chapter 27

1K 100 3
                                    

💗💗💗💗💗💗💗
SARK'AK'IYAR SOYAYYAH
💗💗💗💗💗💗💗

      Na
FOULANI CERDIYA
     &
KHAIRAT UP

   "27"
A rud'e Maisha ta zaro ido waje tace

      "Yah Muhd Meye haka?".
      
        " Yau na tashi daga Yayan love na koma yah Muhd ko?".
        Fizge hannunta take kokarin yi ya k'ara janyota jikinsa yace
        
         "Maisha ki d'ago ki kalli cikin idanuwa na ki tabbatarmun da zargina".

         Hararanshi tayi ta k'asa.

      " Wani irin zargi kenan, kai da ka manta dani kana shaaninka kodamuwa bakayi ba".

        "Wallahi Maisha Ina sonki har yanzu, Maishana ki tab'a zuciya ta, zakiji yadda take beating, a duk second na numfashi na yana bugawa ne da Sonki Maisha, Meyasa zakimun haka, Yah muhd naki ne fa har abada, wallahi da sonki zan mutu Maisha.......".

Wani tausayinsu ne ya kamata tana d'ago da idonta ta fash'e da kuka mai Shiga rai.

        Tace
" Yah pls leave me...........Ka rabu dani kana ta cewa muyiwa Abba biyayya, amma kana k'ara tunzurani. Kana kara ruruta wutar soyayyarka a zuciya ta, Dan Allah ka rabu dani".

        "Maisha ni kike cewa na rabu dake ni muhd?".

          " Eh kai, kuma ka cikani saboda kada azo wucewa a ganmu".
     
     "Bazan cika ki ba, kuma bazan rabu dake ba, har sai kin bud'e bakin ki kince bakya sona I promise u zan rabu dake".

       Fizge hannu ta tayi ta k'ura mashi ido, taga ya rame kad'an idonsh'i yayi jajur kamar garwash'i, k'irjinsa sai bugawa yake fat-fat.

          Girgixa mashi kai tayi ta Nuna kanta da yatsa tace
           " Bakina bazai taba iya furta kalma Mara dadi akanka ba, yaya zan iya cewa bana sonka..........amma tunda haka kakeso nace Yah Muhd Bana Son ka ci gaba da dasamun kaunarka pls".

        Tana fad'in haka ta tafi da gudu tayi cikin gida.

Kallo yabi bayanta dashi, ji yake kamar yaje ya rungumeta, ko ya saceta su tafi tare.

Sai dai kash ba dama.

D'akinsu ta zarce inda tana zuwa ta baje akan bed ta fara kuka, kukan take hankali, babu maijinta Dan kowa na dakin ya dauka gajiya CE banda Rukyy da tasan ko menene.

Ta kalli inda take ta harareta a ranta tace

"Ki mutu mana kawai".

Wash'egari d'aurin aure kowa yana ta sh'iri masu wanka nayi masu kwalliya ma nayi, su Rukayya sai rawar kai akeyi makeover suka dauko ita da k'awayenta ana ta shashshafesu.
Inda Maisha kuwa tana kwance sai baccinta take sh'a, Imtihal ta tash'eta amma sh'iru kakeji babu alamun Maisha.

Kyaleta tayi, taje ta sh'iga wanka.

Mamy jin d'iyarta shiru yau dasafe bata zo sun gaisa ba, yasa tace bari taje ta duba ta ko shaanin bikinne ya boyeta sai dai tana zuwa tayi turus ganin Maisha kwance.

Tash'inta Mamy tayi amma sh'iru kake ji,
" yarinyar nan gajiya CE bari in bari anjima na tasheta".
    Mamy ta fad'a tana sh'afa kan d'iyartata da kuma tausayin ta, sakamakon tasan ba son wannan auren take yi ba.

Y'an daurin aure har sun tafi d'aurin aure amma Maisha bata farka ba, sai can Mamy ta k'ara dawo Wa, hankalinta ya tashi matuka, ruwa tasamo ta yayyafa mata firgigit ta bud'e ido, sai dai tana bude idonta tafara hawaye.

     Janyota Mamy tayi a jikinta tana goge mata itama Mamyn kamar zatayi kuka Dan tsananin tausayin yadda Maishan ta dawo.

        Hutawa tad'anyi sannan Mamy yasa imtihal ta rikota suka rakata toilet tayi wanka.

Yah Muhd tun daren jiya bai runtsa ba, addua kawai yake kwana yayi yana kai kukan shi gurin ubangiji, inda da safe ya tashi da mataccen jiki.

Abokanshi sunzo sun cika d'akinsh'i amma ko wanka ya gagara yi, dakyar ya iya samu ya sh'irya sai dai fuskar nan ba walwala Dan idanunshi yayi jawur kamar garwashi, abokan shi dai sai tsokanar shi sukeyi.

Bakin tabarau yasaka ya rufe asirin idonshi Dan yasan idan ba haka yayi ba, tabbas kowa sai yagane yana cikin damuwa.

Masha Allah An daura Auren
MUHD IBRAHEEM DA RUKAYYA AUWAL
    Akan sadaki naira dubu 50
Sannan aka d'aura Auren

MO'TASEEM ALKHALI SHAREEF
     DA AMARYARSA
HAUWA'U AUWAL (MAISHA)

  akan sadaki naira dubu Dari da hamsin.

D'aurin aure ne daya Tara mutane,manya manyan Yan kasuwa, da shuwagabanni Anyi d'aurin auren a masallacin dake unguwarsu Masha Allah kowa yanata farinciki, Yah Mas baki har kunne inda Yah muhd ana d'aurwa aka nemesh'i aka rasa sakamakon ciwon kan dayake damunshi.

Maisha ce cikin shadda gezinar peach colour, mai take ta shafawa salo salo kamar bata so, a haka dai har ta gama ta nemi guri ta kwanta, inda su Rukyy sai selfie ake tayi da k'awaye.

Wata tsohuwa CE Yar uwarsu Abba ta shigo dakin tana tsokanar amaren.
    Tace
"Aa kaga Farar mace, Doguwa kin kere mata, Farar Mace alkyabbar Mata Sadakinki da ban Dana sh'aura".

Maisha tunda shigowar matar nan ta mike a zubure tana kallonta.
Ta dafata tace"
   Amarya a gidan Mo'taseem yau dai kin zama amaryar Mo'taseem".

Inda ta kalli Baron da rukyy take tace "Aa amarya a gidan Muhd, ah lallai yau kina cikin farin ciki, kin zama matar muhd an daura aure sai dai fatan Allah ya Baku zaman lpy baki d'aya".

Gaban Maisha ne ya buga tas tas kakeji durum, a take a gurin taji wani jiri yana dibanta ta fara ganin duhu-duhu idonta ya rufe ruf a take ta fad'i ji kake tum ta fad'i k'asa.

Ihu Yan dakin suka sa da gudu imtihal ta sauka kasa tana hak'i tana fad'in

" Mamy Maisha, ta fad'i Mamy".
       Karaf a kunnensa baisan sanda yayi saman ba sa saurinsa yana zuwa ya sh'iga jijjigata, ganin bata farfado ba yasa ya d'auketa cak yayi kasa da ita da gudu.

  votes watt pad khairi _muhd

No comments No typing😌

#Sarkakiyarsoyayya

  SARK'AK'IYAR SOYAYYA!Where stories live. Discover now