💗💗💗💗💗💗💗
SARK'AK'IYAR SOYAYYAH
💗💗💗💗💗💗💗
By; FOULANI CERDIYA
&
KHAIRAT UPWattpad@ khairi-muhd
"12"
A GASKIYA BAMA SAMUN COMMENT YADDA MUKE SO, KUNSAN CEWA COMMENT DINKU SHI YAKE K'ARAMANA KARFIN GWIWA KUMA YAKE TABBATAR MANA DA KUNAJIN DADIN LABARIN, PLS COMMENT KO KADANNE MUNASO, KUMA IN KUKAYI ZAMUJI DADI SOSAI.
Abba ma yayi mamaki sosai yadda abun ya faru sai dai kawai sun barshi a tsautsayi ne baisan ya fasa ba.Sai dai Maisha da take d'aure masa kai, sosai ya lura da ita idan ana maganar ma dadi takeji, kuma zaki ga faraa a fuskarta.
Yauma a zaune suke suna cin lunch da yake Sunday ce, suna saurin su tafi Sahatussubiyan isalamiyya, saboda dukan latti ake sosai da sosai, gashi yau duty din wani malaminsu ne mai zafi, gashi ya iya bulala, kuma ba ruwanshi da kawo excuses kawai kina wuce 2:30 to bulala Biyar CE, ko wankin toilet.
"Maisha wallahi idan na gama bazan jiraki ba, kar ki jahomun duka gurin Malam Ali".
Kallonta tayi ta wani yarfe hannu tace" So....What? You can go".
Tana gama fadin haka ta maida dubanta ga Yah Muhd dayake shigowa da kyar saboda zafin da take masa, kyalkyalewa tayi da dariya har da ajiye cokali tana cewa "Oh Wai ni mutum in ya kusan zama gurgu ya yakeji ne Yah Rukayya".
Harararta tayi" banxa ke ai baki da hankali".
Tafa hannunta tayi "Af......Na manta Yah Muhd ya kamata in ma question din nan, ko Yah Muhd".
Ta karashe maganar tana kallonshi.Girgixa kanshi yayi tare da yin tsaki " Ke........kinsan Allah? Kika sake gani na kika mun dariya, yaseen sai na zubda miki da wadannan mitsi mitsin hakoran naki stupid ".
Rukayya ya kalla yace" ki tafiyarki kinji sarakina kyale ta, ita jikintane ke mata tsami".
Shiru tayi ta mik'e sum-sum ta fita.
Powder ta shafa sannan ta Dau Jan janbaki ta shafa (Tab islamiyya da kwalliya?)
Uniform dinta tasaka tana ta sauri - sauri Dan tuni Rukayya ta fice ta barta, sauri take kamar xata tashi sama, danma makarantar babu nisa sosai da gidan nasu.
Tunda ta kusa isa taji k'iraa means an fara tak'ara kenan, hankalinta tashe ta na zuwa kofar makaranta, ihun yara Yan makara ya daki kunnenta, ai batare da wata wata ba taji zazzabi na Neman kamata.
"Tab, ni yanzu in shiga ne ko kada in Shiga? Gaskiya bana son duka wayyo Abbana, koma dai na koma gida naki zuwa ince banda lafiya?.......Kai ai kuma dukan fashin yafi na makara"......... Zancen zuciyanta take tayi batasanma ya fito fili ba wata Yar class dinsu CE tace" Wallahi Maisha gara kizo mu tafi".
Ta jaho hannunta suka Shiga, aikuwa Maisha tace"nifa nafison abani wankin toilet".
"Lallai kema kinsan bazaa baki ba, yanmta ake bawa, kuma ma inajin angama wankin".
" Ku taho Ku matso nan kubi layi".
Malam Ali ya fada yana had'a uban gumi.
Matsawa sukai suka jeru, Inda Maisha ta koma bayansu, wasu sukazo suka tsaya a bayan ta, amma se kiga Maisha ta k'ara komawa baya.
Malam Ali yana kule da ita, hakan yasa ya kudurce sai yayi mata dukan dayafi na sauran.
Aikuwa kafin yazo kantama ya koma bayan ya kaho hijab dinta tuni ta tsanyare da ihu, sai da yayi mata ciki 8 a hakanma danyaji tausayinta ne.Ko a aji ma in banda Ku kanta babu abinda akeji, ga tak'ara sunayi. Malamarsu tai rarrashin ta gaji har ta kyaleta saboda tasan intafara kukan nan bafa zata dena ba.
Baccinta tayi a ajin har aka FITA sallah aka dawo, tana bacci Rukayya ta tasheta taki tashi, har said a aka tashi, Rukayya ta tasheta tace"ki tashi kinji Maishan Abba, an tashi".
Aikuwa da wannan kukan nata ta koma gida, Yah muhd tunda yajiyo ihunta gabansa ya fadi, yasan akwai matsala kenan.
Fitowa yayi ya kalleta fuskarnan tayi jajir abinka da farar fata.
"Lah.......Maisha meye haka? Da girmankin nan kika taho kina ihu".
Tana kukan tace" ni bawani girmana.......abinda ko abubuwan nan irin Wanda yake fitowa Yah Rukayya ban dashi(Wai mama)".
Maganar take tana Nuna saitin mamanta.Sosai ta kuwa sashi Dariya amma sai ya hade rai"ke banason shashanci, ki wuce kije ciki kin wani samu guri a waje kin zauna"......
Bude gate taji ta kuwa baza ido sai ga Abbnta, aikuwa tuni ta kara volume din kuka.
Jin kukanta yasa da sauri ya fito ya sauri ya iso gurin ta.
"Yau malam ya kad'e".
Yah muhd ya fada a ransa.
YOU ARE READING
SARK'AK'IYAR SOYAYYA!
Romancea love story, this is a love triangle between 4 lover's.