chapter 20

1.2K 76 0
                                    

💗💗💗💗💗💗💗
SARK'AK'IYAR SOYAYYAH
💗💗💗💗💗💗💗

       NA
FOULANI CERDIYA
       &
KHAIRAT UP

       "20"

A kaikaice Maisha ta juyo tace cikin fada muryarta a dashe"How could u be so stupid, kina kiran Mijina mijinki ,Hmmm Rukayya kenan kar ki manta ruwa ba saan kwando bane ki kalleni da kyau kinsan nafi ki cancanta da zama matar Yah Muhd, amma saboda San zuciya wai kike kiranshi mijinki, pls nd pls I beg don't ever try to say so again, if not I will finish you".

       Hushi Maisha take tana Nuna Rukayya da yatsa alamun ranta ya b'aci sosai.

"Toh uwata in na k'ara fada zakimun wani Abu ne?".

      Murmushi dayafi kuka ciwo maisha tayi tace
" Uhmmm toh ki kara fad'a mana".

       "Na fad'a Yah muhd Mijina ne, ki fita harkars........".

Ai Rukayya bata gama rufe bakinta ba, Maisha ta ware yatsanta Biyar ta zabga mata mari.

       Yah muhd mik'ewa yayi da sauri yana fadin" Maisha meye haka ne?".

Rukayya ta rik'e kuncinta saboda azaba, aikuwa ta daga Nata hannun ta taskawa Maisha mari.

Bata kai ga sauke hannunta ba Yah muhd ya mayar mata da Marin a kuncinta.

Aikuwa nan Rukayya ta d'ago idonta ya kaho kwalla wani Abu ya tokareta, yau ita Yah Muhd ya daka akan Maisha, kenan yanzu yafi ji da Maisha akanta, tabbas sai ta dauki mummunan mataki akan Maisha.

Tana cikin duniyar tunani rike da kunci ta jiyo muryar yah Muhd yana fad'a da k'ara jin ta baitabayi ba.

      "Wannan wace irin masifa CE? Wanne irin SARK'AK'IYAR SOYAYYAH kuke so kusani a ciki ne? Ke da kike babba kin tsaya kina mana hauka haba Rukayya don't be like childish mana, akaina zaki mari Yar uwarki Maisha?, Me kukeso na fadawa mahaifanmu? Nazo cikinku inason haddasa muku gaba ko yaya,? Ko so kuke Ku kashe ni,pls Maisha, Rukayyah get out of my sides I don't want see u here".

Ya karashe maganar yana daka musu tsawa.

Cikin firgici Maisha ta fita tana kwallah, inda Rukayya ta biyo bayanta, tana zuwa wucewa ta gefenta ta bangajeta ta wani wuce fuuu, girgiza kai kawai Maisha tayi tana mamakin wannan Yar uwartata.

Suna komawa d'aki Maisha kasayin komai tayi, can ta tashi tayi alwala tazo tayi ta nafilfili.
Inda Rukayya ta dauko wayarta ta Shiga rubutawa Yah muhd msg na ban hakuri Dan tasan yayi mugun fushi, tare da yi masa alkawarin bazata kara ba.

Shima bayan fitarsu zubewa yayi akan gadonshi, jijiyoyin kanshi sunyi rud'u rud'u, babu abinda yafi damunshi sai irin yadda yaga Maisha tabar dakin, yasan tabbas yanzu tana can tana fushi dashi.
     

Tashi yayi yayi alwala ya hau praying mat yafara nafil fili, tare da Neman zabin Allah ga dukkan al'amuranshi.

Ba laifi zuciyarshi tad'anyi mashi sanyi sosai, jin k'arar phone dinshi yayi alamar sako, ya dauko ya karanta, kawai ya wani ja tsaki a fili yace
"Mtswww ni kin zamar mun matsala wallahi".

          Memakon yayi reply din msg din saima number din Maisha daya fara nema, tana ta ringing baa d'agaba dayaga haka sai yayi mata msg da fad'in.

      " Haba sanyin idaniyar Yah muhd, Haba rayuwar Yah muhd,Haba Mata's, nasan fushi kike dani ko? Kiyi hak'uri, banjo dadin abinda ya faru tsakaninki da Rukayya ba, naso mu tsaya mu samu maslaha.

       Amma pls kada ki sake biye mata, kinji ai ko bakomai yayarki CE gaba tke dake, INA fatan zaki cire damuwar dake ranki, ki kwanta kiyi bacci kinji wifely, urs Yah Muhd _luv u!!!.

         Lokacin da wayar Maisha ke ringing tana sallah ne sai data idar tai shirin kwanciya sannan ta dauko wayar tata, nantaci karo da missed calls dinshi da kuma text msg dayayi mata.

Msg din ta karanta kawai tayi murmushi batare datayi masa reply ba tayi kwanciyarta, sedai me nanfa bacci yace baisan zancen ba, tuni ya Lula duniyar tunani, inda a hankali take jiyo sautin kukan Rukayya dake kwance kan Gado.

    Sai gab da assalatu sannan bacci ya saci Maisha inda a gurin Yah muhd ma haka abun yake.

Da sassafe kusan bakwai tana bacci taji ringing din phone dinta.

Bata duba ba kawai ta jona wayar a kunnenta, muryarshi CE ta dirar mata a kunne, ba tasan sanda ta had'e rai ba, kamar tana ganin shi .
Jin wani haushin shi take da tsanarshi.

       "Inajinka".
Abinda tace dashi kenan.
      Yana daga dakin shi a kwance yayi murmushi yace

"Kanwata lafiya dai, ko baki tashi ba".

      Yah Mas ya tambayeta.

" Hmmmm in Nata shi ma mai zanyi maka?".

     Dan waro idonsa yayi jin Kalmar data fito daga bakin Maisha, se yace da ita

     "Haba kanwatah inma laifi nayi Dan na tasheki daga bacci yi hak'uri ki koma anjima sai na kiraki".

         Bata bashi amsa ba ta katse kiran tana maijan tsaki a fili tace

"Mtswwww, aikin banza ni nama dauka Yayan love ne Ashe wancan mas dinne".

Rukayya dake kwance tanajin Maisha Dan tsokana sai ta fara waka da fadin

"uwargida amarya ake cemun kai ne Mijina ni kadai Yah muhd ba mai kwacemun kai ehhhhe".

      Murmushi Maisha tayi Dan tasan da ita take, amma bata kulata ba tayi wucewarta tayi alwala tayi sallar asuban da batayi ba.

Kitchen ta nufa ta taya Mamy da mai aikin su girki, kallo d'aya mamy tayi mata tace

      " ke zo nan".

Mamy ta fita daga kitchen din Maisha ta bita.

     Dakin Mamy suka Shiga Mamy ta kalleta da kulawa tace

"Maisha meyayi zafi ne haka? Kinga yadda idonki yayi kuwa, ko duk Dan ance anmiki miji ne?".

Kwalla ne ya zubowa Maisha ta sh'are tace" Wallahi Mamy ni Yah mu.........".

Bata kai ga karasa maganar ta ba Ya sh'igo dakin.

Vote@wattpad khairi-muhd

  SARK'AK'IYAR SOYAYYA!Where stories live. Discover now