💗💗💗💗💗💗💗💗
SARK'AK'IYAR SOYAYYAH
💗💗💗💗💗💗💗💗NA
FOULANI CERDIYA
DA
KHAIRAT UP"50"
Kuka ta tadda sh'i yana yi kamar yaro, ta rik'e hannunsa tana rarrash'insa, yakasa yace komai sai kallonta da yake yana hawaye, can dai yace
"Wallahi Jidderh nai maki son da ban tab'a yiwa wani k'otan k'ocinsa ba, ni kuma tawa k'addarar kenan? Dama Allah ya halicceni ne Dan na so ki, kuma be k'addara rayuwar mu tare ba, ya zanyi Jidderh na".
Ya fad'a yana rungumeta tsam a jikinsa,
Tunda suke dashi bai taba kiran sunanta ba sai yau, yau dinma tsananin kid'imewa ne.
" Am sorry,am so sorry, tabbas rayuwa ta da kai rubutacciya CE, kuma ba yadda zamuyi, ba yadda muka iya, kayi hakuri kadena fad'in haka, Allah yana jarabtar bawansa da duk abinda yaso, kum kasan Allah ma baya d'orawa rai abinda bazai iya ba, kasani ko na dawo gareka nan gaba?"."Maisha? Sefa kinyi wani auren, kina nufin me?".
" Zanyi wani auren, in yaso sai na fito ka aureni".
Ta fad'a da confidence.
Girgixa mata kai yayi yace
"Ni dake duk ba jahilai bane, Dan haka bazamuyi wannan hakan ba, Maisha haka Allah ya tsara, haka Allah ya rubu........"." Tazo ta fice ta tafi gidansu, tunda an sallameta, me kuma take jira?".
Mama dake sh'igowa dakin take wannan masifar hartana katse masu firarsu.
D'ago da jajayen idonsa yayi yana mata wani irin kallo na tsana badan uwa uwa bace da Mama ko kallonta bazai karayi, abinda zuciyarsa take yayana masa kenan.
Maisha ta mike daga jikinsa, ta kalleshi
"Bari na tafi kaji, ka dena damuwa Dan Allah, bakomai"." Maisha kece rayuwa ta, ya zanyi in kika tafi?".
Kallonshi Mama tayi ta galla masa harara tace
"Ka mutu,ko k bar gidan Mara mutunci ka Nuna fifkon waccen Yar iskar akaina".Kallonta Maisha tayi aranta tace yanzu ba sirikata bace, bazan yadda ta na gayan magana ba.
" Ki iya bakin ki Dan ba kyaleki zanyi ba yanzu dama kina cin darajar wannan bawan Allahn ne badan haka ba, ke aka CE ki kalli ne kimun rashin mutunci bazaki yi ba, kuma sakin da kika sa danki yayi zaki gani tsakanin ni da ke waye zai fi cutuwa, Yah mas sai anjima".
Da gudu ta fice tana kukan rabuwa da mutumin da yaso ta tunda kuruciyarta har girmanta.
Maisha na fita Yah mas ya sume.
Gida ta nufa amma wannan karon ta goge hawayenta a nutse taje.
Mamy nata murna haka Little da tunda ta dauke sh'i bata ajiye sh'i ba.
Sai da maghriba tayi Yah muhd ya dawo yana ganinta gabansa ya fad'i.
Dakyar yaci abinci ya kalli Maisha yace
"Dare fa yana yi a tafi gida".Sai a lokacin ta kama kuka hankalinsa ya tash'i haka ma Mamy dakyar ta iya yi musu bayanin abinda ya faru suma sai kuka, Yah Muhd saboda bacin rai kawai ficewa yayi daga gidan.
Bayan sati d'aya.
Maisha zaune tana aikinta na tunani Yah muhd ya shigo kallonta yayi yai murmush'i yace" Yanmatan ba tunanin me akeyi ne? Uhm".
D'agowa tayi tai murmushi
"Ni CE yanmatan kuma?"." Au to uwar mata shikenan, ke na fuskanci tsufa zakiyi da wuri ma".
"Wallahi Aa Allah ya kiyaye sai dai in kai".
" ni ai saurayin ne har yanzu".
Kyalkyalewa Maisha tayi da dariya tace
"Wadin? Ko ka manta kana da Little ne? Ai kai yanzu tsoho ne Yah Muhd ka tsufa baka ganin mudubi".
" waye ya tsufan?".Ya fada yana nannande hannun rigarsa.
"Kai mana Yah muh....."
Bata karasa ba ya dago hannu zai duka ai da gudu ta mike ta fara zagaye kujerun palor yana fad'in sai ya kamata ita kama sai Zillo take masa tana gwalo.
Mamy CE tayi tsaye tana kallonsu, ikon Allah wad'annan yara, angirman ma sai anyi rigimarne ko yaya?.
Gyaran murya tayi aikuwa Maisha tana jin Mamy tayi bayanta da gudu tana
"Mamy ki b'oyeni".
Tureta Mamy tayi tace
" Aa itaku nasan halinki ai tsokanarsa kikayi halan ko?"."Wallahi mamy ki kyaleta wai ni take cewa tsoho".
" Hahhahhhha Yah muhd tsoho WObul wobul".
Ta fad'a tana masa gwalo.
Kukan Little ne yaja hankalinki da sauri kowa yana kokarin daukarsa, Maisha tayi sauri ta d'auke shi tana jijjigashi da cewa
"Yawwa yaro na, kaga Abban ka zai dokine ne ko yasa kake kukan yi sh'iru nawan".
Team
#Sarkakiyar soyayyah
YOU ARE READING
SARK'AK'IYAR SOYAYYA!
Romantika love story, this is a love triangle between 4 lover's.