chapter 31

1.2K 108 5
                                    

💗💗💗💗💗💗💗💗
SARK'AK'IYAR SOYAYYAH
💗💗💗💗💗💗💗💗

         NA
FOULANI CERDIYA
     &
KHAIRAT UP
    
       "32"

"Ai kam gaskiya taba kinkine Mamyn yara kawai a kyalesu, dama Allah yayi bazasu auri juna ba, tunda da ace tunfarko sun yi magana ne, amma wallahi ni banso haka ba.
        Yaja numfash'i yace
       " Muhd shine babba dole sh'i zaafi tausa, tunda shi ne zai zauna da wacce ba raayinsa ba.

    Amma ita Maisha nasan Mo'taseem yana sonta,tabbas zai kularmana da ita yanzu kuyi hak'uri, kema Maryama kiyi hak'uri ki barkomi bakomai ba, kid'auka cewar Allah beyi zasuyi aure ba".
 
       Goge idonta Umma tayi tace
       "Sh'ikenan Yaya duk abinda kace haka zaayi insha Allah zan dannesh'i da yayi hak'uri".

        " Yawwa, Ku taush'esu duka tunda aurene an Riga da an d'aura".

        D'akin Maisha suka nufa suna sh'iga suka taddata tana sallah Wanda da taimakon Yah Mas tayi alwalar.

       Sh'ikuma yana zaune yana daddana waya su Abba na sh'igowa ya mik'e ya basu guri irin girmamawar nan, tare da tsugunnawa suka gaisa.

      Kallonsh'i Abba yayi, yad'anyi murmush'i yace
        "Kai Mo'taseem kaje ka huta mana, tun fa  daaka kahota kana nan ko gida nasan bakaje ba,

     Ya kamata kad'anje gida ka huta tunda gasu Ummanta zasu kula da ita".

      D'an Sosa kansh'i yayi yace
        " Ai Abba saboda kada a Baku wahala, tunda gani aiku ya kamata Ku huta".
    
Dariya Abba yayi yana k'ara jinjina irin son da Yah Mas yakewa Maisha.

          "Toh.....Ai Hutu bai kamamu ba, tunda ba ita kad'ai bace a hospital dinba.Yayanta Muhd bash'i da lafiya kuma Gado suka bash'i sh'ima".

          " Gado Abba? Wad'in Yah Muhd din?.
        Maisha da idar da sallarta kenan ta tambayi Abba tana mik'ewa tsaye a firgice.

         Takaici ne ya kama Abba da kunyar Yah Mas ganin abinda Maisha tayi.

        Takalmi tafara zurawa
        "Abba bari naje gunsa......Yana INA Dan Allah? meye ya sameshi? Wayyo Yah Muhd".

     Maisha ta fash'e da kuka ta fice da gudu daga dakin batare data bari Abba ya yayi mata bayanin inda Yah Muhd yaken ba.

       Yah Mas daya zama statue agurin ya dantse hannayensh'i tare da furzar da iska yabi bayanta da sauri sh'ima.

   A can dakin kuwa        Mamy CE ta kalli Umma data rafka uban tagumi tace
         " Dan Allah Ku duba fa Ku gani irin birkicewar da Maisha tayi."

     "Uhm aini na rasa bakin magana, ni tsorona kada ma yaron nan ya gane Maisha tana balain son Muhd saboda yaron nan ta idonsa zaka san yayi balain fad'awa a kaunar Maisha".

       Abba dai ya rasama me zaice sai kurum ya mik'e ya fara sintiri a d'akin Umma da Mamy su ka bish'i da kallo suna mamakin zagayen da ya soma.

      Rukyy amarya, tayi tayi da Aisha ta zo suje asibin tace ita bazata ba dare yayi ta bari gobe da safe taje.

Amma INA Rukyy tayi nisa batajin kira, sao data bari Aisha tafara bacci sannan ta tashi haka ta tashi ta fito tana sauri-sauri,jin mots'in fita Aisha tayi yasa ta jaho mayafinta ta bita ganin dai da gaske take yasa Aisha tace
       " Muje tare, ni wannan ma Muhd din yadda naga ke kin damu dash'i wallahi sh'i bema damu dake ba, aikin banza,ni na fara bacci na amma kin matsa".

Harararta Rukyy tayi
     "Mtswwwwe ai ke baki son SOYAYYAH bane sh'i yasa".

Haka dai suka fito suka samu me napep suka tafi.

" Maisha!, Maisha!!, ki tsaya nace".

      Yah Mas daya biyo Maisha da sauri yake kwala mata kira, waiwayowa tayi ta kalleshi ta k'ara gudu bata sani ba tayi karo da mutum.

