55

114 6 0
                                    

*LULLUƁIN BIRI*

*55*
kiran sallar farko a kunnen Fillo, tana buɗe ido ta ganta a inda saɓanin Mafarkinta ya nuna ma ta.
ta ɓata fuska tana jin kamar tayi kuka, wayar Baffayo da ke gefen pillow ta ɗauko, adu'arta ɗaya Allah yasa babu pin a jiki, cikin sa'a kuma tana dubawa taga babu, don haka da sauri ta shiga message tayi typing text kamar haka.

_I don't just miss you, i miss the warmth in your breath, depth in your eyes, the touch of your fingers, and feeling your hands on my waist. I miss you truly and deeply._

after ta gama rubutawan kuma sai ta kasa sending, ta tsaya tana tunani, kunyar turawar takeyi, ta zuro ƙafafunta ƙasa daga kan gadon kamar wacca zata yi kuka, har sai da Hamida ta buɗe ido ta tambayeta,"Asiraawo lafiya?".

"yi haƙuri na tashe ki, ji nayi kamar wani abu na bina ne, ashe zaren jikin rigata ne".
Hamida tayi murmushi kawai tare da komawa ta kwanta, don ita kanta ta fahimci tana cikin kewar mijinta ne, duk da tana da nauyin bacci but tana jinta sai faman juyi take.

Fillo ta tura text ɗin sannan ta wuce toilet ta yo alwala ta fito, har ta idda sallar asuba bata ga reply ɗin Turaki ba kamar yanda tayi tsammani. duk sai taji babu daɗi, may be ko text ɗin ne bai yi masa ba, ko kuma abin da ta tura ɗin ne bai dace ba, duk sai taji ta kasa komawa baccin da yake so ya ɗauketa.

da safe wajen ƙarfe tara after sun gama breakfast, taji su na waya shi da Mum har take tambayarsa jikin Maama, tai ta jin kamar tace da Mum ta bata wayar, kewar muryarsa take yi kamar ta shekara dubu ɗari bata ji ba.
kuma bayan sun gama wayar da Mum a tunaninta ko zai kirata a wayar Baffayo sai taga har ƙarfe tara bai kira ba, sai taji kamar ta fara fushi da shi, but haka ta ƙara ɗaukar wayar ta ƙara tura masa text.
_The thought of you makes me smile, but the distance we share makes my heart ache. I am missing everything about you. I wish you were here Turaki._

ta tura da yaƙinin cewa a wannan lokacin zai dawo ma ta da reply tunda dai tasan yanzu wayarsa na hannunsa, but sai ta ƙara jin shiru, idonta ya ciko da ruwan ƙwalla ta ƙara tura masa text.
_kuma ba zan dawo gidan ba._

tana turawa ta ɗauki wayar ta fita ta kaiwa Baffayo, har ya tambayeta ta gama ne tace masa ehh ko ya kira ma ba sai ya kawo ma ta ba.
ta koma ciki ta shirya kamar yanda Mum ta umarceta don za su fara zagayen gaishe-gaishen ƴan uwa.

to acikin kwana biyu dai Fillo sai taji tamkar an sakata a kurkuku, mugun bala'in kewar Turaki take yi, har wata rama tayi ka rantse bata da lafiya, duk dare in zata kwanta sai tayi hawaye, ta riga ta saba da kwanciya a jikinsa, wannan ƙamshin jikin nasa, wannan ɗumin jikin nasa da ɗumin iskar bakinsa me ƙamshin min, wannan cairing ɗin nasa da soyayyarsa.

tun ranar da suka zo bata ƙara jin muryarsa ba, yau da safe ya kira Baffayo ya kawo mata waya amma da ta karɓa sai ta kashe kiran, yay ta kira taƙi ɗagawa ita alallai tayi zuciya tun da ranar nan duk yana kallon messges ɗinta bai yi ma ta reply ba.
wasa wasa dai sai taga ina ba zata iya yin har 7days ba, gida kawai take so ta koma, wurin Turakinta, tana missing late-night talk ɗin su, tana kewar precious smile ɗin sa, she want nothing except his presence around her, being away from him in this 4days she feels like being caged for a lifetime in misery.

a daddafe ta iya kwana biyar ɗin da suka yi, tuni ta fara cutar ƙarya me zafi ta yanda dole su tarkata su koma gida, hakan kuwa akayi, da Mum taga jikinta yay worst sosai musamman da taga kamar har da iskokinta dole suka ɗauko hanya a ranar.
sai ga su ƙarfe biyar na yamma sun sauka, don jirgi su ka biyo saboda Granny tace ba lallai Fillon ta iya jurar zaman mota ba, kuma su na dira a gombe taji ta warware daga cutar da ta fara kamata.

Zaytuna ce tazo ta ɗauke su a airport, duk tunaninta gidanta za'a wuce da ita but sai taga sun yi gidan su Turaki, ba haka ta so ba sam, yacca ta so ta koma gida ko da ace bata same shi yana nan ba, to da ya dawo ya zama yay tozali da ita.

LULLUƁIN BIRI completeWhere stories live. Discover now