30

122 10 2
                                    

*LULLUƁIN BIRI*

*30*
Turaki ya harɗe hannayensa a ƙirji yana ta kallon yanda Fullo ke juye malt akan tiles, sai da ta juye tass tukunna ta turo ɗan ƙaramin bakinta da ya ƙurawa ido, yaga ta tashi without looking at inda yake tsaye ta wuce inda wani ƙofa yake ta buɗe, waje ne kamar balcony, mopper ta ɗauko ta dawo tukunna ta shiga toilet ta ɗebo ruwa ta goge wurin tas da turaren ƙamshi me daɗi.

kamar yanda bai san me zai ce mata ba haka bai san abin da zai yi mata ba.
duk tana jin yacca kallonsa ke shiga jikinta amma tayi kamar ta manta tare suka shigo ɗakin, in ace ba Turaki ba ne ba zata taɓa yarda ta ɗau tsayin sakanni ba balle mintuna tare da wani ƙato a ɗaki ɗaya, but shi ko da yaushe zuciyarta faɗa mata take yi he is a good person, he will not hurt you, sai dai ma ya kare mutuncinki da iyakar ƙarfinsa. kuma kamar yanda zuciyartata ta faɗa mata haka Hajiya Madina ta faɗa mata,_"me babban suna ba zai taɓa cutar da ke ba Fullo, ko kaffara ba zanyi ba akan hakan, saboda haka kar ki taɓa jin ɗarr dan kun kasancewa wuri ɗaya tare da shi"._

kuma in the same day ne bayan ta koma ɓangarensu, da Kaka ta ganta a firgice ta tambayeta lafiya?, ta faɗa mata cewar tana ɗakin Maama ne Turaki ya shigo, kuma ya hanata fita yace taci gaba da aikinta shi kuma ya kwanta kan kujera. abin da Kaka tace mata a lokacin shine,_"ba'a shaidar ɗan kuturu sai ya kwana 100 da yatsa, to amma ni zan shaidi Turaki, ba wuri ɗaya muke kwana mu tashi ba, ban san halinsa ba, amma zanyi rantsuwa kan cewar Turaki ba zai cuci ƴa mace ba, ko da ace kuwa zasu kwana wuri guda. kawai dai ki kula sosai Fullo"._

sai da ta gama mopping en sannan tayi bakin ƙofar wurin da har yanzu yake tsaye, tayi ƙasa da kanta sosai ƙirjinta sai bugawa yake yi, tana ta aikin jan yatsu shi kuma yay shiru kamar baya wurin. sai da ta gaji da tsayuwa tukunna tace masa,"dare yayi, Kaka tana jirana". tai maganar a sanyaye.

ya sauke hannayensa ya zuba su cikin aljihu sannan yace mata,"kin gama shan malt ɗin?". da mamakinsa sai yaga ta ɗaga masa kai alamar eh, ya ƙara cewa,"ya isheki ko a ƙaro?". tace,"ya isheni".
hannunta kawai ya kama suka koma zuwa ciki, har yanzu jikinta kwai zafi sosai. yay mata nuni da bakin gadon na alamar ta zauna, tace"don Allah". maganar ta katse dalilin haɗa idon da suka yi yana jifanta da wani wawan kallo.

babu shiri ta zauna hawaye na biyo kuncinta, yaja stool ya zauna yana ce mata,"tare aka haife ku da kuka ne?".

tai saurin girgiza kai, yace,"to yi min shiru, in kuma anan kike so ki kwana kar ki fasa".
babu shiri tayi ɗif tana goge hawayenta da gyalenta. shiru ya gimla cikin wasu ƴan sakanni, tana ɗago ido ta kallesa taga yana ɓallo magani, bata san lokacin da tace,"ni kam na shiga uku".

yaci gaba da ɓallan maganin sannan yace da ita,"bani ruwa".
cikin azama ta miƙe ta nufi ƙofa zata fita, a dabararta na in ta fita ba zata dawo ba, amma tana zuwa taji yasa key a ƙofan, ta waigo tana ce masa,"ƙofan rufe yake". ba tare da ya kalli inda take ba yace,"not necessary sai kin fita, ga ruwa nan akan drower".

taji kamar tai ihu, sai kace wadda ƙwai ya fashewa a ciki haka ta wuce inda roban faro yake ta ɗauko tare da cup, ta kawo masa yace ta zuba a cup, ta zuba sannan ya kamo hannunta ya zuba maganin yace ta shanye. da ƙyar ta sha maganin tana sha tana hawaye, suma da guda ɗai-ɗai ta dinƙa sha, tana gama sha sai ga amai nan ya taho, ta miƙe da sauri tayi hanyar toilet taji yace,"idan kin gama aman sai ki kwanta anan". ya faɗa yana nuna mata gado da bakinsa, tare da miƙewa zai fice.

kamar wacce aka dannawa pause haka ta tsaya tana sa hannu ta rufe bakinta, idanuwanta suka firfito waje dan ita ɗaya ta san me take ji, haka har sai da maganin ya koma, tana sauke numfashi tace,"na shanye".
yay mata shiru ya fice ya barta, yin duniya ta buɗe ƙofan duk da cewar there is spare key amma ƙofan yaƙi buɗuwa, means ya bar key ta waje kenan, wucewar five minutes sai ga shi ya dawo da coolern abinci a hannunsa, tana kallo ya wuce sai dai at this time ta kasa attempting buɗe ƙofan, binsa tayi da ido kawai har ya zauna kan kujera.

LULLUƁIN BIRI completeWhere stories live. Discover now