chapter 47

973 78 1
                                    

💗💗💗💗💗💗
Sark'akiyar soyayya
    ❤❤❤❤❤❤

na fulani cerdiya
       &
khairat up

  
F.O.W

            " 47"

"mami ta cafke ta ce alhaji ae kawai ni ina ganin a bar maganar nan haka dan kuwa yarinyar nan bata ganin girman mutane da ma shi kan shi mijin nata kuma saboda Allah ya zata dauko dan wani ace da na ya raina kuma dan ma na tsohon saurayin ta."

"baffa kawai ji yay ransa ya baci ya ja ajiyar zuciya ya ce kai mas magana tana hannun ka ina jin ka yanzu fada mun zaka maida matar ka ko kuwa a hakura?"

"baffa...ni ban da matsala da ita,matsalata daya ce wannan yaron idan tana so mu koma tare ta maida wa muhammad dan sa,matukar bazata yarda ta ajiye sa ba ni kuma bazan yarda ta koma ba na hakura."

"karaf maisha ta ce ni kuma wallahi bazan rabu da wannan dan marayan nawa ba dan yar'uwa ta. nima na hakura da kai koda kuwa kai ne autan maza bazan kuma gidan ka ba."

"umma ta ce ae maisha kin mun dai dai nagode _ZUMUNTAR KENNAN_ yaje ya zauna da me ganin girman manya da me kin zumunci.in banda rashin imani ma me a wannan dan wanda be san komai ba? an dai ji kunya kuje maisha ta bar ku har abada."

"eh muma dama mun fi san haka Allah raka taki gona mama ta fada ta ce kai kuma tashi mu tafi."

"haka ya mike ya ajiye musu takarda wanda ya riga dama ya rubuta mata shi."

"mami dai bata ce komai ba sai hawaye da ta dinga zubda wa na rashin miji da ya bnda haka wa ya isa ya ma maisha haka? "

"ke kuma kina ji na ? zumuncin da ki ka rike Allah ya saka miki da alheri, kar ki damu kan ki ae ba kan ki farau ba kuma ba kan ki karau ba,yaje shi ne yay asara kuma ze danasini nam gaba."

"bayan ta shiga ciki ne ,umma ta ce a karo na biyu ina neman alfarma yay"
"ta me maryama?"

"idan ta gama idda a maida auran ta kan muhammad ko dan kaunar juna da suke da kuma wannan jaririn da maisha ta ke kauna kamar ranta."

"mami ta ce nima nayi wannan tunanin a taimaka a tausaya musu,da farko sun yi biyayya suka hakura da juna wannan karan a yarda a hada auran su."

"baffan ya ce shi kennan Allah ya nuna mana ya kade fitina,ya kuma basu hakuri da juna."

"amin, amin!"

"nan kowa ya watse daga falom baffa ya koma gida umma ma haka."

"maisha banda kuka ba bu abinda take yi na bakin cikin abunda mas ya mata da mahaifiyar sa wai bata daraja su? banda ma abun yah mas me little dina ya sani? wata zuciyar ta ce kayi wa kan ka."

   MANAGE

  SARK'AK'IYAR SOYAYYA!Where stories live. Discover now