[10/26, 11:03 AM] Cerdiya😍: 💗💗💗💗
SARK'AK'IYAR SOYAYYA!
💓💓💓💓💓💓
Luv story
Written by; FOULANI CERDIYA &
KHAIRAT UPWattpad khairi-muhd
"2"
A zazzaune suke kowannensu ya dauko books dinsa mai assingnmet nayi, mai karatun bita yana yi.
Shigowar sa gidan kenan rai a hade saboda Bacin ran fadan da Abba yayi masa akan Maisha, shi abunnan yana damunsa ya rasa mai yasa Abba baya iya ganin laifinta. "mtsww".
Yaja tsaki palorn ya shiga inda ya tadda Rukayya da Ameenuh suna zaune suna game,Asleem da tasleem ma da suke Yan nursery suna homework.
Hararar Ameenuh yayi yace" Kai meye haka?, maimakon kayi karatu ka wani zauna kana buga game".
"Aini Yah Muh na gama yanzun nan ka tambayi Rukayya".
" wai haka Saraki?".
Ya tambayeta yana kafe ta da ido yarinyar tana burgeshi, yana yin shiru shirunta da kuma Jan ajinta.
Sai dataja class sannan tace"Eh mana".
"OK".
Ya kalli barinsu Asleem bai hango Maisha ba hakan yasa ya mike ya nufi dakin Mamy, ai tun kafin ya karasa ya jiyo muryarta tana rera waka irin ta Yan nursery da" I luv u, u luv me we are happy Family......."
"Mtswwww"Jin sautin tsakinsa yasa tai sauri ta katse wakar da take ta wayance da tsugunnawa tana nemon Abu.
Jan gashinta yayi ya murtuke fuska yace"ke baki da aiki sai rera rhyme ko?, where is ur assignment?".
Kallon Kusa da ita tayi ta Nuna masa da hannu.
Murde kunnenta yayi yace "Can't u open ur mouth nd talk"?. Ya daka mata tsawa tare da zare ido.
" Ah......ah......I can, gashi nan ai nayi nama gama".
"OK, bari naga inbakiyi dai dai ba, hmmm wlh saina zaneki stupid girl".
Daukowa yayi ya duba yaga tayi dai dai, a ransa yace ita sai wasa amma tana da kokari ba kamar Rukayya da in aka bata assignment saita nemi Dan tayi ba.Amma duk da yaga tayi dai dan,muguntar tana nan yace a ransa saita masa explain Dan ya kamata da hujjah.
" Ke zo nan".
Tasowa tayi tana sussun da kai tanemi gu ta zauna
Mika mata book din yayi yace" Oya yimun explain ina jinki".
Batare da bata lokaci ba Maisha ta fara masa bayani dalla-dallah harda Dan iyayinta wai irin yadda Aunty din take musu.Sosai yaji ta burgeshi, amma bai nunaba saima dungure mata kai da yayi yace" ki gode Allah u escaped da sauna b'allaki a gidannan naga ni".
Ya tashi ya fice daga dakin.
Aikuwa yana fita Maisha tabi bayansa tana masa gwalo.
Tace"mutum sai muguntar balai, ni na rasa mema na tsare masa duk su Yah Rukayya baya musu haka saini, wallahi nima wataran sai na rama ehhe.Su biyu ne a gidan kawai daga ita sai Rukayya, Maisha ta kalli Rukayya tace"wallahi ni yau Yah Rukayya wainar fulawa ma nakeson ci".
Banza Rukayya tai mata saboda ita batason surutu, batason magana ma ko kadan."Wallahi bari naje store na auno fulawa ko kwankwan biyu CE inzo ins soya".
Jin tace zatayi suya yasa Rukayya tace" Aa fa Maisha kinsan halin wannan rub'bb'an kirjin naki,ke aiki ma bayi kike ba amma zaki tsiri suya'.
"Toh ai nasan innace ki soyan ba soyan zaki yi ba kuma ni gaaskiya inason ci".
" nima fa ke inaso, bari inyi sauri in soya mana kafin Mamy ta dawo".
"Yawwa Yayanah shi yasa nake sonki".
" uhm". Kawai Rukayya tace tare da mikewa ta nufi store din gidan danta auno fulawar.Da aka gama suyar waina sai ta kama kowa faifai biyu zai samu da rabi tunda guda biyarce.
Nan suka gama cinye bibbiyunsu, Maisha ta jaho dayar zata fara ci, Rukayya ta galla mata haraara tace"sannu sara, in soya wainar kuma ke kici uku nida na soya inci biyu baki isa ba wallahi".
"Tab, danke kika soya wallahi bazan yadda ba,naga aini nace inason wainar bake ba".Rukayyah tashi tayi ta fito tsakar gida tana fadin" baki da hankali kiyi da saanki kinsan ni ba saarki ba CE wllahi".
[10/26, 11:06 AM] Cerdiya😍: Biyota Maisha tayi tana rigimar saita bata, nanfa Rukayya ta tureta ta fadi kasa tasa ihu, tana wallahi saita bata, janyo mata riga Maisha tayi, tana Allah ya isa wallahi indai baki bani ba kuma saina fadawa Abba"...."MAISHA!!!."
Taji an daka mata tsawa ta juyo a razane ganin sa yasa ta fara tsula fitsari tare da sulalewa kasa.
YOU ARE READING
SARK'AK'IYAR SOYAYYA!
Romancea love story, this is a love triangle between 4 lover's.