chapter 42

999 70 0
                                    

💗💗💗💗💗💗💗💗
SARK'AK'IYAR SOYAYYAH
💗💗💗💗💗💗💗💗

         Na
Foulani cerdiya
       Da
Khairat up

         "42"

A haka suka karasa cikin gidan inda Maisha ta zube akan 3sitter tana mik'a.

Guri Yah Rukyy ta samu ta zauna
       Tace
   "uhm wlh nifa sisto maganar da kika fada' ta tsaya mun a rai kuma wai da gaske kike ne?".

       Dariya Maisha tayi sannan tace
          " Haba Yah Rukyy, ke kuwa ko d'an ruwa baki bani ba kin fara mun tambaya".

        Murmushi tayi ta mik'e tana fadin
         "Ke bakisan hanyar fridge ba, sai kin sani aiki ko tausayina bakyaji".

        Dariya tayi tace
      'Na gaji ne kedai d'aukomun ruwan before".

           Suna zaune suna hira inda hankalin yah Rukyy duk yana ga maganar da Maisha ta fara yi mata wai da gaske Mas aure zai k'ara?.

            Abinci suke ci, Yah Rukyy ta kalli Maisha tace
         " ni kink'i gayamun da gaske ne wai Yah Mas aure zai k'ara?".

        Lumsh'e ido Maisha tayi ta bata labarin duk abinda yake faruwa, Wanda babu Wanda yasani harta Mamy ma.

       "Kut melesi..........Me kikace Maisha? Tab kuma ke kika hakura".

        Murmushi dole Maisha tayi
      " To ya zanyi Yah Rukyy, bakomi Allah ya bamu zaman lafiya ".

        Ajiyar zuciya Rukyy ta sauke tace
           " Tab zanga ranar da Yah Muhd zaice zai k'ara aure ai inajin k'ona yarinyar zanyi wallahi".

Dariya Maisha tayi tace
         "Ai dama ke sisto baki da dama".

           Girgixa kanta Rukyy tayi tace
       " Ke sisto tunda har na iya kish'i dake ke da kike k'anwata to wlahi banga wacce zan ragawa ba indai akan sweetheart dina ne".

         Haka dai sukayi ta firarsu gwanin ban sh'aawa.

    Sai can dare Yah Mas yazo suka tafi inda Yah Rukyy tayi masa ta tas shi dai baice komi ba sai murmushi.

       Suna hanya zasu koma tace sai ya tsaya a murtala suya ya saya mata kaza,bayan sun saya suka wuce gida.

Tana zuwa wanka tayi ta Dan shafa powder tayi kyau sosai.

       Riga tasa iya gwiwarta ta fito tana Dan sauri sauri Dan ta k'agu taci kazar.

          Yah Mas na zaune akan kujera yana kallon  film din da akeyi a zee cinema Maisha ta k'araso ta zauna.

    Ta janyo kazarta sai kuma ta tuna wani Abu ta kalleshi tace
         "Yah pls plate zaka daukomun wallahi na gaji".

       " Aike baby akwai sa aikin tsiya bari in dauko maki".

         Said a ya dauko mata ya ajiye mata lemo da ruwa ta fara ci tana yanga.

          "Ni wallahi kazar ma sai naji ba dad'i Kamar zanyi amai".

Maisha ta fada tana yamutse fuska.

Kara yago kazar tayi ta kai baki, aikuwa take ta fara kyalaya amai kamar zata amayar da cikinta.

Hankalin Yah mas duk ya tash'i beyi wata wata baya dauko mata doguwar Riga ya saka mata, ya d'auketa sai asibiti.

            Private hospital ne dake Kusa da su nan ya kaita, ana mata test gwajin farko sai ga ciki na sati uku da kwana shida.

          Murna gun Yah Mas baa magana ya d'aga ta sama ya dinga juyi da ita

Da zumudi ya Dau wayarsa ya kira Ummanshi yana sanar mata sai cewa tayi.
      " To farin shigar ciki, sai kace wani abun arziki kaketa rawar kai ko, to ka dakata haka".

          Ta kashe wayar a take.

Fuskar Yah Mas ta saanja Dan baiji dadi ba amma sai ya dake ya Kamo hannun Maisha suka tafi mota.

       Bayan sati d'aya
Laulayi yana ta damun Maisha Dan duk ta lalace tayi baki ta rame kamar ba ita ba.

         Suna zaune ta d'aga waya ta kira Yah Rukyy take tsokarta
           "mum's triple ya akai?".
          Ajiyar zuciya Maisha tayi tace
           " Dan Allah ni bari wannan Dan naki sai wahalar dani yake, Yah Rukyy dama tambayaraki zanyi".

         "Inajin ki mene"
        Dan rufe fuska Maisha tayi tace
           "Wallahi ruwa nake gani a Mama na........Shi.......ne nace kema hka kikayi".

Dariya Yah Rukyy tasa tana jinjina hali irin na Maishan ta.

  SARK'AK'IYAR SOYAYYA!Where stories live. Discover now