chapter 15

1.2K 106 3
                                    

💗💗💗💗💗💗💗

SARK'AK'IYAR SOYAYYAH

💗💗💗💗💗💗💗

        Na
FOULANI CERDIYA
      &
KHAIRAT UP

    
    
vote @wattpad khairi_muhd

          "15"

Tafe take zata school a nitse take kana ganin ta kasan tarbiyyah ta wadace ta.

Tunda ta taho yaketa murmushi abinsa, ya hard'e hannayensa a kirji.

     Itama tana zuwa tai murmushi tace "Ina kwana Yah Mas".
        Lumshe idonsa yayi kafin yace" Ni ya kamata na fara H Yar kan wata ya ta tashi, Dan haka ki rik'e INA kwananki".

       Dariya tadanyi har hakoranta suka bayyana ta rausayar da kai tace"Hmmm Yah Mas kenan nifa sauri ma nake kada nayi late a school".

        "Nasani, nima bazanso kiyi latti ba Maisha,  amma meyasa bazaki kirani da mo'taseem dina ba sai Mas".
        " Hhhhm, saboda shi ne sunan ka ai kuma nafijin dadin kiranka haka".

       "Well......dama zan fad'a miki gobe zan tafi saudia, k'aro karatu, sai kuma bayan shekara 4 zan dawo nasan kafin sannan Maisha an zama y'anmata".

    Rufe fuskarta tayi da hijab dinta, tace" kai Yah Mas, gaskiya zanyi kewarka".

       " Kada ki damu kan wata nidai kawai ki bani abinda in na ganshi zan dinga tunawa dake".

        Lumsh'e ido tayi, ta xaro zoben hannunta ta mik'a masa tace"duk da nasan yamaka kad'an amma gashi kada kace nayi rowa".

Ta mik'a masa.

   Hannunshi ta kalla sai cewa tayi" nima ka bani wannan na hannun naka Dan bazakaimun wayo ba, ka anshen nawa".

Ciro mata yayi. Yana mamakin hali irin na Maisha wata kan halin yarintar yana nan. Mik'a mata yayi sukai sallama suna d'agawa juna hannu har suka b'acema juna.

      Bayan sati d'aya

Maisha ce rik'e da littafinta na Mathematics da aka basu assignment, gashi malamun naso baa gane bayaninshi, Dan a ajinma Maishan CE mai Dan ganewa to itama yau ta kasa.

  Parlour tazo ta zauna tana k'ara dubawa amma INA ta kasa.

Rukayya ta kalla da tunanin ko ta kaimata ko zata iya, tunda ta wuce ta a karatu.

Matsowa tayi ga Rukayya data hard'e a 1siter, sanye da dogon wando jeans da jar Riga.

      "Dan Allah Yah Rukayya ko zaki dubamun, wallahi na kasa saka final answer din".

Kallonta tayi ta tuntsire da dariya tace" kema kinsan ba iya maths nayi ba, da zaki wani cemun in duba miki, INA laifinma ki kahon Hausa danni nafi kauri anan".

       Numfashi Maisha ta sauke tace"Ashe Abba asarar kudinshi yake bai sani ba? Gaskiya zan fad'a masa ya sauya maki school".

         "In kin fasa ke ba Maisha bace ,banzar yarinya sai tsinannen surutu da iyayi, komai saikinwa mutum kadifire".

       
          Tafa hannu Maisha tayi tace" Woooooo andaiji kunya,ko sallah zaayi ma sai ansaki a gaba ai inagani jiyama Yah muhd ne ya ...........".

        "Me ni Muhd nayi?".
       Yah Muhd da shigowarsa kenan dakin yayi tambayar jin ana ambaton sunan sa.

    Rukayya CE ta Mike tace
" wannan yarinyar CE wai fa ta kahon assignment kuma tasan ba iyawa naiba danni karatun nan bafa son shi nake ba".

        Wani malulun abune ya tokarewa Yah muhd arai ya kalleta yace "fice daga dakin nan Rukayya indena ganin ki".

Ai Rukayya jin ya ambaci sunan ta da bai saba fad'aba yasa tasha jinin jikinta ta haye dakin su.

       Kallon Maisha yayi yace" taho in Nuna miki".
Shi ya Nuna mata harta gama.

Ta washe hakora tace"ngde Yah muhd wallahi malamins ne bai iya teaching ba gashi in ba muyi ba ya zanemu".

Gyada mata kai kawai yayi ya tashi ya fita.

Tundaga ranar Yah muhd ya soma yiwa Maisha karatu, yana Nuna mata yadda zatai assignment.
Ganin yadda take gane karatun da kuma kokarin ta da dagewarta yasa harya soma zama tare da ita suyi fira.

Har Takao wataran har d'akinshi take binshi suyi karatun, wataran kuma taita bashi labaran school din da yadda teachers dinsu suke, shi kuma hakan yana dashi nishadi, itakam Rukayya abun yana mata haushi, saboda yanzu Yah muhd ya rage Shiga harkarta.

Maisha kuwa kowa yana mamakin sauyawarta, da yadda suka fara shaquwa da Yah muhd. Sedai fa duk da shakuwarnan tasu wataran suna fad'a, kuma in fadan ya hadosu sai a rabu ana kuka wiwi.

THANKS ALOT FOR UR COMMENTS, WE REALLY APPRECIATED.

WE SALUTE U!!!.

Team#maishamuhd

  SARK'AK'IYAR SOYAYYA!Where stories live. Discover now