SARK'AK'IYAR SOYAYYAH
NA
FOULANI CERDIYA
&
KHAIRAT UP"56,57"
"Dan Allah kada na k'ara jin Kalmar so a gareni indai bata yan uwantaka ba, dame zanji?".
" Maisha ki tausayan pls kinsan irin son da na jima INA miki kuwa? Wallahi tun kafin kiyi auren farko nake sonki,Dan dai lokacin INA bautar kasa na ne kuma ban samu aikin da zance zan tunkari aure ba, amma yanzu kinga INA da aiki Maisha zan iya rikeki na kula dake pls don't say no pls".
Yah Ameenuh ya fad'a yana begging da hannu biyu.
Kuka Maisha ta fash'e da shi a ranta fad'i take inama bata zo duniya ba, Yah Muhd ya gama nasa sannan yanzu shima yah Ameen yazo mata da wata magana to duk cikinsu babu wanda zata aure ehe.
"Maisha say something pls Maisha Pretty na pls u re my heart desire, I didn’t choose you, My heart did ki tausayan ko na samu sassauchi a zuciya ta".
Cikin kuka ta CE
" wallahi Yah Ameenuh bazan iya sonka ba, ka dena gayamun wadannan maganganun saboda kamar saukar ruwan dalma ne a zuciya ta why sai ni zuciyarka zata zaba? Ga yan mata nan da yawa, why sai ni? Ka rabu dani Yah Ameenuh".Tana gama fad'in haka ta mik'e fuuu tana kuka tayi stair da gudu.
Cin karo tayi da mutum aikuwa tuni ta fad'a jikinta ta saki kuka mai cin rai.
Mamy ta d'agota tana girgixa mata kai da fadin
"Daughter meye ya faru kinsan bansan ganinki cikin damuwa da b'acin rai pls ki dena wannan kukan haka is ok,indai akan Muhd ne abar maganar banson a takura maki".
" Mamy Yah Ameenuh ne,".
"Me yayi miki? Keda mutuminki Maisha?".
" wai ni Yah Ameenuh ya keso Mamy wai menayi musu?".
Ta fad'a tana rushewa da kuka.
Yah Ameen daya biyota ya k'araso gun Mamy yayi k'asa da kansh'i yace
"Mamy a matsayin uwa na daukeki, saboda kimun rikon da babu Wanda zai minshi bayan mahaifiyata, Mamy wallahi inason Maisha, Mamy kintuna? Randa aka haifi Maisha kikace kinmun mata?".
Kallonshi Mamy tayi da sauri ita da Maisha tuni Mamy ta sh'iga tuno maganar.
Sati daya da aka haifi Maisha Yah Ameenuh ya shigo lkcn shima baifi shekara 7 ba.
Yah Muhd na zaune
Mamy ta miko mashi ita ta Dora mashi akan cinyarsa tace
"Muhd rik'e kanwar nan taka INA zuwa,?""Kai Mamy kinsan ta da kuka yanzun nan zata ishemu da kuka".
Yah Muhd ya fada yana mikewa tsaye.Yah Ameenuh yace
" Mamy a bani ita na rik'e miki ni INA sonta ko zatayi kuka".
" Yawwa ameenullaah ai dama matarka CE gatanan rik'e kayarka na baka ita".
Dungure mashi kai Yah Muhd yayi yace
"Banza sarkin had'in fad'a, ai nima ba cewa nayi bana sonta ba kawai kukanta ne banso".Mamy tayi ajiyar zuciya tana jinjina maganar Ameenuh ya akayi har tsahon wannan lokacin Ameenuh bai manta ba? Gaskiya ne rubutu akan dutse baya gogewa.
" Ameenuh ga Maisha nan indai ta yadda dakai na baka ita".
Mamy ta fad'i tana sauka ta barsu a gurin, karo taci da mutum yana tsaye ya had'e rai ya jingina da karfe yana saurarar duk abinda suke cewa.
Kallon Mamy yayi yayi saurin d'auke Kansa haka itama Mamy din, domin Muhd yana bata tausayin daga shi har Maishan.
Kala bata cemasa ba ta wuce shima bayanta yabi ya wuce k'asa.
Domin yaji duk abinda suke fad'i.D'akin sa ya wuce wani tuk'uk'i! Yake ji a zuciyarsa k'aninsa shi ne yake Neman zame masa shinge tsakanin sa da Maisha dole yasan abunyi.
Hotunanta ya baje akan gadon sa wasu tun tana rarrafe wasu ta fara tafiya gasunan dai kala kala kowannensu ka gani da faraarta dama Maisha sarkin dariya CE.
Wayarsa ya dauko ya kira number din Maisha amma bata d'aga ba, yayi kiran yakai sau goma amma bata d'aga ba tashi yayi a fusace yayi d'akin ta yana zuwa ya tadda ta ita da Ameenuh zaune kowannensu yayi jugum jugum.
"Fita ka bani guri".
Yah Muhd ya fad'a cikin wata iriyar murya mai zafi.
Kallonshi Ameenuh yayi yayi murmushi ya mik'e ya fice daga d'akin.
*Hahhhhhh toh Fans ga Ameenuh ga Muhd fa wane ne zai ciri tutar zabi ya rage gareku Wanda comments yafi yawa Kansa shine jarumin Maisha toh a fafata*
YOU ARE READING
SARK'AK'IYAR SOYAYYA!
Romancea love story, this is a love triangle between 4 lover's.