         D'agowa yayi da sauri tare da ja da baya mamaki k'arara a fuskarsa yace
         "Aa, wannan ba patient din da aka ba Gado bace".

      Dr Nura da Maisha ta bige ya tambaya.

      " Eh, INA Yah Muhd yana INA? Meye ya samesh'i'".
           Ganinta a har gitse duk ta rikirkice yasa yayi saurin nuna mata d'akin dake bayan shi dama kuma daga duba jikin Yah muhd din ya dawo.

      Bangaje sh'i tayi tayi cikin d'akin da gudu tana sh'iga ta saka kuka, tare da nufar kan gadon dayake tana zuwa kawai ta afka jikin Yah Muhd ta fara kuka mai tsuma zuciya.

           Yah Mas ganin d'akin data sh'iga yasa ya bita a baya Dan yana tsoron kada taje ta cutar da kanta ganin yadda tabi ta fita hayyacinta.

      Yana sh'iga idonsa yayi masa dusu-dusu wai Maisha ta manta da auren sh'i ne akanta take irin wannan abun, kafafuwansa ne sukayi masa nauyi ya kasa d'aga su, ga wani irin turirin Masifar kishi daya rufesh'i.

      Rukyy da sh'igowarta asibitin kurum ta nemi d'akin dayake, nan ta nufa tana sh'iga ta hango mace akan gadon kuma ta kalli Yah Mas dayake taka k'afarsa a hankali har yaje bakin gadon.

Kallon matar sa yake rungume da wani namiji da bashi ba, duk saboda me tayi hakan
" Saboda So".
    Zuciyarshi ta bashi amsa.
       Maisha kuwa da ba tasan da sh'igowar duka su biyun ba yasa da soma surutai
         "Yah na ka tash'i, ni ban mutu ba kaima kada ka mutu, pls wallahi Maishan ka tana sonka, Dan Allah ka tash'i Kar katafi ka barni Dan Allah".
       Tana magana tana hawaye shar-shar Wanda yake ta zuba saman k'irjinsa.

Kamar a mafarki ya soma jin kuka da maganar da bazai taba mance ko ta waye ba yasa ya soma d'an bud'e idonsh'i a hankali.

           Yah Mas ne ya sa hannunshi ya d'ago da Maisha, yana girgixa mata kai, hannunshi ya d'aga da niyyar marinta amma ya kasa, Rukky da b'acin rai ya kusan kash'eta yasa batare da wata-wata ba, ta d'aga yatsanta biyar ta zabgawa Maisha mari
             

       " Ki dawo hankalinki Maisha U gone mad, meyasa bazaki rabu da Mijina ba, kinyi auren ma kinada aurenma da igiyar wani a kanki amma bakiji kunyar rungume Mijina wata ba, kuma tsabar hauka a gaban Mijinki?".

            Rukyy tana maganar tana runts'e idonta alamar ranta yakai k'arshen b'aci.

           Marin da Rukyy yayiwa Maisha shine ya dawo da ita cikin hankalinta, Dan tabbas da bata cikin hayyacinta.

           "Menai mata ta maren".
     Maisha ta tambyi kanta da kanta.
       " Nazo na rungume mata miji".
    Ta kuma bawa kanta da kanta amsa.

        D'akin ne yayi tsit, Yah Muhd dakyar ya iya tash'i zaune, ransa a matuk'ar b'ace.

          A ran Yah Mas dad'in Marin Maisha da Rukyy tayi yaji, sannan kuma yaji haushin Marin tabbas, Dan gaskiya yana son Maisha So bana wasa ba.

     Amma tabbas yasan ya fad'a SARK'AK'IYAR SOYAYYAH!!!. Me wuyar warwarewa, tabbas yana dakyau ya farga yasan meke damunsh'i.

Tsugunnawa Maisha tayi ta d'ora hannunta aka, tafara kuka, tunaninnika ne sukai mata yawa, for the 1st time da tafarjin kunyar Yah Mas,.

Dan tasan tabbas bazai ji dad'iba, saboda shima mutum ne kamar kowa.

Kunyarsace tasa ta kasa d'agowa inda sh'i kuma kamar ya fuskanta.

Ya tsugunna ya d'agota, kunyarce still yasa ta kasa d'ago da idonta ta fash'e da kuka, kukan abubuwa da yawa.

         COMMENTS, VOTE & SHARE.

          votes wattpad khairi muhd

      Gaskiya team#Maishamas kufa k'ara dagewa dan naga team#Mai sh muhd sunfi yawa.

#Rukyymuhd
#MaishaMas
#Muhdmaisha

  SARK'AK'IYAR SOYAYYA!Where stories live. Discover now