chapter 60

1.1K 88 2
                                    

💗💗💗💗💗💗
   Sark'ak'iyar soyayya!
        ❤❤❤❤❤

foulani cerdiya
      nd
khairat up

F.O.W

Vote @wattpad khairi_muhd

       "60"

"ta ido ya mata alama da yana san ta biyo shi waje."

"ita kuma ta make kafada"

"yay kicin2n da fuska alamar rarashi da ta zo dan ALLAH."

"Su'ad ne ya ce aboki me hoto na magana wai saurin me ka ke anjima fa za a kawn maka matar."

"dariya aka saka shi kuma ya fuske ya sha mur."

"haka aka yi ta hotuna a gidan late alh.auwal."

"da yamma aka dauki amarya zuwa gidan angon ta wanda yake cike da kaunar ta da begenta. burin sa ya gan shi ga maisha ya hukunta ta a kan wahalar masa da zuciya da ta yi na tsawon lokaci."

"da misalin karfe tara da rabi muhammad da su'ad da ayman suka sauka gidan muhammad inda ya hanasu shiga ku dakata daga nan kawai nagode yanzu zan turo maku wayanda zaku kai gida ae kun gan ta da yawa lada ya isa."

"su'ad ya ce gaskiya ne aboki ae mun gama maka wahala addu'ar fa."

"ae ku mun a nan nagode da zumunci da kauna saida safe."

"ae ba komai,amma muhammad ko mu kulle maka gida daga waje da kwado zuwa next week!"

"dariya suka saka sossai."

"da sallama ya shiga gidan nasa, ya fadawa kawayen maisha guda uku suje ana jiran su, za a maida su gida. sallama suka yi da maisha wadda take nannade cikin laffaya wata grey da ratsin fari a jiki."

"fuskarta a kulle ruf haka suka yi musabaha, da kawayen ta suka kuma musu addu'a."

"waje ya koma ya kulle ko ina ya tofe ko ina da addu'a sannan ya koma dakin ya kare mata kallo tun daga sama har kasa."

"hakika maisha ta nada qualities wadda mace ta kamata ta samu irin wadda ko wanne miji ke so, ga body ga kyau ga zazzakar murya."

"a hankali da nutsuwa ya ce *MAISHA!* with passionate love da intense care ya saukar mata da kasala a duk wata gaba ta jikin ta."

" *MAISHA*, yau ubangiji ya nuna mun wannan rana me albarka da tarin farin ciki a tattare da mu ni da ke, ya zama dole mu godewa Allah, mu kuma gode masa da ya cika mana burin mu "

"duk wani abu da ya faru mukadiri ne daga Allah kowa da yadda Allah yake tsara masa rayuwar sa, tun lauhul mahfuz an gama komai,maisha irin son da nake miki ke shaida ce kuma ke ganau ce irin san da nake miki zn iya komai dan na kasance dake a rayuwata."

"a lokacin da ameenuh ya zo da batun yana san ki da aure wallahi da a lokacin ya hallata a kashe wani ko kashe kai ina tabbatar miki da cewa a lokacin cikin daya zan aikata daya."

"da sauri ta daga kanta ta sa laullausar hannun ta ta kulle masa baki ta na zubda hawaye hade da girgiza kai ta ce yah nah Allah ya sani, nima ina san ka ina kuma kaunar ka yah muhd lokacin da muka rabu ni kadai nasan wahalar da zuciya ta , ta sha a kan rashin ka, a duk lokacin da nake ganin ka tare da yah rukky tamkar na fada wuta haka nake ji. kuka nake ba dare ba rana saboda kishin ka."

"haka nima in na ganki da motaseem sai na ji kamar na hada ki da shi na murkushe ku sai dai na hakura na tausa zuciya ta na danne."

"ajiyar zuciya ya sauke ya ce hushh, maisha let bygons be bygons mu manta da baya abunda ya faru ya faru! mu yi kokarin gina rayuwar mu ta hanya ingantaciya,tasfta,amana,yarda,da fahimtar juna, da kaunar juna, maisha in na miki laifi ki fada mun a take dan na gyara , kema in kin mun zan fada miki,saboda mu zauna lafiya kuma kin san ni mutum ne me kishi ki kiyaye."

"insha Allah zan kasance me biyayya a gare ka da gujewa bacin ranka da kasancewa me kusanci da farin cikin ka fatana Allah ya bamu zaman lafiya da kaunar juna hade da zuri'a dayyaba!"

"amin my maisha ya fada hade da rungumota jikin sa yana sauke zazzafar ajiyar zuciya tashi maisha tashi2 muje muyi alwala muyi sallah ya sa mana albarka a zamantakewar mu ni da ke tashi my lobe."

        VOTE
       SHARE
      COMMENT!

*TEAMSARK'AK'IYAR SOYAYYAH!*

HOPE U GUYS ARE ENJOYING?

KEEP VOTING,COMMENTING,AND SHARING WE GIV U THE BEST.

  SARK'AK'IYAR SOYAYYA!Where stories live. Discover now