💗💗💗💗💗💗💗💗
SARK'AK'IYAR SOYAYYAH
💗💗💗💗💗💗💗
NaKHAIRAT UP
"37"
Sh'iryawa sukayi da sauri sauri suka fice basu zarce koina ba sai hospital.
Kowa yana d'akin kama daga Abba Usman da Abba Nazeeru duk suna nan ga Umma ma, kai kowa dai da ka sani na family din Alhaji Muhd Abdul Ali suna gurin.
Kiran da Abbane yasa a sanar da kowa wai saboda had'in kan y'ay'ansu ko bayan ransa.
Magana ya fara wacce dakyar take fita, Dan seka saurara sosai zakaji abinda ma yake cewa.
"Usman, Kaine mabiyina kuma kune yan uwana kai da Nazeeru, dan Allah, Ku rik'e zumunci Ku kula da yaran nan, kada kuyi laakari da halinsu........Kuyi hak'uri ga y'ay'ana nan, nabaku halak Malak ko bayan raina na barmuku su.",
Shiru yayi sannan ya cigaba da cewa
" Muhd Maisha Kuyi hak'uri da yadda rayuwa tazo muku".
Abba ya fad'i hakane SBD abinda ya tsaya masa arai na kasa faranta ran y'ay'ansa mafi soyuwa a ransa, tabbas duk da Muhd Dan kanwarsa ne, amma ji yake kamar sh'i ya haifesh'i.Kuka ne ya kufcewa Mamy Dan zuciyarta wani zafi take mata, inda Maisha ma ta hau nata kukan.
"Matata ta kaina kenan meye kike kuka, kar ki damu ai ke y'ar aljannah CE, tunda tun zamana dake baki tab'a yimun musu fu, Allah yayi muku albarka Khairatu".Abba ya fad'a tari yana turnuk'esh'i.
" Maisha ki bi mijinki, Dan Allah Mo'taseem yana sonki, kinji kada ki ki yi masa biyayya, in kuwa kikai haka bazan taba yafe maki ba, kiyiwa Mo'taseem biyayya, kuma ki dinga girmamash'i.
Ke Rukayya kece babba, k'anwarki Ku had'e kanku keda ita, saboda wataran itace zata share maki hawaye"."Wai Yaya duk meye na wannan maganganun? Pls ka bari kana tsinka mana zuciya da tsoro".
Abba Usaman ya fad'a yana goge kwalla data zubo mash'i.
" Barni na fad'a musu gaskiya Kanina, wataran zasu tuna maganar dole".
"Abba munji Maganarka, kuma zamu had'e kanmu insha Allah, Abba ka dena fad'in hka".Maisha ta fad'a tana fash'ewa da kuka.
" Tabbas ko bana nan inason Ku rik'e zumuncinku, Rukayyyah nasan halin ki,ki sanja hali, Maisha Yar uwarki CE, ki zauna lpy da ita, in kika ki yin haka Allah ya isa zan maki saboda zaki ruguzamun family na".
Kuka tasaka tana
"Wallahi Abba lpy zamu zauna Dan Allah Abba ka warke, ka dena fadin hka".Ranar nan dai Abba haka yasa su a gaba, daga kan wancan ya koma wancan kuma kowannensu naseeha yake musu, wacce dakyar ma yake furta su, shiyasa ya kamo can ya cika can.
Dayake Jumaah CE, kowa yayi shirin masallaci suka tafi, inda Abba yayi tashi sallar a zaune Dan baya ma iya yi sai dai ya hararo.Da dare yayi kowa ya tafi banda Maisha da ta zauna a Kusa da Abba in banda kuka ba abinda take.
D'aga hannunsa Abba yayi dakyar ya dafata tadan kwanta a jikinsa, tanajin yadda zuciyarshi ke beating fat-fat.
