💗💗💗💗💗💗
Sark'ak'iyar soyyayah!
❤❤❤❤❤_vote @wattpad khairi_muhd_
"39"
"haka aka kai abba gidan sa na gaskiya,maisha kam tamkar gawa haka ta kasance dan gaba daya bata uhm bare uhm'uhm mutuwar ta tabata saboda yadda ta saba da abban ta."
"sai ga rukky an nutsu ta matsa gun maishan ta mika mata plate din abinci ta dafa kafadunta maisha ta fada tana kuka ita ma juyowa maisha tayi tana kallan ta ki daure ki ci abincin nan kin ji?"
"na koshi ni me zan kuma so nayi a rayuwa ta bayan abba na ya tafi ya bar ni!"
"uh'uhm ki ci saboda abba amanar juna ya bamu ki manta da baya ta rungume ta suka saki kuka dukan su gaba daya yan dakin suka tausaya musu"
"mami kam dauriya take kawai amma ya zata yi tayi rashin miji gwarzo na gari tsayayye da san iyalin sa."
"haka aka share makoki maisha da rukky sun jone sun dinke tare suke komai."
"bayan kwana arba'in baffa usman suka sa aka yi rabon gado aka sallami wayanda suke bin abba bashi."
"wata iriyar shakuwa ce ta kullu tsakanin yah mas da kuma maisha wanda hakan ya faru ne saboda hudubar abba ta manta da komai ta rike mijin ta da hannu biyu."
"yau ma tana zaune a kan kujera ta dau wayar ta da ke kara ta dauka ta kara a kunnen ta."
"hello yah rukky ya gida?"
"alhamdulilah ya ki ke?"
"ina lafia lau wlh"
"ya babyn mu?"
"baby ma haka naji ki shiru ne dama kwana biyu."
"kin gan ni ina nan zuwa ae."
"to Allah sa dan kullum haka ki ke fada ko dai kina rike da ni ne har yau?"
"ah a wallahi makaranta ne ta rike ni wallahi. amma zan zo cikin satin nan."
"to ina jiran ki nima ai kin ga ma yanzu gun mami zan je na duba ta dasu amira"
"ah wayo baki fada mun ba da na fada masa mun je tare amma ba komai zan je daga baya."
"to ae shi kenan ki kula mun da baby na da kyau dan ni ce uwar goyon sa/ta"
"haha ae in kika ce a baki ma za a baki kin manta ke ce fa er gata er gaban goshin mu darajar abban mu."
"haka ne nagode sai anjima"
"to ki gaida yah mas"
"ze ji kam "
"suka ajiye waya ta na juya wa taga yah mas da dariyar ta ,ta tarbe sa welcome mijina 😄"
"youwa ke da wa? ki ke ta nishadi?"
"yah rukky ce naji dadin yadda ta manta da komai ta kuma maida mami mahaifiya a gun ta "
"hmm kawai ya ce ta mike ta kawo masa ruwa me sanyi ya sha."
"dama ina so na tambaye ka jibi zan je ni gidan yah rukky tana ta korafi ban je ba."
"ya bata rai ya mike tsaye gaskiya baza ki ba."
"saboda me ?"
"ke ma kin sani ai "
"amma dai kasan da ne kuma yah rukky er uwa ta ce dan me zaka raba mana zumunci a kan wani dalili marar tushe?"
"dalili mara tushe fa ki ka ce? in zaku hadu kuna haduwa a gidan mami dan ban yarda ki je gidan wannan mutumin ba kuna haduwa ke da shi har magana ta hada ku sam bazan dauka ba. "
"yah mas ! ban gane ba ae da yah rukky da yah muhd duk jini na ne kuma ba wanda ya isa ya raba mu ko waye "
"hararta yayi ya ja tsaki yay shigewar sa dakin sa."
"zaunawa tayi kawai taji wasu hawaye na bi mata fuska me ya ke nufi? dan ya ci darajar abbana shi ne ze taka ni? ya ce ze raba ni da yan'uwa na to bazan dauka ba wallahi be isa ba wallahi."
"shawar ya sakar ma kan sa dan takaici da bakin ciki ai shi duk abinda zai hada maisha da muhd baya kaunar sa kuma dojewa yake yi saboda yana da kishi gani yake kamar zata kuma birkice masa ta daina masa abinda take masa."
"ranar dai ba a yi zaman lafiya ba tsakanin maisha da mas dan sai fi'ili yake mata da neman magana indai maisha ce ae ga guri nan shi ya fara wasan ita zata kammala shi dan sai fi ta ji a jikin sa in ta dauka da zafi."
YOU ARE READING
SARK'AK'IYAR SOYAYYA!
Romancea love story, this is a love triangle between 4 lover's.