chapter 54

961 73 0
                                    

💗💗💗💗💗💗💗💗
SARK'AK'IYAR SOYAYYAH
💗💗💗💗💗💗💗💗

        Na
Foulani cerdiya
Khairat up

          "54"

"Oh sorry ai bansani ba, but amma ai kawarki tacemun baki da aure yanzu".

       " to ni nace maka INA dashi kuma ga Mijina ".

       " fine......Shikenan ".

Binsa da kallo Yah Muhd yayi har ya bar gurin tare da mamakin Maisha.

Hannu ya mik'a mata itama ta mik'a masa ya rik'e hannunta ya zagaya da ita mota yana fadin

        " muje kimun rakiya".

Shiga tayi tana kallonsa da mamaki tace

         "Uh INA zamu bikifa muke ya zai na bar gidan biki in tafi yawo".

      Harararta yayi taja bakinta tayi tsit.

Gidan Ummah sukaje tare da shi.

Umma ganinsu ya sata matukar farinciki.

   Sai faraarta take saboda kara ganin dacewar da Muhd yayi da Maisha.

         Gaidata sukayi cikin sakin fuska tana tambayar yaya suke kuma daga INA suke.

        " gidan biki nakefa Ummah kurum ya kama ya xo ya taho dani".

Maisha ta fad'a tana zunburar baki.

         Doke kanta Yah Muhd yayi yace
           "Ummah siriki na samu tanaimun bakin ciki."

           "Toh abun naka ya zama zolaya ai".
Umma ta fada tana harararsa alamun ya kara Sanya ya rasata a karo na biyu.

Murmushi kawai yayi yana jin son mahaifiyarshi a ranshi.

Sai 4 ya dauko ta suka taho tare, sao da yayi mata warning kan ana kai amarya ta dawo gida in ta wuce 7 ita da shi ne.

           After 2 weeks

" Little.........Little where are u? Ur mum is back".

       Maisha da shigowarta kenan ta dawo daga makaranta take ta kwalawa little kira Dan yanzu ya fara Dan koyar tafiya.

         Aikuwa yana jinta sai gashi ya fito yana ta balbala dariya, da Dan gwarancinsa.

Daukarshi tayi ta rungume tana juyi dashi tana mashi waka.

Shi kuma sai dariya yake ta bangalawa kamar gonar auduga.

         Shi ma da yake tsaye murmushi yayi yana kara jin son Maisha a ransa saboda yadda take kular masa da jininsa.

        
            Juyi take dashi tana masa waka,ai tana juyawa ta had'a ido biyu dashi tsaye ya sakale hannunshi sai murmushi yake.

Ja tayi ta tsaya tana zazzare ido.

Matsowa yayi Kusa da ita ya kama hannun Little yana Dan masa wasa.

         D'agowa yayi ya kalleta ta kafeshi da ido ko kiftawa batayi, sai ji tayi yace

         "Maisha zaki aureni?".

         Dummmm gabanta ya fad'i take fuskarta ta sauya idonta yayi jajur a zahiri tanajin bazata iya auren Yah Muhd ba, saboda Yah Rukyy.

          Jin tayi shiru ne yasa yace cikin tsoro da fargabar amsar da zata bashi?

         " Maisha zaki aureni?".

  SARK'AK'IYAR SOYAYYA!Where stories live. Discover now