💗💗💗💗💗💗
SARK'AK'IYAR SOYAYYA❤❤❤_Gajeran labari_
_written by foulani cerdiya & khairat up_
_vote @wattpad khairi_muhd._
"11"
"ameenuh na shiga d'akin wan na su ya tarar da shi a zaune ya dafe kan sa wanda yake sara masa kaman me tsabar zafin kwalbar."
"rud'ewa ya yi ya ce subahanalahi yah muhd garin ya ka ta ka kwalba?"
"ameenuh kai ni chemist tukuna ka ji ko? "
"fia ya yi daga dakin ya dauko mukulin mota a falo da ke sakale a jikin kusa,mami ta ce ameenuh ina za ka je kuma?"
"mami zan kai yah muhd asibiti ne"
"asibiti kuma me ne ya same shi?"
"kwalba ya taka a dakin sa ba ki ga yadda ya zama abun tausayi "
"inallilahi muje kamin nan ina zuwa dauko shi."
"me aikin ta ,ta kira ta umarce ta da ta dauko parker da tsintsiya ta share dakin su yah muhd."
"da taimakon ameenuh ya taka ya kai shi mota."
"maisha da ke kan kujera na ji wani dadi ya lulube ta taji wani sanyi a ranta an fada maka mu din na wasa ne?"
"za ka kuma mun shishigi ae a al'amurana yah muhd kawai ta fada tana tafa hannu."
"saraki ta ce ke me haka ki ke mana tafi da dariya?"
"ina ruwan ki? ta fada tana zumburo baki gaba."
"yah muhd din yaji ciwo amma ki ke murna?"
"and so? sai me? yah naseer ne ya ji ciwo?"
"saraki ta bude bakin ta cike da mamakin maisha ta ce maisha fada mun ke ce ki zubar masa da kwalba a d'akin ko?"
"ni kuma? ta fada tana zuba mata harara."
"mami ta katse musu fadan da suke yi ta hanyar musu tsawa ku mun shiru malamai mara sa hankali kawai go inside and sleep "
"sum sum suka bar falon suka yi d'akin su ana yar ture2 da harare2n juna."
_chemist_
"an masa allura bayan an ciro kwalbar daga kafar katuwa kuwa ta shiga sossai,aka wanke masa aka ba shi magunguna ma."
"da za su koma gida ne yah muhd ya ce ameenuh mu biya ka siyo mun yogurt da nama yunwa nake ji kuma ga magani!"
"tam"
"mami na jiran su a falo ta dinga masu sannu ,an wanke? an ciri kwalbar?"
"eh anyi ga magunguna ma an bashi."
"to allah ya sauwake"
"amin amin"
"a nan ya zauna kan kujera ya sha yogurt ya hada da naman sa sannan ya sha maganin."
"saraki ta fito daga dakin ta ce sannu yaya na da zafi?"
"uhm uhm saraki baki yi bacci ba?"
"eh na kasa yin baccin ne shi ya sa ba zafi ko?."
"ya lumshe idanuwan sa ya ce da sauki sarki go and sleep kin ji ko akwai school gobe fa"
"to sai da safe."
"saraki na dawowa ta ce wai ya daina tafiya ne? ya zama gurgu ne?"
"bakin ki ya sari danyan kashi na gobe da sassafe da zaki yi."
"haha wowoh wayyo allah na, yah muhd gurgu."
"ta jefa mata fillo ita kuma ta kwanta tana dariyar mugunta."
"washe gari suka shirya dan tafiya makaranta.yah muhd ya fito yana dingisawa ya hau dinning dan yin break.""ina kwana yah muhd ya jikin?"
"da sauki saraki an fito?"
"uh"
"yah muhd ina kwana? "
"lfiya lau maisha"
"tana driya ta tsuguna ta danna masa kafar ciwon "
"argh ya fada da karfi."
"ayyo sannu yah muhd ashe da zafi?"
"ya watsa mata wata harara wadda ta sa maisha nutsuwa ta kame ta dau cup din tea din ta, ta kai bakin ta tana sha."
."ameenuh je ka kaisu makarantar"
"to yah muhd sai na dawo"
"a dawo lafiya."
"bayan tafiyar su mami ta ce ni ko muhammad ya akai ka fasa kwalba ka taka haka?"
"wallahi mami ni kai na ina mamaki kaina ya kulle ni dai nasan bn fasa kwalba ba da zamu fita da muka dawo ma ban shiga dakin ba fa sai da na dawo daga masallaci tukuna sai na je dakin kawai naji na soki abu."
"abun da akwai ban mamaki wallahi allah ya kiyaye gaba."
"amin!"
YOU ARE READING
SARK'AK'IYAR SOYAYYA!
Dragostea love story, this is a love triangle between 4 lover's.