chapter 13

1.3K 94 2
                                    

💗💗💗💗💗💗💗
SARK'AK'IYAR SOYAYYAH
💗💗💗💗💗💗💗

By; FOULANI CERDIYA
&
KHAIRAT UP

WATTPAD@ KHAIRI-MUHD

"13"

"Ke wai se yaushe zaki girma ne,"?
" Wallahi nima har sai na fara wadanc........".
Kan ta karasa maganar ya galla mata harara aikuwa ta k'ara man kukan nata, Abba da ko rufe motar baiyi ba kawai ya nufosu.

Tashi tayi da gudu tun kafin ya karaso taje ta rungumeshi tana kuka, dago da ida yayi yace"Uwata me akayi miki ne".

Tana kukan tasoma bashi labari"Wallahi Abba Malam Ali ne, dama ya tsaneni yayi ta dukana haka kurum, shi ne yau da naje tunfa daya da rabi naje......,".

"Lah kai Maisha ki fadi gaskiya,".
Rukayya ta fada tana katse mata xancen.

Harararta tayi, Abba ya kalli Rukayya yace" Ke kinga kina k'aryatamun uwa zan fa zaneki a gidan nan, cigaba inajinki Maisha na".
Yafada yana kallon Maisha.

Aikuwa ta hadiyi yahu ta cigaba"Toh yaufa Abba tun da wuri naje, yasani sharar filin makaranta, sannan yasani wanke bandakunan nan duka, kuma shi ne Dana gama ya Riga dukana yana ball dani harsai da su Ya sayyadi Babba suka masa magana hihihh".
Ta karashe maganar tana rusa kuka irin an cucekan nan.

"Tab sannu Maisha".
Yah Muhd ya fada saboda tsabar mamakin sharrin data xauna ta shirgawa malami.

A fusace Abba yaja hannunta, beyi wata-wata ba ya shige motor ya figeta da gudu.

" yau malami ya Shiga uku, a gun Abba ".

Rukayya ta fada tana tagumi
Murtuke fuska Yah Muhd yayi, yace" makara tayi nasan ba wani Abu ba, Maisha bataji yarinyar nan, yanzu haka zaa barta tana cin karanta babu babbaka"?.

"Muhd meye ne ya faru najiyo hayaniyar yara da kukan Maisha, suna ina? Ina Abban naku?".

Mamy da ta fito yanzu take tambayar Yah Muhd.

" Hmmmm, kema kinsani ai Mamy, Maisha CE ta makara malaminsu ya daketa,shi ne take ta wannan kukan, wallahi ni abun haushin ma da Abba ya dawo nasan sai abinda yau mukaji kuma".

Dora hannu Mamy tayi akai tace"kai kai ni Maisha me takeso mu zama ne?,".

Rukayya CE tace"kuma wlh Mamy abinda ta fadawa Abba ba haka bane cetaifa Wai sharar filin makarantar yasakata ita kadai, kuma abinda ko zaa share ma wasu ne suke yi fa baasa yara sai manya manya wadanda suka wuce duka".


Muhd Mamy ta kalla tace" amma kai kuwa meyasa bakayi mishi magana ba".

"Wallahi Mamy niyyar binsu ma nayi, to ganin yadda ran abban ya baci yasa nai gum da baki na".


A makaranta kuwa Abba yana zuwa yai parking, yace inane office din Headmaster, aka Nuna masa yana shiga kuwa ya tadda malamai da yawa a ciki a zazzaune da alamar meeting suke.

Sallama Abba yayi ya mike musu hannu sukai musabiha.

Headmaster Ya kalleshi yace" Alhaji Allah yasa dai lafiya naganka kamar da daliban makarantar nan kuma an tashi wani Abune ya faru".

"Eh gatanan wani malaminsu ya kamata yayi ta duka ........".
Ya kwashe duk abinda Maisha ta fada masa ya gaya musu, kuma ya kare da cewar" Ina malamin yake ni shi nake nema, Dan sai na ramawa y'ata dukan da yayi mata akanme ko an gayamasa jaka CE ita ".

Toh fa headmaster da sauran malamai suka bishi da kallon mamaki, ganin yadda ya fututtuke yana masifa.

