SARK'AK'IYAR SOYAYYAH
NA
FOULANI CERDIYA
&
KHAIRAT UP"52"
"Maisha what are u doing here?".
Ya fad'a ransa a murtuke ai tuni Maisha ta mik'e ta fara rawar jiki Dan bata manta wanene Yah muhd ba.
Kara jefo mata wata tambayar yayi da cewa
" Bakyaji na who is this guy?"."Uhm..........uhmmmm saurayin.........Uhmmm wannan".
" Yi mun sh'iru".
Ya fad'a yana Jan hannunta sai inda yayi parking mota yana zuwa ya cillata ciki, ya koma yazauna mazaunin driver.In banda tafasa da zuciyarshi take ba abinda takeyi a haka ya samu ya k'arasa har gida yana zuwa bai gama parking ba Maisha ta kama handle zata bude ya fusgota aikuwa a take ta fad'a jikinsa gaba d'aya.
Wani kasala da gajiya ta saukar musu gaba dayansu, sakamakon wani magnet daya jasu.
D'agowa tayi ta kalleshi still tana kwance a jikinsa.
Lumshe idonsa yayi, ya kalleta tare da janye jikinta daga nasa.
"Kada in k'ara ganin k'afarki a waajen gidannan with out my permission kinji ko".
Ya fad'a muryarsa a matukar kasalance.
Budewa tayi itama ta fito, hankalinta duk baya jikinta sakamakon wani tabo da taji ya fash'e a zuciyarta.
A cikin gida kuwa bata bi takan kowaba,Dan Mamy ma tana tambayar ta ya taga ta dawo yanzu kawai ta gyada mata kai ta wuce.
Little ta tarar a dakin sai baccinsa yakeyi, murmushi tayi ta nufi toilet tayi wanka ta dauro alwala, sallah tayi da ake binta dayake ana ta rabo basuyi sallah ba.
Idarwanta kenan ya sh'igo d'akin ya nemi guri ya zauna sai da ta idar sannan ta kalleshi tayi murmushi tace
" Yah Ameenuh ya akayi ne?".Lumshe ido yayi yace
"Wallahi yunwa nakeji kuma naga Mamy girkin ba yanzu zaa gama ba, ko zaki Dan tafan indomie pls"." kai Yah Ameenuh wannan ne matsalarka? Ai kasan ba abinda zai hanani dafa maka".
"Yawwa tawan luv u sosai".
Yah Ameenuh ya fad'a yana murmushi ya fita daga d'akin.
Abakin k'ofa yaci karo da Yah Muhd, wani kallo ya watsa masa sannan ya wuce shi yabar gun, Yah ameen kuwa tambayar Kansa yake to me yayi masa?,.
Sai da Maisha ta gama girkin ta nufi d'akin Yah Ameenuh sanye take da dogon skirt irin me robar nan sai rigarta wacce tadan matseta sosai ta gyara gashnta tayi kyau sosai.
Kwankwasawa tayi ya bata umarnin sh'iga.
" Ga abincinka nan na gama Yah Ameenuh ".
" wow thanks you my pretty girl,kinga yadda kikayi wani kyau kuwa kamar a gidan Mas".
Kallonsa Maisha tayi ta Dan hararesh'i ta buga kafa tace cikin shagwaba
"Kai Yah Ameenuh meye haka wallahi ni munyi fada ma ba ruwa na dakai".
Tayi hanyar kofa tana niyyar fita yayi saurin tare ta, hannunta ya rik'e ya fara magiyar bada hakuri yana lallash'i, Maisha kuwa sai shagwabarta take harda kwallarta,
Hannunsa yasaka ya share Mata tare da wure mata idon.
Dai dai nan Yah muhd ya shigo dakin kawai sai ji yayi numfashinsa yana Neman daukewa.
Aransa fad'i yake wannan yarinyar meye yake damunta? Ko Dan ta saba da jikin namiji, shiyasa yanzu ma take wannan abun, dazu ya ganta da wani yanzu kuma gata da ameenuh da wata irin sh'iga wacce ta bata masa rai.
Kishinsa tuni ya motsa ya daka Wa Ameenuh tsawa.
" meye hakan? Ameenuh?".
"Laifi nayi Mata ne Yah".
Ameenuh ya fada yana zare hannun Maisha daga nasa.
Kwafa kawai yaja fice fuuuu
" ke kuma kizo inason ganinki".
Hantar Maisha ta kad'a saboda tsoron halin yayan nata, amma haka ta daure tayi hanyar dakin sa
A zaune ta taddashi ya had'a kai da gwiwa tana shigowa ya fara surfa mata masifa"Ke rashin aure haukane? Baki da aji ko? Meyasa kike kokarin sanjawa ne Maisha?, wallahi kinji na gaya miki na kara ganin ki a haka ko, tashi mike tsaye"
Maisha ta mike tana Jan rigarta.
"Dubi wani sh'iga, idan na karaa ganinki a cikin gidannan ba hijab ko wallahi sai ranki ya b'aci kuma meye na wani sh'iga dakin Ameenuh?"..
Ikon Allah itamafa yayanta ne kamar kai, kinji su muhd kishi ya rufe ido.
Kuyi hkr da rashin typing wlh ni bani da lafiya khairat kuma she's busy yanzu, kuna mana uzuri pls.
we are really sorry for the dely!
YOU ARE READING
SARK'AK'IYAR SOYAYYA!
Romancea love story, this is a love triangle between 4 lover's.