💗💗💗💗💗💗💗
SARK'AK'IYAR SOYAYYAH
💗💗💗💗💗💗💗NA
FOULANI CERDIYA
&
KHAIRAT UP"23"
"Yah muhd na meye naga fuskar Abba haka?".
Tash'in hankali ne k'arara a fuskar muhd, amma seya dake yace" hope dai babu inda yake miki ciwo?".
Itama murmushi tayi masa me kamar kuka ta daga mashi kai alamun eh.
Rukayyyah kuwa Abba tabi a baya tana kara zuzutashi tace"wallahi Abba haka suke kullum, wataranma fa Abba d'akinshi take tafiya, kuma ta kwana a can, in nayi mata magana setaki ji, tace wai INA ruwana ni kuma Abba ni INA tsoron Maisha ta kaho mana abun kunya n..............". Ta karashe maganar tana kukan munafunci.
Sosai Abba ya yadda da abinda tace tunda gashi ya gani, ai in ba rami meya kaho rami?.Mamy CE ta dawo daga unguwa ta tadda Abba sai zirga-zirga yake, Neman guri tayi ta zauna cikin Nuna damuwa tace"Aa Abban Maisha meyafarui. Naganka haka?".
Be bata amsa ba sai cewa yayi da Rukayya
"jeki kiramin su".
Fita tayi tana wani hararen mamy ta gefe, tana zuwa ta tadda su still a gurin.
Yatsine fuska tayi
tace" Abba yana kiranku".
Da sauri Yah muhd ya kalleta yace
"Yana kiranmu ni dawa?"." kai da wacca ya ganku tare mana".
Tana fadin haka ta juya ta koma parlon Abba.
"Yayan love wai meke faruwa ne? Nd meye haka naga waccan abar tanayi?".
" ki tashi kije ni bari naje na sako ko jallabiyya CE sai na sameki kije".
Yana fadin haka ya fita da niyyar sako Riga a jikinsa.Maisha tana sh'iga dakin ta samu guri ta zauna Mamy ta kalla tayi mata murmush'i tare da cewa
"Mamy sannu da zuwa, Ashe kin dawo".
Mamy bata cemata k'ala ba sai murmushi data yi.Ana haka Yah muhd ya shigo yayiwa Mamy sannu da zuwa sannan ya nemi guri Kusa da ita ya zauna.
Abba ne ya juyo fuskar nan tashi a had'e duk iskar dake dakin gumi ne yake ta tsatstsafo masa.
Yayi jummm yace
" Muhammad,Maisha!!!! Nagode nagode nagode!!!!.Irin tarbiyyar dama Dana Baku kenan? Yanzu INA so Ku gayamun wani Abu ya taba Shiga tsakaninku?".A rikice kowannensu yake kallon Abba ba tare da gane inda maganar shi ta dosa ba.
Yah muhd yayi kasa da kai yace
"Abba kamar yaya fa? Bangane me kake nufi ba?".
" Abinda aka cemun kai da Maisha kunayi mana shin ya abun yake?"."Alhaji wai mesuke yi ne"?.
Mamy ta tambaya hankalinta a tashe.
Maisha kallon Rukayya kawai tayi ta fash'e da kuka tace
" wallahi wallahi Abba ni baamun da mukeyi da Yah Muhd Fad'uwa nayi akan tiles shi ........".
"Shi ne Ubanki?".Abba ya Daka mata tsawar da tunda aka haifeta a gidan nan bai taba yi mata ba.
Kuka Maisha ta fash'e dash'i saboda razani.
" Alhaji kabi abun nan a hankali pls don't loss ur temper " .
Ajiyar zuciya ya sauke yace
"Ni bansan wani dogon zance, ke kuma da zaki CE inbi abun a hankali ai da kaina nagan su Dan haka zan yanke hukunci na yanzun nan".
YOU ARE READING
SARK'AK'IYAR SOYAYYA!
Romancea love story, this is a love triangle between 4 lover's.