Headmaster ne yayi kokarin cewa" Aa Alhaji baayi haka ba, ka zauna a samu a sulhunta, kuma ma bata fadi Wanda yayi mata hakan ba ai, duk da mu a saninmu gaskiya bama masa ka yara kamar ta irin wannan aikin".

"Ke wane malami ne?".

Murgud'a baki tayi tace" malam Ali ne".

Kallonta sosai malam Ali yayi danshi yama manta fuskarta, sai da yayi tunani ya tunota.

"Alhaji in rantse maka zaka yadda, wallahi baasata wadannan ayyukan ba, nasan dai na mata bulala".

" au Kaine ka daketa kenan?, to bazan yadda ba kuwa, ka fito nan in ramamata dukanta".

Hakuri suka Shiga bashi dukansu amma ya fitittike sai ya daki malam Ali.

Ana cikin hakane Director din makarantar yazo yana Shiga office yaga Alhaji Auwal, Ashe ya sanshi.

"Aa Alhaji yau Kaine a makarantar tamu?".

" Au Ustax Musa ni ne zuwa nai akan yarinyata".

"Meya faru".

Nan ya bashi labari aikuwa yayi ta bashi hakuri yace kada ya damu zaima kori malam Alin kawai.
Shi kuma Abba yace" Aa kada ya koreshi ya barshi, amma da sharadin kada a sake dukar mai ya.

Suka taho suka dawo gida.

Parking mota kawai Abba yayi ya wuce ciki, su Rukayya dajin dawo war Abba aka fito.
Harararta yayi aikuwa sum sum ta wuce ciki.

Bayan sati daya

"Saraki Saraki".
Yah muhd yake kwalla mata kira da wani bag a hannunshi mai kyau.
Fitowa tayi tace" Yah Muhd gani".

Me cemata k'ala ba ya mik'a mata bag din yace"this is for u".

Karb'a tayi ta bud'e, kayan kwalliya ne a ciki, da dogwayen riguna kala uku da wani uban takalmi mai tsini.

Murna ta Shiga yi sosai.

Maisha ta fito da littafi a hannunta ta kalli Rukayya tace"Lah yah Rukayya nagani naki ne?".

"Eh Yah muhd ne ya sayomun".
Amsatai itama tana murna sai kuma ta d'ago tace" Yah ni INA nawa bag din?".

Harararta yayi yace"Wa? Ni Muhd insa kud'ina in sai miki Abu? Allah ya kiyaye, dallah tafi kibaiwa mutane wuri shashasha".

Ajiye bag din tayi ta tafi dakin Mamy jikinta a sanyaye.

Kan cinyar Mamy ta zauna tare da share kwalla tace"Mamy waini meyasa Yah muhd baya sona ne?, ni menayi masa sai yayi ta hantara na".

Kallonta Mamy tayi da kulawa tace"Aa yana sonki mana meye yayi miki yayan naki? ".

" Yah Rukayya ya bawa gift ni nace INA nawa yace Allah ya kiyaye ya sai mun Abu da kudinshi".

Sosai Mamy taji ba dadi, ganin yadda yake Nuna banbanci da Rukayya amma sai tace da ita"Aa. Maisha kema yana sonki kurum rashin jinki ne bayaso, sannan ki nutsu ki dena tsokana, in kikai haka zaku iya shiryawa dashi ".

Rausayar dakai tayi tace" Shikenan, amma ni da Abbana zan fad'awa nima ya sayomun tunda shi yana sona ".

Dariya Mamy tayi tace" kinga kina fadawa abbanku sai Ku kara yin fada da yayan naki kada ki fada Wa kowa kinji Maisha na".

Sauka Mamy tayi ta barta a can tana fitowa ta hango Yah muhd zaune shi da Rukayya suna hira, hard a murmushi "Aa Muhd anya kuwa".

Mamy ta fada da faraarta.

Juyowa yayi shima yace" Mamy menene"?.
"Anya ba y'ar gida zaayi ba kaida Rukayya".

" Ah .....haba Mamy ni kanwatace Rukayya ko Rukayya? ".

Ya fada yana kallon fuskarta.

  SARK'AK'IYAR SOYAYYA!Where stories live. Discover now