chapter 43

983 82 0
                                    

💗💗💗💗💗💗💗💗
SARK'AK'IYAR SOYAYYAH
💗💗💗💗💗💗💗💗

NA
FOULANI CERDIYA
&
KHAIRAT UP

"43"

"Ai bawani Abu bane alamun cikine kurum kada ki damu".
Da haka suka yanke firar.

Toh kwanaki na tafiya, rana na wuce satittuka sun shude watanni ma haka.

A yanzu cikin Rukyy watanshi 9 cif inda har date din haihuwa ta ya kama sai dai fatan Allah ya sauketa lafiya.

Maisha ita kuma cikinta watansa biyu da sati uku.

Yah Rukyy CE kwance kan cinyar Yah Muhd ta d'ago ta kalleshi tace
" Yah na kasan me?".
"Aa sai kin fad'a".

" yanzu kafana a gida biyu take ko duniya ko lahira, ko"?.

"Haka ne".

" Kasan me so nake naje gidan Mamy da gidan Sisto saboda suyimun addua".


"Kai saraki bakya jin magana yanzu da wannan tirtsetsen cikin zakije gidan mutane?".

Shagwabe fuska tayi
" Haba yayana yanzu meye na gidan mutane sisto fa nace".

"Naji kirata a waya kuyi zumuncin amma basai kinje ba".

Rukyy kenan sarkin biyayya bata karayi masa musuba ta d'aga waya ta kira Maisha.

Bayan kwana uku.

" Sweetheart! Help me wayyo bayana".

Rukyy keta tashin Yah muhd da yake bacci.

Jin tana cewa cikinta bayanta yasa ya farka da sauri ya rikota sai gumi take duk kuwa da sanyin da ake sh'ek'awa.

Goge mata gush'i yake yana mata sannu dakyar yadaga waya ya kira mamy da Umma cikin darennan suka fita asibiti.

Wahala kam Rukyy tash'a ta, Dan sai da ta kwana tana Abu d'aya duk ta fita hayyacinta, gashi Dr since ayi mata cs Yah Muhd yaki yadda.

A haka dai Allah ya taimaka ta haihu ta haifi d'anta namiji santalele Mai kama da ita sak sedai hasken babansh'i ne das'hi.

Maisha na kwance akan cinyar Yah Mas wayar ta tayi kara ake sanar mata haihuwar, ai tuni ta tash'i ta hau shiri sai asibiti.

Suna zuwa tace sai anbarta taje taga sisto dinta da babynta.


Maisha na sh'iga d'akin ta hango ta kwance tayi haske sosai.

D'an Maisha ta d'auka tana murna tare dayi masa addua

"Sunnu Yah Rukyy babyn nan kamarku d'aya amma fari na yayi".
" wallahi inasonka babyna". Maisha tayi masa Peck a goshi.

Dakyar Yah Rukyy ta iya yin dariya wacce kana gani kasan yakece.
Ta rik'e hannun Maisha tace
" Ai danki ne Maisha, ki rainesh'i na barmiki".

Dariya Maisha tayi tace
"Kinji wai kin barmun da gaske kike? Aikuwa nagde".

Ana haka Yah Muhd ya sh'igo shima ya amsh'i babyn yayi masa addua sannan yayi masa khuduba.

Sai da sukayi kwana biyu sannan aka sallamesu.

Kowa murna yake yi, ranar suna akash'a budiri sakamakon yaron ansaka masa sunan Mahaifin su rukky wato Muhd Auwal, Wanda a take Maisha ta lak'aba masa Little Papa.

Soyayya suke nunwa yaron sosai, kowa yayiwa little kaya bana ba kayaba, yaro yayi goshi g farin jini.

Bayan suna

Maisha na zaune tana kallon hoton little Papa da yayi wayo sosai bazaki tab'a cewa sh'ine jaririn da ko wata biyu baiyi ba.

Wayar tace tayi ringing ta d'aga ganin Yah Mas ne,
" Baby kina gida".
"Eh mn INA zani kaima dai in banda abinka?_"

" Yawwa dama canai ki sh'irya, ki rakani unguwaa yanzu kafin na iso".

"To"
Kawai tace ta datse kiran.

Baafi 10mnt ba sai gashi ya sh'igo.

Ganinsa tayi wani irin ta nemi guri ta zauna tana tambayar sa
"Lafiya naganka haka Mijina?".

" Hmmmmm wlh Hajiya dan dai mahaifiyata CE amma da........"

Saurin tosh'e masa baki tayi tace
"Uhm uhm karka fad'i koma meye mahaifiyace gurinmu dole mu bita........."

Wayar tace ta sake ringing ta duba taga sunan Ummah ne yake yaho, haka kurum Maisha taji gabanta ya fad'i da kiran amma ta dake ta dafe kirjinta.

"Ehe? INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIRRAJIUN WAYYO YAH TA".

Tuni cikinta ya kulle mararta ta rike a take Maisha ta fad'i kasa tummmmm ba numfashi inda tuni jini ya fara bin k'afarta.

Wayar tata data wullar yah mas ya dauka yabi number din data k'arasa,ai shima baa gama fad'i masa maganar ba ya ajiye wayar yana salati.

  SARK'AK'IYAR SOYAYYA!Where stories live. Discover now