chapter 58

993 73 0
                                    

💗💗💗💗💗💗
Sark'ak'iyar soyayya!
     ❤❤❤❤❤

foulani cerdiya
&
khairat up

vote @wattpad khairi_muhd

F.O.W

             "58"

"cikin kankanin lokaci aka gama komai sati biyu kacal aka saka na biki."

"mas na gida a kwance saudah take sanar masa ae bikin maisha nan da sati biyu."

"a hankali ya daga kwayar idan sa ya kalle ta ya ce da wa?"

"wai wannan mijin yar ta din nan."

"umm muhammad kennan? Allah ya basu zaman lafiya"

"amin"

"hakika rabon auran maisha da muhammad ne ya sa rukky mutuwa . rabon little kuma ya hada muhd da rukky!"

"shi yasan wannan ita ce kaddarar sa amma Allah sheda yana san maisha kuma ba ranan da rana zata fito be tuna da maisha ba."

"a sukwane ya mike ya ce zan fita."

"a dawo lafiya."

"Allah yasa."

"amin"

💗💗💗💗💗💗

"tunda aka gama komai aka sa rana maisha bata kuma ji daga yah muhd ba, kuma bata kuma sa shi a idan ta ba."

"hakan ya sa ta gane cewa ya shaqa ya dau fushi da ita."

"yah muhd daurewa kawai yake amma haushin maisha yake ji."

"yana zaune cikin motar sa ya kira wayar mami ya ce a aiko masa da little zasu gaisa."

"to dan gidana!"

"maisha ki kai ma muhd megida na."

"to kawai ta fada a sanyaye!"

"kwalliya ta sake masa ta dau mayafi ta dora a kanta."

"a gun driver me zaman banza ya zauna ya sauko da kafar sa daya waje yana danne danne a wayar sa kuma sarai yasan ta taho amma ko dagowa be ba kuma be fasa danna wayar ba."

"salamu alaikum"

"wa alaikum salam ya fada sama sama"

"ina wuni?"

"da ban wuni ba kya gan ni?"

"uhm ta fada a dan darare."

"little ta mika masa ya amsa."

"my boy kana ta wayo abun ka ji yanda ka zama big boy! kato da kai me ka ke ci.?"

"little da gwalangwalantan sa ya dinga dariya yana tsalle yaga mahaifin sa."

"kamshin turaren maisha tuntuni ya sauke masa kasala "

"wani abu?"

"da me fa?"

"kin mun tsaye a kai"

"uhm ta fada ta juya ta dau hanyan komawa cikin gida."

"mutum sai masifa ya iya da fada."

"kan kujera ta samu ta zauna tana kunkunai."
"har kin dawo?"

"eh"

"ya fita dashi ne?"

"tukuna dai amma kila ya fita dashi"

"to ga abincin nan an gama!"

"tam sannu mamin mu"

"youwa yarana yan albarka!"

"reverse yayi da motan ya yi waje gidan su ya yi tunanin kai sa wajan umman sa su gaisa"

"yana fita daga layin motan mas ta karyo kwana ta shiga layin."

"megadi ya ji horn ya mike ya bude kofa ah barka da zuwa yallabai"

"youwa mallam ko maisha tana gida?"

"eh tana na "

"dan Allah a kira mun ita"

"to to an gama"

"da sallama ya shiga gidan maisha ta amsa masa baba ya aka yi?"

"dama yallabai ne yake neman ki a waje."

"to ina zuwa,a tunanin ta yah muhd ke kiran ta."

"fita tayi waje cike da mamaki tayi turus da ganin ya mas,da kyar ta dake ta karasa gun sa."

"yah mas manyan yan kasa dama talaka na ganin ku?"

"murmushi yayi kawai ya ce gashi kuwa muna ganin ku"

"haha ya gida ya matar taka?"

"alhamdulila"

"ya aiki?"

"mun gode Allah!"

"to madall"

"ya mami"

"tana nan lafiya garau"

"to masha Allah"

"duk suka yi shiru abinsu da kyar ya ce ashe kuma an kusa biki?"

"tay sunkyuy da kai ta ce saudatu gulma har ta fesa maka?"

"to kinga laifin ta? dan ta fadi abun alkhairi"

"aa ban ce ba"

"to kin gani"

"to maisha allah ya sanya alheri ya baku zaman lafiya ya baku hakuri da juna, maisha rabuwar mu kaddara ce amma tabbas mun shiga cakwakiyar SARKAKIYAR SOYAYYA!"

"Haka ne amma ya za ayi?"

"babu idan kina da buktar wani abu ki fada mun kin ji koda bama tare a matsayin mata da miji ,muna tare a matsayin wa da kanwa kamar tun asali saduwar alkairi ya fada ya shige mota kwalla na zubo masa da gudu ya figi motar ta sa."

"tausayi ya bata a sanyaye ta koma cikin gida."

  SARK'AK'IYAR SOYAYYA!Where stories live. Discover now