💗💗💗💗💗💗
Sark'ak'iyar soyayyah!
❤ ❤❤❤
_written by foulani cerdiya_
_&_
_khairat up_*vote @wattpad khair_muhd*
"25"" MAISHA NA"
"Juyo wa tayi ta bishi da wani kallo da kyar ta ce ina wuni?"
"lafiya lau maisha ya ki ke?"
"alhmdulilah ya mama?"
"tana lafiya tana ma gaida ki yaushe zaki je ki gaida ta?"
"muje mu zauna ta fada."
"be fasa magana ba ya ce mata kin kwana biyu baki je kin gaida ta ba."
"zan je ae"
"maisha na wallahi ina san ki ina kaunar ki, maisha ki tausaya mun koda digo goma ne a cikin kaso dari ki soni! wallahi maisha tunda ki ka juya mun baya na kasa sukuni da kyar nake bacci."
"yah mas zan aure ka na yarda amma ina da sharadi"
"farin cikin fuskar sa ya karu maisha na miki alkawari duk abinda ki ke so zan miki ni dai kawai ki aure ni."
"ajiyar zuciya ta yi ta ce zan aure ka amma ban yarda ka taba jiki na ba da sunan hakkin ka har sai na kammala karatu na sannan ban yarda ka ga ind harkokina ba kana sa mun takunkumi ko ido, bana san ka dinga takura mun da maganar so"
"amma maisha ta ya ki ke so muyi irin wannan zaman i love you..."
"prove it ta fada tana mikewa"
"zauna maisha na yarda har sai lokacin da ki ka yarda cewa ki na so na kin kuma yarda dani "
"nagode kasan me ne ne wahalar so i need time na yi recovring daga rashin abun sona da nayi!"
"shi kenan nagode hakan ma zan koma ki kula da kan ki"
"uhm kawai tace dashi ta koma cikin gida."
"tun a waje kiran yah muhd ke shiga wayarta amma taki dauka tun bayan abinda rukky tayi dazu taji ta tsani kowa ma da komai a kan yah muhd rukky ke zagin mami to ta bar mata shi har abada wasu hawaye suka zubo mata a fuska ta zauna kan kujera. text ya shigo mata.
_kanwata zaki iya fada mun dalilin kin daga waya ta?_
"tsaki ta yi ta ajiye wayar a gefe ta dafa goshin ta."_raini ne ko me? ko dan kinga ina wahala a kan ki?_
"reply ta masa tana kuka tana rubutawa.
_yah muhd da fatan ka isa gida lafiya,ina bakin ciki wajan rubuta maka wannan sak'on yah muhd ni maisha na hakura da kai na barwa rukky kai ka taimaka ka daina kira na ka manta da cewa mun taba yin wani abu soyayya ka rike sarakin ka na rike yah mas dina.yah muhd kamar yadda ka fada muyi wa abba biyayya mu hakura da juna kai dan'uwa na ne haka nima,yah muhd ina san ka mun alkawarin mantawa dani let's do it for our parent's rukky tana san ka zata kula da kai kaima kasan hallayan ta zaku zauna lafiya.nima yah mas na sona ze kula dani.iya sakayyar da zan ma abba kenan a irin kaunar da yake mun tamu kaddarar kenan.baza mu taba auran juna ba duk da mun so juna. maishan abba 😭_
"innalilahi kawai yah muhd ke maimaitawa yaji wasu siraran hawaye sun zubo masa.be san haka so yake ba sai da ya shiga cikin sa ya Allah""dafa shi umma tayi ya juyo subahanalahi muhammad me zan gani?"
"umma na rasa ta wallahi na rasa ta umma..."
"muhammad wai me yake faruwa ne? na gan ka ,ka dawo da kayan ka me ya faru?"
"umma abba ne ya koro ni daga gidan"
YOU ARE READING
SARK'AK'IYAR SOYAYYA!
Romantizma love story, this is a love triangle between 4 lover's.