chapter 1

6.4K 331 13
                                    

[10/25, 9:53 PM] Cerdiya😍: 💗💗💗💗💗💗
*sarkakiyar soyayya!*
💗💗💗💗💗💗

  _true life story_

_luv story_

_gajeran labari_

written by :_

_foulani cerdiya_
        _and_
_khairat up_

_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_

_YANDA MUKA FARA WANNAN LITTAFIN LAFIYA ALLAH SA MU GAMA LAFIYA AMIN_

_VOTE FOR ME @WATTPAD khairi_muhd_

_your comment's are needed_



                01

Gida ne dan dai dai matsakaici,me dauke da dakuna hudu da kitchen daya babba da bandakuna biyu daya a kasa daya sama. A sama akwai dakuna biyu,yayinda a kasa ma akwai dakuna biyu,me gidan dan kasuwa ne yana da rufun asirin sa,matar sa d'aya da yaya hudu maza uku mace daya tilo tak, mutum ne shi me hazaka da san iyalan sa da cigaban su ga dattako ga hakuri ga kyauta. Hakan yasa mutane ke san sa suke kuma girmama shi ya na da sanin ya kamata ba ruwan sa da shiga abunda ba ruwan sa,haka ma matar sa,

yaran sa suna makaranta me kyau ta boko data arabi.

wannan gidan alhaji muhammad abdul_aali kenan haifafan garin kano dan kasuwa,uwargidan sa hauwa'u mustapha yar garin kano ce ita ma ta samu tarbiya a gidan su dan ma mahaifin ta malami ne ta kai matakin secondry a makaranta daga nan ta yi aure!"

Babban d'an sa sunan sa Auwal ,ma biyin sa kuma usman, me bi masa kuma naziru sai autar su maryama!.

suna zaune a cikin unguwar Chiranci Allah ya azurtasu,Dan kowannensu yana da abunyi shi Alhaji Auwal Dan kasuwa ne, Inda yake samun budi sosai dan mutum ne dayayo gadon halin Mahaifinsa sak gashi da dattako kuma kowa na gidan yana jin tsoronsa, Dan baya wani wasa dasu sosai, gashi da magana daya idan yayi ta kuma baya sauya ta sak yake baya magana biyu, sakamakon shi ne babba kuma duk hukuncin daya yanke ya yanku. Ya auri matarsa ta farko Inda ta haifi yaya uku Yah naseer, sai Yah zainab sai Rukayyyah, a lokacin haihuwar tane mamansu ta mutu a lokacin alllhaji Auwal ya auuro wata baafulatana Mai suna Ummul khairi suke kiranta da Mamy tana da kirki ta haifi ya mace wato  Hauwah mai sunan baba ta chiranchi sai kannenta uku Asleem da tasleem sai Hafeez.
      Shikuwa usman wato uncle usman mutum ne me sanyin hali bashi da fada ko Kadan, kuma shi maaikacin gwamnati ne.
       Sai uncle naziru shima daya kasance Dan kasuwa, sai maryam wato Umma maryam. Dukkan ninsu sunyi aure kuma kowanne yana da yaya.
    Ita Ummah Maryam danta babba namiji ne daga shi sai niimah, sai Ameenullah su ukune. Mahaifinsu ya rasu Dan haka rukon su biyu da Yah Muh da niimah ya koma gun yayan mamansu wato alhaji Auwal,inda
Mamy ita ke rikonsu dukansu da yayanta da yayan alhajin da kuma su yayan kanwarsa.
   A gidan Alhaji Auwal kowa yana son Hauwa, saboda sunan kakarsu ne,gashi in kika sake kika fadi sunanta kin Shiga uku a gurin Abba, hakan yasa suke kiranta da MAISHA (Pretty). Abbantane yasa mata sunan saboda duk gidan ta fisu kyau, tundaga kan yayyanta kuwa har kannenta babu mai farinta da kyawun idonta, Maisha yarinya CE mai tsiwa gata da son kwalliya tun tana yar kararrama, kome takeso shi ake mata, kuma duk abinda tace tanaso shi zaayi. Duk kuwa da cewar ga yayyanta nan a gidan amma basu da bakin magana, ko rashin kunya tayi ba Wanda yake mata magana sai Yah Muh danshi baya mata wasa ko kadan, sakamokon mutumne mai son girma da kuma class.Ita ma Maisha tsoronma yin laifi take a gabansa duk da bawai Shakkar dukansa take ba, Dan tasan a gidan ita ta gaban goshi ce,.
    Hakan yasamo asali tasanadin rashin lpyr datake dashi tana fama da pneumonia sannan gata da sunan Maman Abbanta a yanzu Maisha shekararta 8 amma in tana wani abun saikin rantse katuwar budurwa ce , saboda iyayinta. Inda Yah Rukayya keda shekara 12
     Wannan kenan

      "Maisha! Maisha!!."
     Jin muryar Yah Rukayya na kwala mata kira yasa ta ajiye Jan bakin datake gogawa a lips dinta ta sauko zuwa palorn dantaaji meye, tsayawa tayi akanta ta zumburo baki tace" meye ne?.....".
     "Lallai to bani nake kiranki ba dama Yah Muh ne yace in kiraki,"
  Zaro ido tayi jin an ambaci malaikanta.
     "Mtswwww.......Taja dogon tsaki, tace" wollah na dauka kece da na sauke miki sh..........".
     "Iyyye........Yayartaki kike fadawa haka, idan ita ta kirakin kenan bata isa baki?..".

   Yah Muh ne ke maganar a lkcn dayake shigowa palorn yanemi guri ya zauna tare da ajiye jaridar dake hannunshi Dan shi dama akwai karatun jarida.
       Zazzare ido ta soma Tana ja da baya ya kuwa sa hannu ya cafkota tare da tsugunnar da ita ya kalli Yah Rukayya yace" Saraki(Sunan da yake fadawa Rukayya kenan sbd shakuwarsu Dan yafi sakarmata fuska ko a gidan.) daukomun Wayar can
    Ya fada yana Nuna mata wayar chaja, aikuwa ta ta dauko ta kaho masa.

   Beyi wata wata ba ya daga Maisha ya zula mata ita aikuwa take ta sa ihu tana "Wayyo Abbana......Wayyo Mamy na".
    Mamy dake wanka ta jiyo ihun diyartata amma batabi ta kanta ba Dan tasan Maisha bajin magana take ba.

   Tana cikin ihun nan ta jiyo horn din motar Abba, aikuwa ta sake fashewa da kuka harda zaa kasheta, alhalin bulala biyu ma yayi mata.
    Abba dake parking mota jin ihun Yar lelensa yasa ya shigo a fusace aikuwa yana zuwa, ya kalli Yah Rukayya ita da Yah Muh yace" waye ya daketa".

       Tana kuka da shashsheka ta nufa Yah Muh da yatsa tana wani hararensa.
     Aikuwa Nan Abba ya fara masa fada ta Inda yake shiga batanan yake fita.
      Inda Yah Muh baice komai ba illa hakuri daya bawa Abban.
     Ya tashi ya fita da tunanin yadda zai koyawa Maisha Hankali inya kamata.

        We need ur comment pls

  SARK'AK'IYAR SOYAYYA!Where stories live. Discover now