💗💗💗💗💗💗💗
SARK'AK'IYAR SOYAYYA
💗💗💗💗💗💗💗Na
Foulani cerdiya
&
Khairat up"14"
Murmush'i kawai Rukayya tayi.
Ameenuh ya shigo ya kalleta ya tab'e baki yace"ai Maisha tafi dacewa da Yah muhd wallahi Mamy ".
Harararsa yayi, Mamy kuwa tayi murmushi tace" wai Maisha da muhd da suke kamar kalanzir da Petir? Ai zamansu bazai dadi ba, sai dai Sarakin tashi."Heheehhe, Wa? Ni? Tab, Allah ya kiyaye wlh ni Yah Muhd yayi mun tsufa ma yah Ameenuh".
Maisha dake sakkowa daga stairs take fadin maganar.
Kallonta Yah muhd yayi yace" ke dallah matsa banza, ana maganar mutane kina sako mana baki, ni mezanyi dake jibarki kamar aljana,ke ko a kafa aka lik'an ke sai na yadda ke".
Tuntsirewa da dariya Ameenuh yayi yace "anayi munajin dadi woo Maishan Abba".
Mamy ma tai dariya tace" to dai kinji kewama yasa bakinki a ciki".
Fari tayi da ido ta murgud'a baki tace"ai dama inajinku, kawai shiru nai muku, kuma ma in banda abinka Yah Muhd ai kaima kasan ni na wuce ajinka ehhe"."Eyye?!!!!, Maisha ni kike fad'awa haka?".
Yah muhd yayi maganar yana mikewa tsaye ya nufota aikuwa da gudu ta sawa k'afarta mai tai sama.Bayanta yabi yana fadin"ai zaki gayamun dawa kike tunda ni saanki ne ko_".
Bayan kyaure ta buya, yana shigowa yafara nemanta, aikuwa tasa k'afarta ta shureshi ta sauka da gudu tana masa dariya, ganin in ya biyemata zata wahaldashi yasa ya kyaleta da zummar ya kamata hankali kwance.
Sati ya wuce watanni sun shud'e shekaru sun k'aru Inda Maisha tai shekara goma sha daya cif-cif, ta k'ara ky'au, iyayi ya k'aru, hazak'arta a makaranta ma tafi ta da. Inda Yanzu ta Shiga secondary tana jss 1. Yah rukayyah kuwa anzama budurwa.Alokacin kuma tuni Yah Nasser har yayi aure matar ma ta haihu. Yah muhd kuma ya gama Masters dinshi har ya samu aiki, yabar kasuwanchi, duk da dai yana Dan taba'awa kad'an.Yau jumaa, sun dawo daga gidan Baba ta chiranchi, Maisha hijab ne ajikinta dogo mai hannu har k'asa Inda ita kuma Rukayya sanye take da dogon skirt irin mai robar nan sai Yar rigarta da mayafinta karami Wanda tayi rolling dashi, ta girma sosai itama ta kara kyau.
Sauri suke suka sh'ige cikin gida kowannensu a gajiye, suna zuwa d'aki Maisha tai alwala Inda Yah Rukayya ta baje a Gado wai ta gaji.
Sallah Maisha tayi ta dauko Qur'an ta fara karantawa cikin k'ira'a mai dadin gaske.Sanye yake da wando bak'i sai Riga red yayi wani kyau sosai, takalmin kafarsa sau ciki ne sai agogon hannunshi shi ma mai kyau n gaske.
Cikin gidan ya shigo kasancewar dawowarshi kenan daga masallaci, cikin palour ya nufa ya tarar da Mamy da mai aiki suna Jere abinci.
Murmushi yayi mata yace"Mamy sannu da aiki ya gida",
"Lafiya lau Muhd".
" Su saraki kuwa sun dawo daga chiranchin?"."Eh sun dawo suna d'akinsu ma".
" OK."
Yace yana wucewa dakin
Tunkafin ya k'arasa sh'iga yafara jiyo k'ira'a wani sanyine ya ziyarceshi, Dan mutumne shi maison sauraron qur'ani.Cikin dakin ya Shiga ya tadda Maisha kan sallaya tana karatu, ya kalli saraki da tayi d'ai-d'ai akan gado daga ita sai shimi, tsaki yaja ya kada kanshi yace
"Wai ke meye yake damunki ne,".
Dagowa Rukayya tayi wacce batasanma yah muhd ya shigo dakin ba.Murmushi tayi tace" lah Yah na, yaushe ka Shiga.........".
D'aga mata hannu yayi yace"wai Saraki me kikeson zama ne, kinmayi sallah ?".
Mik'a tayi tace"wallahi nagaji ne Yah na, hutawa nakeyi kuma ma gaka ai lokacin ta bai k'ureba".
Tsakin ya kuma ja yace"wallahi kindaiji kunya, k'anwarki tasan tai sallah har tai bitar karatunta amma ke banda ke ko?,".
Mik'ewa tayi tace"Aa bari intashi inyi.......Yi hak'uri".Samun guri yayi ya zauna yana jiran saraki tayi sallar Dan yasan tas zata iya had'esu tace tayi da isha'i, tunda yanzu wani son jikin masifa ta koyo.
Maisha CE ta idar Da karatunta taje ta ajjiye qur'anin Inda yake ta dawo, tsugunnawa tayi tace"Yah muhd INA wuni".
"Lafiya lau".
Yace da ita tare da mik'a mata hannu sukai misabaha.Linke sallayar tayi, da hijab din ta tafi dakin Mamy ta gaidata sannan suka d'anyi fira ta tashi ta koma palor.
Acan ta samu Asleem da tasleem suna homework ta zauna tana koya musu.
K'arar dawo war Abba sukaji su Asleem suka fita da gudu suna ga Abba oyoyo.TAMBAYA GA MABIYAN WANNAN BOOK
*SHIN KUNAJIN DADIN BOOK DIN NAN?
*ME KUKE TUNANI TSAKANIN MUHD MAISHA & RUKAYYA
*WAKE NUNA ALAMAR SO TSAKANIN MUHD DA RUKAYYYA*WAYE STAR DIN A GANINKI?
*TEAM WA KIKE?
#TeamMaishmuhd❤
YOU ARE READING
SARK'AK'IYAR SOYAYYA!
Romancea love story, this is a love triangle between 4 lover's.