💗💗💗💗💗💗
SARK'AK'IYAR SOYAYYA
💓💓💓💓💓
Luv storyWritten by; FOULANI CERDIYA &
KHAIRAT UPwattpad@khairi-muhd
"5"
"Kiyi sauri Maisha, in ba haka ma mu tafi mu barki".
Rukayya ke fadin haka ga Maisha sakamakon shirin da suke zasuje r/zaki gidan Umma Maryam(Umman Yah Muh)."Ai se Ku tafi tunda gidan Ummanku ne, naga Umman ma tafi murnar xuwana ba naku ba ehe".
Ta fada tana karasa shafe janbakin ta." Ah Pretty ta a sali irin wannan kyawun haka? Wlh da baki shafe shafen nan ba".
Ameenuh dayake shigowa dakin a lokacin yake tsokanar Maisha.
Murmushi tayi tacigaba da kallon mudubunta.
Kallon b'arin da Rukayya ke zaune yayi yaga ta had'e rai,ga wani uban gumi da take sai kace taiwa sarki karya.
Ameenuh me zaiyi inba dariya ba yace.
"Wai..... Tab gaskiya Ruky ki gyara kwalliyarki jibifa yadda Maisha ta cinye ki". Ya karasa maganar yana Dan mata kwalo.
Aikuwa nanfa ya kunna Rukayya Dan ta tsani ace Maisha ta fita kyau ko kuma suyi kwalliya ace Maisha tafi yin kyau.Zumb'urar baki tayi taja mayafinta ta fita tana cin mur tazo sauka daga stair kenan saiga Yah Muh.
Kallonta yayi yaga ta wani kumbure, yace" Saraki na waya tab'anke?".
Yayi mata tambayar da kulawa."Ba Yah ameenuh bane yace Wai banyi kyau ba,...,..Kuma tun dazu nake jiran Maisha ta fito ka kaimu gidan Umma amma tak'i".
Tsaki yaja don har ransa yaji haushin bacin ran sarakin sa.
" muje".
Yace da ita fita sukayi basu zarce koina ba sai R/zaki.
A can gida kuwa Maisha ta gama cin kwalliayarta, ta dauko pink les Riga da skirt, tasaka kayanta sannan ta fesa turare.
Mamy ta shigo tai dariya tace"Oh Maisha na irin wannan kyau haka sai INA".?
Fari tai da ido sannan tace"Sai gidan Umma maryam kinsan fa nasan tanacen tana jirana".
Dariyane yaso kwacewa Mamy saboda tana jin lokacin da suka fita abokan tafiyar tata.
"Ai kiyi SAURI to kada su tafi".
Mamy ta fada tana shigewa daki".
" Maisha zo in miki photo, irin wannan kyau kamata yayi a nunawa Abba gaskiya".
Ameenu dake zaune still ya yi maganar.
Yatsine hanci tayi sannan tace "Ok yimun ko kala uku ne".
Shi ya bata style tayi ta gama ta fita sai dai me?
Wayam ba kowa ba Yah muh ba Yah Rukayya.
Kwalla ne ya cika mata ido, amma saita tuna ai itama zata iya zuwa da kanta, hakan yasa batare da Shakkar komai ba ta fice daga gidan batare da kowa ya sani ba.Titi ta fita ta dinga kalle kallen hanya Dan ita batasan ma tayaya zata tafi ba tunda bata da kudi.
Can kawai ta hango wani matashi zaune yana duba wani littafi, ta nufi gunshi tace cikin iyayi " Dan Allah Dan uwa in tambayeka mana".
Mamaki yayi sosai ganin y'ar yarinya ta tunkaroshi kuma tana kiranshi Dan uwa bama yaya ba ikon Allah.
"Inajinki Yar uwa".
Ya kafeta da ido." Aina zan hau motar R/zaki pls ni bakuwa CE bansan garin nan b......"
Dariya sosai ta bashi yai murmushi yace"Allah ko".
Tace"kwarai".
Tana wani juyar da kai yadda Yan Mata sunayi."Toh keda a wani gari kike"
Ya tambayeta yana leka fuskarta.
"Ni?......Ni yar Malaysia CE".
" Hhahhhhhhhh, Malaysia? Kice bama Yar kasar Nigeria bace ke, Toh a Malaysia Aina",.
"Uhmmmm......Uhmmmm a.......a dai can nake fa".Dariya yayi sosai ganin yarinya da wayo ga iyayi.
" OK.......never mnd muje in kaiki to, amma acan kike ko?". Ya fadi hakan sbd yaga akwai alamar wauta a jikin yarinyar nd kada ta fada mugun hannu.
"Aa kai dai muje zan baka labari".
Tayi gaba shi kuma ya shiga gidansu ya dauko motar.
Seda suka fara tafiya ta juyo ta kalleshi tace" hmmm waifa Yayanmu ne zai kaimu gidan Umma maryam shi ne Dan na tsaya ado ya tafi ya barni, kuma zan fadashi da Abbana sai ya masa fada ko ya zaneshi kaga Abbanmu fa duk yafi sona saboda ni CE autar sa kuma kaga ko shi Yah Muh yafiye son mugunta ta, kuma Dan Allah banyi kyau ba? Kalli fa".Tafara maganar ko hadiyar yawu batai.
Murmushi yayi ya lumshe ido yace"sosai kam".A dai dainan suka iso ya kalleta yace "to gamu mu shigo rijiyar zaki ina zamuyi".
Tagumi ta buga ta ajiyar zuciya tace" Tab nifa bansani ba nifa kawai nasan a nan take a na zuwa sai aga wani guri kamr kasuwa sai a shiga sai aje"."Ikon Allah, to mukoma na ajiyeki a Inda na dauko ki ko".
A zuciyarsa yana tunanin koma aljana ya dauko.Tabe fuska tayi sannan tace" shikenan ai ".
Juya kan motar yayi ya koma Inda ya dauko ta sannan ya bata chocolate da sweet da yawa a yar bag.
Aiko taji dadi tayi murmushi tace" bama kasan yaya suna na ba, koda yake kagafa gidan mu a canyake".
Ta Nuna masa wani layi.
"Ok ,muje in rakaki, amma ki dena fitowa waje ke kad'ao saboda mugaye".Suna zuwa kofar gidansu ta tsaya tana CE masa"yau zan cewa Abbana na hadu da wani Yayah, bayan Yah M.......".
Cak ta tsaya da maganar sakamokon hango Motar Yah muh na shigowa layin ai ba shiri Maisha ta falfala da gudu tana d'agawa Sabon Yayah dinta hannu.Juyawa yayi yana murmushi alokacin motar Yah muh ta wuce shi.
Kallonsa sosai Yah Muh yayi da ido yana tunanin meye yasa Maisha ta fita, kuma Aina tasan wannan guy din daya gansu tare.
A ransa yace " Kai Maisha trouble CE wlh, yarinya kamar me jinin aljanu zatamun bayanin Aina tasan wancan guy din Mtswwww".
YOU ARE READING
SARK'AK'IYAR SOYAYYA!
Romancea love story, this is a love triangle between 4 lover's.