chapter 7

1.4K 109 0
                                    

💗💗💗💗💗💗💗
SARK'AK'IYAR SOYAYYA
💗💗💗💗💗💗💗

Written by: FOULANI CERDIYA
       &
KHAIRAT UP

wattpad Khairi Muhd

       "7"

      "Ga Yah Nass! ga Yah Nass"!.
       Maisha ke tsallen murnar ganin yayan nata da ya dawo daga tafiyar dayi a wajaen aikinsune aka tura shi wani course.
       " Keh?, Kama kanki meye haka, kinwani cikamana kunne da ihu......".
     "Aa....Muhammad kyaleta taga big bro dintane ko Maisha Abba".
     Yah Naseer ya fada yana shafa kanta.

    Turo baki tayi tace" Ai Yah Nass zan gaya maka wani abu Amman fa sai bakowa saboda......."
           Taki karashe maganar sakamakon Yah Muh daya harareta.

    Cikin gida suka nufa aka baje a dining sakamakon liyafar da suka hadawa babban yayan nasu sakamokon sa mashi rana da akayi bikinsa saura wata biyu.

       "Yaya ni zanyi serving Ku".

    Maisha ta ce.
   " ke dallah ki zauna ayi serving mu kece zaki serving din namu Dan rain in hankali."

    " barta mana ni CE nan zanyi".
   Rukayya tai maganar tana wani hade rai.
   "Eh Saraki ".

        Kallonshi Yah Nasser yayi yai dariya yace" Aa fa Muhammad wallahi kanaiwa Maisha haka, zaka hadu da Abba".
       "To na nawa kuma kaima kasani ai Abba baya kyale kowa a gidannan har Mamy ma".

      yah muh ya fada yana harararta.

      Mamy CE ta fito da faraa tace " bari ni nayis serving dinku kada abun yazama rigima kunsan Halinta".

     Kowa ya fara cin abincinsa cike da nishadi banda Maisha datake ta tsokane tsokane da jagolgolo.

   Yah Muh ne ya kalleta yace" Ke Eat Ur Food ko ki tashi ki barnan".
     Mamy tai murmushi tace"Ta tsare mutane ba, Allah yaso ai Me daure miki bayan baya nan".

         Hararar Yah Muh tai ta k'asa, sai kuma ta d'ago ta kalleshi ta tuntsire da dariyah tace" Hahhhahhahhhhhh, tab Dan Allah Ku kalli Yah Muh yadda yake ta zuba loma spoon baka spoon kwarya".

     Kowa shi ya kalla aikuwa duka suka tuntsire da dariya, sakamokon sudai basuga abinda yake na hannu baka hannu kwarya ba, amma saboda shakiyancin Maisha ta tsokano shi.

Aikuwa ya cika yayi fam sakamokon dariyan da suke more especially Maisha da saboda iskanci harda rik'e cikin ta tana nunashi tana dariya.

   Beyi wata- wata ba ya mik'e da sauri ya nufeta.
   Aikuwa ta cilla da gudu sai bayan Ameenuh dake shigo Wa palorn a lokacin.

       Tana nish'i tace"Yah Ameen pls save me".

      Rik'eta Ameenuh yayi ya kalli Yah Muh daya had'e mugun rai yace"Yah pls bazata k'arab....."
      "Dallah Matsa in Bahaka ba yanzu ranka ya b'aci".

    Ameenuh bayasan a tab'a Maisha sedan bayadda zaiyi ne yasa ya tura masa ita, Dan shima yana gudin a maresh'i.

    Ja da baya ta farayi ta fara rau -rau da idanu" Dan Allah Baba Yah Muh kayi hak'uri bazan k'araba". Tai maganar tana had'e hannayenta biyu alamun begging.

   Sh'i dariya ma taso bashi watan yau Baba ma ya zama saboda gudun duka.

     "Ai Maisha wallahi tunda baki jin magana yau ko Kaka zakicemun sena farfasa miki jikinki kuma nasan hukuncin da zan miki zo nan".

       Ya Nuna mata Kusa dashi.

A hankali ta dinga takawa tana hawaye tan tafiya tana ja baya kuma.
Ganin zata b'ata mashi time yasa ya janyota yace" Oya Frog Jump".
    Ya jata yayi farfajiyar gidan da ita, aikuwa ganin haka Rukayya ta bisu Dan tayi kallo.

        "Sau goma zaki zagaye gidannan",
         " ke kuma mikon chair".
      Ya cewa Saraki aikam miko masa tayi da rawar jiki.

Ya karba ya zauna ya had'e rai (Nikam FOULANI nace da KHAIRAT kinga Yayah ba Imani kenan).

           Ta fara tsallan kwadon tana ta kuka ,duk kaiwa sai Maisha ta bashi hakuri amma ko kallonta beyi ba, Rukayya kam dariyama take tayi mata.

   Tana ta frog jump aikuwa kafarta ta gurde take ta saki k'arar da su Mamy da Yah Nasser duka saida suka fito.

     

Hope u re enjoying it?,Pls We Need More Of Ur Comments.
    We luv u all our follower's.

  SARK'AK'IYAR SOYAYYA!Where stories live. Discover now