*LULLUƁIN BIRI*
*60*
*Jarabawa daga Mahaliccin mu.*Rayuwa tana cike da nasara da kuma faɗuwa, kuma akwai lokutan da gwaje-gwajen da ake yi mana kamar ba za su ƙare ba.
A cikin Alkur'ani me girma, akwai ayoyi da dama da Allah ya yi magana a kan hanyoyi daban-daban da za a gwada mu, amma kuma ya ba mu ƙunshin kulawa da zai taimaka mana mu bibiyi waɗannan lokutan masu wahala a gare mu.Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce:"Babu wata musiba da za ta samu musulmi face Allah ya kankare masa wani abu daga cikin zunuban shi, ko da kuwa tsinuwar ƙaya ce". (Bukhari Wa Muslim).
haƙiƙa jarabawa ba azaba ba ce daga Allah, tana daga cikin rahamarsa marar iyaka.
Musulmi ko wanda ba Musulmi ba, babu makawa kowannen mu yana fuskantar jarabawa a rayuwarsa. Rayuwa ba gadon wardi bane ga kowa, Akwai mutanen da ke fama da talauci, akwai masu fama da lafiyarsu, sannan akwai masu fama da danginsu, akwai masu fama da mutuwa a jere a jere.Jarabawar ubangiji ta bambanta ga ɗaiɗaikun mutane daban-daban, an yi su ne bisa la'akari da irin ƙarfinmu da rauninmu. Abubuwan da suka zama kamar gwaji a gare ni, wataƙila ba za su dame ku ba, nima akasin hakan.
tambayar gama gari da kowa ke yi a lokacin da ya shiga wani hali shi ne; me ya sa Allah ya sa na shiga cikin wannan halin? Me ya sa ba zan iya zama mai farin ciki a ko yaushe ba?, Menene na yi don cancantar wannan jarabawar? Me yasa Allah ya jarraba ni?.
kuma rashin sanin amsar waɗan nan tambayoyi wani lokacin yana iya nisanta mutum daga imaninsa.jarrabawa na iya haifar da mummunan tunani mai tayar da hankali wajen mutum ya aikata saɓo, kamar faɗin Allah ba ya so na!. ko ma mafi muni mutum yace Allah ba ya yi mini adalci(astagfrullah). Amma Allah shi ne Al-Adl, Mai adalci, kuma shi ne Ar-Rahman, Mai jin ƙai, wanda ba ya ya nufin cutarwa ga bayinsa, face yana son alheri a gare mu.
Akwai hikima a yanayin da ya ke sa mu a ciki, duk abin da muke buƙata mu yi shi ne haƙuri.
Akwai dalilai da yawa a cikin Alqur'ani da hadisi da suke taimaka mana wajen amsa tambayar dalilin da ya sa ake jarraba mu.An halicce mu ne domin mu bautawa Allah, wannan yana ɗaya daga cikin dalilan da yasa ake jarabtar mu.
tabbas an halicce mu ne domin mu bautawa Allah, kuma dukkanmu mun yi alƙawarin yin haka kafin a aiko mu a duniyar. Jarabawa hanya ce a gare mu don cika wannan alƙawarin.
jarrabawa ita ce hanyar da Allah ya ke bambanta mu, domin tana taimakawa wajen bayyanar da imani da rashin imani.Allah yana jarrabar mu, ya tsarkakemu ya kuma wanke mana zunubai. jarabawa gwaji ce ta maye gurbin wani mummunan bala'in, tabbas da munsan musibun da Allah yake kare mu, da ba za mu taɓa rasa sallah ba, kuma ba za mu taɓa son ɗauke goshin mu daga sujjada ba.
Gwaje-gwajen da ke ɓata mana rai na iya zama nau'i na kariya daga wani abu mafi muni da wataƙila ya same mu.
Allah yana so ya tsarkake mu, daga soyayyarsa da rahamarsa, domin mu samu ba Aljanna kaɗai ba, har ma da mafi girman darajar Annabawa da salihai. Gwaje-gwaje su na fallasa kurakuran mu da kasawarmu, kuma sanin hakan yana ba mu damar mai da hankali da himma wajen gyara waɗannan ɓangarori na halayenmu.Allah yana jarrabar wanda yake so. Annabi(SAW) yana cewa: "Duk lokacin da Allah ya nufi mutum da alheri, sai ya sanya shi cikin tsanani".[Bukhari].
me yasa?, domin idan bawan ya amsa jarabawarsa da haƙuri, da gamsuwa da hukuncin ubangiji, hakan yana kusantar da bawa zuwa ga Allah, Kuma Allah yana son masu haƙuri.Ibn Al-Qayyim (rahimahullah) ya ce idan aka yi mana jarrabawa, muna fuskantar zaɓi guda biyu; muyi haƙuri ba rashin haƙuri ba.
muke sauraren Alqur'ani da yawaita ambaton Allah saboda wadatar zuci, domin karanta alƙur'ani yana ba da wadar zuciya, addu'a don neman taimakon Allah, da ƙarfinsa, da samun sauƙi daga jarrabawa.mu tunatar da kanmu jarrabawar da Annabawa suka yi, sun ba mu kyawawan misalai na juriya. mu tuna cewa kowanne mutum guda ana gwada shi ta hanyoyi daban-daban. mu tuna babu wani abu a cikin wannan rayuwar da ke dawwama, don haka jarrabawar za ta ƙare insha Allah.
domin ko acikin alƙur'ani Allah yace,"Lallai ne tare da kowane wahala akwai sauƙi".