" Maisha na, haba pretty na, meye na kuka haka, duk saboda ni ne? Yi sh'iru na Kusa warke Wa gaba daya kinji, na Kusa in samu sauki, kuma nasan zakiji dadi in na warke".Haka dai Abba yayi ta rarrashinta, Kowa yayi da ita data tafi gida amma ta kasa seda Abba yayi ta bata baki harda Ciro wani abunsa ya dank'a mata a hannu sannan ta tafi.
Tazo fitowa a dakin Yah mas ya rik'e hannunta Dan tsabar tausayinta da yakeji, har hawaye yake fitarwa. Sunzo dai dai fita a kofar d'akin ta juyo suka had'a ido da Abba yayi mata murmushi, tare da daga hannnunsa d'aya yayi mata bye yana murmushi Wanda har seda hak'oransa na azurfa suka haska.
Dawo Wa tayi da gudu ta fad'a jikinsa ta saki wani marayan kuka. A haka dai aka samu aka janyeta daga dakin mota Yah mas ya sakata, ta fash'e da kuka rarrashinta yayi na duniyarnan amma INA ta kasa yin shiru.
Sallah tayi tayi, har sai da bacci b'arawo ya saceta a nan kan sallayar.Mafarki tayi da Abbanta yayi kyau sanye da green kaya,ya k'ara wani haske sosai.
Rik'e hannunshi Maisha tayi tace
"Lah Abba da gaske ka warke, Abba jikinka yayi kyau fiye da da".Murmushi' yayi mata yace
" Dama ai na gaya maki Maishan Abba, Abbanki zai warke gash'i kuma kin gani".Girgixa mai kai tayi tace
"Aikam dai Naji dadi".
" toh amma ki dena wannan kukan kinji Maishana ".
" Nadena Abba, na dena na dena, ta fad'a kuma hakan ya fito har a baccinta datakeyi.Yah Mas addua ya fara yi mata, aikuwa ta farka.
"Kasan me, Abba na ya warke. Nayi mafarki dash'i".
Ka tash'i muje asibitin yan..........
Bata k'arasa maganar ba sako ya shigo wayar Yah Mas.
Yana karantawa wani gumi ya sh'iga keto masa, a take ya sulale ya ajiye wayar.
" Yay dai Yayana".
Murmushi ya ka'kalo
"Ah bakomi Abba ya warke tabbas Maisha ki shirya in gari yayi haske muje ki gansh'i yana gida ma yanzu haka".Tsalle tayi ta rungume shi,
" Aikuwa har girki zanmasa, tunda kaga baici wancan ba,kuma nasan zaiji dadin abincin".Haka ta gama girkinta inda Yah Mas yake ta Binta da wani irin kalllo.
Suna zuwa unguwarsu ta fara cin karo da mutane
"Meye yake faruwa ne Yah Mas".Maisha ta tambayeshi.
" Uhm.......Uhm....inajin taro akeyi.......Uhmmm ah.....ko d'aurin aure.......".Ganin kofar gidansu mak'eel da mutane.
Da sauri ta fito daga cikin motar.
Ta nufi hanyar cikin gida inda taji wani yana fad'in.
"Allahu akhbar Alhaji Auwal lokaci yayi kaico duniya".Da sauri Maisha tayi baya tana zaro ido tare da dafe kirjinta tace.
" Innalillahi wa'inna ilahirrajiun Wayyo Ni Wayyo Abbana".
Tafiya tayi luuuu zata fad'i Yah Muhd ya k'araso shi da Yah mas suka rik'e ta.
Tabbas Mutuwa gaskiya CE Allah ka jikan iyayenmu ka k'afarta masu, K'ulhuwallahu 3 pls ga duk Wanda iyayensa suka rasu Allah ya jikansu ya
Kyautata namu zuwan. amma zafi da rad'adin mutuwa baya gogewa forever.
the pains is still the same#sark'akiyar soyayyah.
YOU ARE READING
SARK'AK'IYAR SOYAYYA!
Romancea love story, this is a love triangle between 4 lover's.