💗💗💗💗💗💗💗💗
SARK'AK'IYAR SOYAYYAH
💗💗💗💗💗💗💗💗Na
FOULANI CERDIYA
&
KHAIRAT UP"28"
Mamy ta fito hankalinta a tashe tace
"Muhd meya samu Maisha".
Bai tsaya bata amsa ba kawai yayi waje da ita yana kwalawa mai Gadi kira da gudu yaje ya fito da mota.
Yana shirin sakata ciki sai ga su Mo'taseem da abokanshi, Hankalinsa yayi matuk'ar tashi yayo gurunsu, ai Yah Muhd yana ganin ya doso gunsu yayi sauri ya sakata a cikin motar.Gaba ya koma yana kokarin tayar da motar Yah Mas ya dakatar da cewa
" Meye ya samu Matata?".
Wani bakin cikine ya tokare Yah Muhd, baisan lokacin da ya Wa tsawa Yah Mas wata harara ba ya tada motar ya fice.Mamy ta kira Abba, yazo suka tafi gaba dayansu, a hanya Abba yadauki wayarshi ya kira Yah muhd.
Bugu daya ana biyu ya dauka, Abba yace
"Muhd kuna inane, wani asibitin kuka tafi?".Daga dayan bangaren Yah Muhd ya bash'i amsa da
" Muna Jiddah Hospital, Gamu ma mun k'ara so".
Katse kiran yayi ya kash'e Motar ya kira wani abokinshi dayake aiki a asibitin, yana ganin kiran Muhd ya d'aga, yayi masa bayani yace gashinan zuwa.Baa jima ba Dr Nura yazo yasa aka Shiga da ita ciki, Gado aka bata kafin daga bisani aka fara mata Yan gwaje gwaje.
Kofar d'akin da Maisha take Yah Muhd ya zauna ya rafka uban tagumi, zuciyarshi sai bugawa takeyi, yana kokonton inya rasa maisha a rayuwarsa anya zai iya rayuwa?.
Yana cikin tunanin wayar Abba ta k'ara sh'igowa, Kwatancen inda yake yayi masa yace " to gasunan".
A tare suka taho Yah Mas,Mamy, Umma, Abba, Ameenu dukansu kana ganin su zaka ga tsantsar damuwa a fuskar sa.
Dukkansu Neman guri sukayi suka zauna Abba yace da Yah muhd
"Tana INA?"." Tana ciki, Dr din suna kanta ba matsala".
Duk suna zazzaune kowannensu da abinda yake sak'awa a ransh'i.Sai bayan wasu hours sannan Dr Nura ya fito ya samu su Abba yace yanason magana dasu.
Ai gaba dayansu suka bisa Yah Mas shi ne a gaba zuciyarshi bugawa kawai takeyi.
Dr Nura ne ya kallesu yace
"Abba Ku jiramu bari naiwa muhd bayani".Yah Mas ne ya kalli Dr din yace
" Nima ina da bukatar jin bayanin coz i'm her husband".
Murmushi Dr Nura yayi yace
"No bad........".Dr Nura ne ya kalli Yah Muhd yace
" Muhd waini wannan yarinyar ba ita CE kanwarnan taka mai tsiwa ba"."Eh, itace".
" Ayyah amma nayi mamakin yadda akai har ta kamu da hawan jini, gashi matsalar tana ta girma amma Baku fuskarta ba".
" Maisha da hawan jini ya salam, Yanzu dai ta farfad'o ne ko kuwa".
"Eh to mundai sa mata oxygen kasan tana da matsalar numfashi so dole yanzu sai munbari nunfashinta ya dai-daita, amma gaskiya a kula da ita sosai, a guji duk abinda zai sata bakin ciki da Wanda zai tsoratar da ita, sannan a dinga debe mata kewa sbd condition din datake tana bukatar Kulawa sosai."Wani bakin ciki ne ya turnuk'e Yah mas ,watakan Maisha saboda kinshi ne har jininta ya hau, duk saboda son wannan Muhd dinne.
Kallon b'arin da Yah Muhd yake yayi yaja tsaki, Yah Muhd Dr nura duk sai da suka Bish'i da kallo, wani irin tsanar Yah Muhd yakeji a ransa. Ko fuskar shi baya son gani kishi ya rufe mashi ido sosai, ya fice daga office din Fuuuuu.
Yah Muhd ma fitowa yayi, yayiwa su Mamy da Abba bayani, Suma zuciyoyinsu duk sun tsinke.
Abba wani tunani ne ya fad'o mashi a rai, kardai Maishansa akan wannan auren ne ta saka damuwa a ranta?, karfa yaje ya jaho mutuwar y'arsa da kansh'i, dole ne yasan abunyi Dan ganin ta cikin farin ciki.
Yah Muhd ne ya tafi pharmacy don sayo magungunan da Dr ya rubutawa Maisha.
Yana zuwa ya mik'a takardar aka bashi bill ya biya aka bashi receipt sannan ya zagaya gun amsar maganin, takardar da receipt din ya basu suka sh'iga dauko mashi.
Wayarsa dake cikin aljihunsa tayi ringing Ya Ciro ya duba kan screen din wani tsaki ya ja tare da katse kiran.
Tana katsewa kuwa wata ta k'ara shigowa ya kashe,sai da aka kira sau biyar yana kashewa, ana shidan ne ya d'aga ba tare da jiran me mai kiran nashi zai CE dashi ba ya hau fad'ar
"To Witch ya akayi, wallahi ki fita a idona".
Rukayya dajin sunan da Yah Muhd ya kirata yasa ta kwalla amma sai tace dashi
" Dan Allah Yayana kana INA? Ni da k'awayena gamu sai jiranku muke kuzo muyi hotunannn..............".
"Ke, dawa kike irin wannan maganar, kin rainani ko, akan wannan yasa kike ta kirana?".
"Eh mna"." To bazaa zo ba, kuma wlh kinsan dai banson unnecessary call ko? To kish'iga taitayinki very stupid girl ".
Ya katse kiran yana huci kamar Rukayyan na gaban shi.
Magungunan ya amsa ya koma gun Dr din ya dudduba ya bash'i.
After 3 hours
Maisha ta farka, wata nurse ta shigo ta sameta, sannu tayi mata ta d'auko allurar da zatayi mata.Nurse din CE ta fito take sanar dasu suje ta farka.
Ai kamar jira suke Yah Mas Yah Muhd duk sukayi ciki.
Dukansu biyun Kusa da ita suka tsaya, ta d'ago ta kalli Yah Muhd, ta mayar da dubanta ga yah Mas tace
"...........".Vote@wattpad khairi-muhd
Happy jumaat Kareem Allah ya bamu albarkar wannan rana ya taimakemu ya yaye mana damuwarmu yasan ya farin ciki a gidajenmu.
team#Maishamuhd
team#MaishaMas#vote
#comment.
YOU ARE READING
SARK'AK'IYAR SOYAYYA!
Romancea love story, this is a love triangle between 4 lover's.