💗💗💗💗💗💗💗
SARK'AK'IYAR SOYAYYAH
💗💗💗💗💗💗💗Na
FOULANI CERDIYA
&
KHAIRAT UP" 17"
Janyota Rukayya tayi aikuwa ta dawo baya, tangal kamar zata fad'i.
Ranta ne ya baci tace"wai ke Rukayyah what's going on ur head ne? Kina Abu kamar jahila".
"Ke Maisha ni kikiyayeni, ni kike kira da jahila?, wallahi in kika kaini karshe sai na fasa miki baki, sedai duk abinda zaa mun yau a gidan nan ayimun shi".
Mamy CE ta taho dakinsu saboda tagani idan sun tashi sallah sai kuma ta faraji yo hayaniyarsu, kamar suna fad'a.
Shiga dakin nasu tayi ta saki baki tana kallon su, a ranta tace oh Maisha da tsokana bari inji meye kuma ya faru." Ku meye haka daga tashi da asubar fari kun fara masifa".
Rukayya CE tayi wani Jan zuciya tace tana Nuna Maisha da yatsa"wannan abar CE take Neman zagi na, akan nace mata ta dena kwana a dakin Yah muhd, naga ai.......".
"Kika ga me Dan k'aniyarki?, kinga Rukayya in baki sauya wannan halin naki ba zan maidake gun goggo fa".
Goggon kakartace data fara rikesu kafin ya auro mamy.
Zunb'urar baki tayi " to Abba ai............".
Marinta yayi ji kake Tass" watakan ke baki da mutunci ko,ni INA magana amma kema kina magana ko, koma akan meye ni banason ji".
Yana gama fad'in haka ya fice daga dakin.
Mamy ma tabi bayan sa, Maisha kuma tayi sallarta anan tabar rukayya tana had'a kayanta wai gidan yah Nasser zata koma.
Misalin takwas maisha tayi shirin school ta fito ta gaida Abba. Tace"Abba kayi hakuri, laifin da mukayi maka dazu ni baason raina ba".
Murmushi yayi Dan tabbas Abba yana alfahari da Maisha, ko a waje ayi ta yabanta da kyawawan dabiunta,""Bakomai Maisha na, kinji tashi ki tafi Allah yayi miki albarka".
Fitowa tayi tafara fita daga gidan tajiyo sautin maganar Yah muhd yana kiranta " Maisha kin manta dayan book din naki fa a dakina kije ki dauko, ".
Karasowa tayi Kusa dashi da faraarta ta gaidashi ya amsa.
Dakin nashi ta Shiga ta dauko littafinta ta fito.
" Yah na tafi makaranta ".
" a dawo lafiya Yar Abba".
Goma dai-dai Rukayya ta had'a Yan kayanta a jaka ta saici hanyar fita , Dan ko mamy bata gayawa ba, ita a ganinta saboda mamy ba babarta bace shiyasa Abba yake mata haka, wai yafi son su Maisha.
Yah muhd tagani a kofar fita ta tsaya har ya karaso yace fuskarsa a hade"Saraki sai INA? Naganki da jaka da safiyar nan".
Hawaye ta fara masa tace"Ni tafiya zanyi gidan yah Nasser, tunda kaima yanzu kafison Maisha, ni yanzu babu mai sona. Maisha ta kwacemun kai ma".
Kukan ta sake fashewa dashi , sosai yaji tausayinta Dan dama shi yana tausayin Rukayya kasancewar mamanta ta rasu kuma tana yarinya.
Jaho hannunta yayi ya rik'e gam,ya Dan sassauta ya rungumota jikinsa yace"am sorry Saraki na, kema kinsan INA sonki sosai,Rukayya kuma kinsan ba abinda zai rabamu ni dake".
Karaf wannan kalma ta INA sonki Rukayya ta daki kunnen Abba, kuma ya ganewa idonsa.
Inda wannan kalma ta ruguza duk wani shiri na Abba.Komawa yayi cikin gida.
Rarrashinta sosai yayi, ya d'ago da ita daga jikinsa yace da ita"matsala ta dake daya CE Rukayya bakyason karatu, gashi yanzu kin koyo halin banza, bazaki sallah akan lokaci ba, sannan ba karatun Qur'an sai rashin kunya da kika kokarinma koya".
"Na dena ai Allah Yah na, toh amma zaka cigaba da kulani ai ko".
Murmushi yayi yace" kwarai kuwa Saraki na, yanzu muje in kaiki gidan yah Nasser din amma fa ba kwana zakiyi ba".
"Toh naji, bari in je in ajiye jakar kayan sai in dauko wata".
" Yawwa to hurry up ".
Koda sukaje gidan Yah Nasser ma baya nan, suna Shiga suka tararda Aunty Jamila (matar Yah naseer).Da faraarta ta karbesu, Dan tana da faraa sosai.
Gaisawa sukayi tajuyo ta kalli muhd tace" uhm da yake kaida Rukayya ne ai gashi ka zauna, amma Indai kazo gidan nan kamar Ana dukanka".
Murmushi kawai yayi yace"saraki ni dai tafiya zanyi, in na dawo zan biyo saimu tafi".
Sallama sukayi ya fice.
Aunty jamila ta kalli Rukayya tace"kun fa dace keda muhd wallahi, wayasani ma ko Yar gida zaayi".
Dariya Rukayya tayi tace"uhmmm to, nidai yunwa ma nakeji fa".
K'arfe biyar Yah muhd ya tashi daga office direct gidan Ummansu ya tafi, yana Shiga palorn ya taradda Maisha zaune tana yankewa Umma farce.
Dadi yaji sosai yadda Maisha take Nuna kula akan mahaifiyarshi.
Lah "Umma kamar nasan Yah muhd zaizo,".
Zama yayi kan kujera yace" me akayi da ake cewa kamar ansan zanzo.
Da faraarta tace"INA zuwa na tadda Umma zatayi girki, nikuwa nace mata a yi wake da shinkafa ur favorite, kuma sai gashi kazo".
Rausayar da kanshi yayi yace"Uhmmm ".Gaisawa suka fara da Umma, Maisha ta mike ta tafi kitchen Dan hado mashi abincin.
Hirarsu suke tayi Maisha tazo ta Jere mashi abincin ta k'ara komawa kitchen din.
Umma CE ta kalleshi tace" oh kaga Maisha yarinyar nan, tayi hankali ta nutsu, wallahi yaron nan kun dace kaida ita, mai zai hana ka nemi aurenta kada wani ya rigaka".
Sosai Umma ta bashi dariya ya Dan maze yace"............"
TOFA K'AK' K'ARA K'AK'A!!!!!.
TOH NIDAI FOULANI NACE DA KHAIRI WAI YA ABUN YAKE NE?
KUMA NASAN TAMBAYAR TAKU KENAN.
KUKASANCE DAMU.
VOTE @WATTPAD KHAIRI-MUHD
YOU ARE READING
SARK'AK'IYAR SOYAYYA!
Romancea love story, this is a love triangle between 4 lover's.