15

111 10 3
                                    

*LULLUƁIN BIRI*

*©️Halima h.z*

_nace muku i love you ko na bar kayata?...kai aradu sai na faɗa ko me xaku yi sai dai kuyi😏, idan na faɗa sai na ruga da gudu yanda ba zaku iya kamani ba😝...nace ba *I LOVE YOU MY FANS* 🏃‍♀._

*15*
tunda taga Turaki ne ke tunkarota tayi ƙasa da kanta, ta shiga wasa da hannunta, haka kawai kuma sai ta tsinci kanta da mugun faɗuwar gaba, saboda haka a hankali ta shiga karanto innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, hasbunallahu wani'imal wakil.
_laifin me ta aikata?._ shine tambayar dake yawo acikin ranta, dan ita dai ta sa ni tsawon lokacin da ta ɗauka a gidan nan bai taɓa ambatar sunanta ba, to amma yau kiran nata na menene?.

tana cikin wannan saƙe-saƙen yazo ya wuce ta gefenta, ta ɗaga kai tabi bayansa da kallo tana ganinsa har ya shige part ɗin Boɗejo, sai a sannan ta sauke ajiyar zuciya me nauyi.
maganar Khalil da ta ƙaraji a gabanta ita tasa ta baro da kallonta daga entrance na boɗejo.

"ina za ki?". Khalil ɗin ya tambayeta yana kallon hannunta dake karkarwa tana ƙara damƙe box na glass din, ya lura kamar tana so ta hana hannuwan nata karkarwa ne amma hakan ya gagara.

tace,"Boɗejo ce ta aikeni ɗakinta zan ajiye mata idon baturenta".
Khalil yay murmushi yace,"kema ta koya miki idon bature kenan...to amma me ya samu ƙafarki?".

ta ɗan kallesa da mamaki amma sai ta kawar, bayan ta kalli ƙafartata tace da shi,"babu komai".

sai kawai ya jinjina kansa yace,"to shikenan tunda babu komai je aiken".
ya faɗa yana tsare ƙafafun nata da ido, sai ta tsaya bata tafin ba, ya ɗago ido yaga shi take kallo, da murmurshi ya ɗaga mata gira ɗaya yace,"ehen je ki mana". ya faɗa ba tare daya nuna mata so yake ya ƙureta ba.

ta juya zata tafi sai kuma ta ƙara juyowa ta kalle shi, ya ɗauke kansa yana kallon sama as in idonsa ba'a kanta yake ba. tana fara tafiya taji yace,"babu komai?, to shi wannan jan ƙafar na menene?, ko wani laƙanin ne nima a sammin?".

ba tare da ta juya ba ta girgiza masa kai bata ce komai ba, ta rumtse ido tana so ta ɗaga ƙafar ya ƙara cewa,"to jan ƙafa dai babu kyau, idan ma dai da kyau to kika ci gaba da janta ƙafarki faso zata yi ki rasa mijin aure, dan babu me kaiki gidansa kina yaga masa ledar ɗaki".

bata san lokacin da ta saki dariya ba, ta ɗan waigo tana kallonsa tace,"Hammah Khalil kana da ban dariya".
hannayensa a aljihu yace,"ke kuma kina da ban mamaki".

tace,"mamaki kuma?".
yace,"yes, banda haka ace mutum na ciwon ƙafa kuma yaƙi faɗa kuma a tambaya ya mu sa...to faɗa min, magani kike tsoro ko kuma allurar?".

ita kam bata san taya akai ya lura da ita ba tun farko, duk yanda ta dinga ɓoyewa ashe sai an iya ganewa. fuskarta tayi narai-narai kamar me shirin kuka, yana lure da ita da hakan, ya fiddo da hannunsa daga aljihun sannan yace,"je ki kai aiken kizo mu wuce asibiti". ta ɗago ido ta kallesa sai dai bai bata damar magana ba ya ƙara cewa,"ina jiranki a mota".

yana faɗin haka ya juya ya bar wajen, ita kuma ta juya ta ƙarasa part ɗin Boɗejon.
Khalil ya kira Hajiya Madina a waya ya sanar mata zancen ciwon ƙafar na Fillo wanda itama bata san da shi don tunda suka dawo bata ganta ba.

a parlon Boɗejo Fillo ta tarar da Turaki hakimce akan kujera ya zubawa tv dake kunne ido, kallo ɗaya zaka yi masa ka gane kallo kawai yake amma ba don yana fahimta ba, dan gaba ɗaya hankalinsa baya wurin.
tunda tayi masa kallo ɗaya bata ƙara ba, a iyakar wannan kallon ta gane cewar yana ɗauke da damuwa, wata damuwa da yake so ya rabu da ita.

dole ta gabansa zata wuce kafin taje bedroom ɗin Boɗejo, ta durƙusa a gabansa tace,"ina yini". bata sa ni ba ya amsa ko ba amsa ba, ta tashi ta bar wajen.

LULLUƁIN BIRI completeWhere stories live. Discover now