa yay alwala ya wuce masallaci.
a masallaci ya zauna har sai da akayi sallar isha'i tukunna ya dawo, for the first dawowarsa gida bai wuce ɗakinsa ba kai tsaye, bedroom ɗin Fillo ya wuce, yana shiga ya tarar har yanzu bacci take yi, ya girgiza kansa yana mamakin irin baccinta.durƙusawa yayi a gaban gadon yana yaye blanket ɗin ya kamo hannunta, ɗayan kuma yana shafa fuskarta sai kallonta yake yana murmushi, fuskar baccin nata kaɗai ya isa ya shaida maka rigimammiya ce, haɗe gefen fuskarsa da tata yayi, ya lumshe idonsa for some minutes ya buɗe, yasa hannu yana jan hancinta yace,"Fulani nah baccin ya isa haka".
ta buɗe idonta a hankali, cikin baccin da yake cinta ta dube shi ta mayar da murfin idon ta rufe tana juya masa baya. murmushi yay ya miƙe tare da hawa gadon ya cicciɓeta ya fita da ita zuwa ɗakinsa.
direta yay a ƙasa yana kama hannayenta ya ɗaga sama, sak irin yacca akewa ƙanan yara idan za'a tashe su, ta buɗe lumsassun idanuwanta ta kalle shi tana sakin kukan shagwaɓa,"ni fa bacci nake ji".
ya rumgumeta yana kwaikwayon muryarta shi ma yace,"ni kuma i want you to wake up, kin barni ni ɗaya i feel lonely, ki tashi ko rigima ce muyi".haka yay ta damunta har sai da ta wartsake tukunna ya ƙyaleta, ya kama hannunta suka isa wajen gado, ya zauna a gefe yana ƙoƙarin ɗorata a saman cinyarsa sai taƙi, taƙi zaman becose she is not feeling comportable saboda period ɗin da take ciki, tana jin ma kamar tayi staining.
"mene amfanin ƙafafun nawa idan ba ki zauna akai ba?".
ta ɗan kauda fuska tace,"ɗaki zanje".yaja hannunta har sai da ta juyo ta kalle shi yace,"nan ba ɗaki ba ne?".
"to ai toilet zan shiga".
ya miƙe tsaye yana faɗin,"nan ma ai akwai toilet ɗin, muje let me escort you".ya faɗa yana kama hannunta zuwa toilet, sai ta maƙale a bayansa taƙi shiga, ya janyota zuwa gabansa yana kallonta, ta kifa kai akan cikinsa tana cewa,"ni toilet ɗina ba wannan ba, ina so zanyi wanka".
ya ce,"nan ma ai ana wankan".
tasa taɓara,"ni ba wannan ba to, nawa zanje please leave me".ta faɗa tana ta maƙalewa a bayansa, bai kulata ba ya buɗe toilet ɗin suka shiga ciki duk da faman tirjewan da take yi, tana kallo ya kunna ruwa a bathtube har sai da ya cika sannan ya dawo da idonsa kanta, su na haɗa ido ta ɓoye fuska a bayansa, ya juyo da fuskartata yana cewa,"kiyi wankan anan".
sai ta shiga dukan ƙafafu a ƙasa cike da kukan shagwaɓar da ke neman juyewa zuwa na gaske tace,"to ai..".
ya katse maganartata ta hanyar ɗora yatsansa saman lips ɗinta,"ba na son musu, kiyi anan nace".tayi narai-narai da idanu hawaye na sakko mata tace,"to ai zan ɗauko abu ne".
bai kulata ba ya janyo towel ya bata,"ko kiyi da kanki ko nayi miki".
ta saurin karɓa ba tare da ta yarda ta kalle shi ba.
"zan ɗauko miki ko me kike buƙata".ya faɗa yana sakin hannunta, yana ganin yacca take ɓata fuska, bai tsaya sauraronta ba ya fita ya rufe mata ƙofar.
tana ta faman ɓata rai tayi wankan, idonta duk ya taru da ruwan hawaye ƙiris yake jira ya zuba, ita fa kawai saboda ya kira mata Umminta ta yarda suka shirya, shi ne zai wani kawota toilet ɗinsa yace tayi wanka.
sai bayan ta gama wanka ne sannan ta ɗaga towel ɗin zata ɗaura, sai ta gan shi ɗan ƙarami sai kace ɗan kwali kwatan yadi, idonta ya haska mata tana fita da wannan ɗan ƙaramin abun shi kuma yana ɗakin a zaune, sai kawai ta turo baki gaba tana kifa kai da bango ta saka kuka.