💗💗💗
KAUNACE SILA
💖💖
💗💗💗💗💗AISHA A .BAGUDO (MMN SUDAIS)
Page 32
Ganin ta fito da sauri ya biyo bayanta a kasa yaganta warwas cikin rudewa ya dauke ta Dan bata agajin gaggawa da kyar yasamu jinin ya tsaya ,Amman ya sha wuya Ga wani irin tausayinta dayaji yana sake bin jinin jikinsa
Duk yadda yayi kokarin abin yafi karfinshi Dan kuwa wani jinin ne ya kuma balle wa ,gashi bata samu kanta ba har sai da ya nemi taimakon Daga wajen wasu likitoci Dan kuwa shi ya shiga rudu ,an samu jinin ya tsaya sai dai kuma tana bukatar jini har Leda uku.
Jininsa zaa diba har Leda uku har sai da Dr kamil yayimishi magana da bai yi yawa ba kuwa zasu dibi biyu a nashi inyaso sai su nemi wani.
Yace Dr babu matsala ko Leda nawani Ku diba babu damuwa Duk yadda yake tunani matsala tasha gaban shi ,nadama da danasani babu irin wanda bai yi ba ,gudan jininshi ya zubar da hannushi in kuma shi kadai ne rabonshi a duniya fa,gaban shi ne ya fadi
Su uku ne akanta sun samu numfashinta ya dawo,da kanshi yayi wa inna waya da mama alhj hasan ne tsaye a kanta ,inna CE ta sanar da momy nafisa arude ta tawo .nafisa karfe biyu na dare ta farka ,yana zaune a kusa da ita ya zuba mata hannushi cikin nata jin motsen data yi ne ya gane ta farko da sauri ya mike yana kiran sunanta ,nafi sai ma ta rufe idonta wasu zafafan hawaye ne suke xubo mata,babu irin maganar da bai yi mata ba Amman ta shareshi.bandaki ya shiga ya hada mata ruwan nsi dumi xuwa yayi zai dauketa Duk da jikinta babu kwari,Amman sai da ta fisge tace ,na tsane ka ,ka rabu dani "
Kuka ne yaci karfinta jin kukan nan yakeyi har cikin xuciyar shi ,ya kasa CE mata komai tace, bana son kowani irin taimakon Daga gareka kai azzalumi ne banason ganin ka cikin matsanancin kuka komawa tayi ta kwanta kamar mai barci har asuba tana jin fitarshi masallaci .
Koda yadawo ma kusa da ita ya tsaya banda hawaye babu abinda idonta yake zubarwa ,cikin sassayan murya yace.
Don Allah nafi ba rokeki dakibar kukan nan haka ,kiyi hakuri nafisa "gefe ta juyar da kanta .mama CE da alhj hasan suka shigo ,a lokaci karfe shida na safe kamar tare suke da inna ,rashid ya gaishe su,duba daya zakamishi ka gane yana cikin damuwa da tashin hankali danasani da nadama mara iyaka inna CE ta matso kusa da ita tare da kamo hannunta tace nafisa?
Nafi tayi saurin bude ido hawaye ne suka zubo mata,inna cikin damuwa da yanayi datake ciki ita da mama hanuuta tasa tanashare mata hawaye.
" yi hakuri nafisa ,Allah yana tare dake ,insha Allahu zai baki wani"
Inna tace ,ai asara takin nema CE nafi da sanin Allah kada kiyi bakin ciki Duk abinda aka fara da rashi mai amfani ne yana nan tafe"
Haka ma alhj hasan yayi mata nasiha tare dayi mata fatan Allah ya mayar mata da mafi alkhairi, Dr rashid ya dauke ta cak yayi bandaki daita ,wani kallo da tayi mishi mai dauke da na tsane ka take auna masa ,wanka yayi mata da burosh ,ya fito ya dauki kayanta fes ya gyarata ya dawo da ita ya zaunar da ita a wata kujera mai kama da gado tea ya hada mata taki amsa,alhj hasan ne yayi musu sallama,momy da aunty Maryam ne suka shigo har lokaci nafi taki amsar tea din mama CE ta amsa a hannun rashid.
Inna tace ,karbi kinji nafisatu "da dabara ta amsa kadan tasha aunty Maryam ta matsa kusa da ita,tace nafi haka Allah ya dora miki,kiyi hakuri kinji bby na ,insha Allahu shekara mai zagayowa zaki dauki danki a hannunki ,yanzu INA ne yake miki ciwo ? Na daure cikin zubda hawaye Nace babu ko 'INA,kawai dai so nake a sallame ni "
Rashid yayi saurin Daga Kai suka hada ido ta banka mishi harara mai cike da tsana inna tace rashid bakayi magana ba yace naga bata gama warwarewa bane" cikin fusata tace,ko ban gama ba yau dinna ko Nace maka yanxu xan bar asibiti nan"
Ta mike cikin rashin kwarin jiki,yayi saurin kamata haba nafi ,ki bari na kara dubaki " tafada cikin tsiwa ,banaso ko ganinka ,ka fitar mini Anan
Yace nafi ..........
Ta Daga mishi hannu, tace please man don't say anything "mama CE ta kamata,tace sakarta inna tace haba kawalliyata bari ya dubaki mana " zatayi magana kuka mai tsanani yaci karfinta, ta ma kasa cewa komai hanyar waje tayi, mama tace INA zaki nafisa?
Tafiya zanyi tunda ba zai sallame ni ba
Dr rashid yace OK look nafi ,Bari a sallame ki"
Da suka fito ma sun sha fama da ita, Dan cewa tayi bazata hau motar rashid ba domin ba komawa gidan shi zatayi ba ,mama tace to ni mutafi nawa gida
Nace mata Aa kebbi zan kawai zani mominta tace Wai me yasaki haka ne ,me yasa bazaki yi tawakkali ba ?bafa akanki aka soma rasa ciki ba,Allah daya baki shi zai kara miki,kinji mamana zan dawo wani sati naganki
Ba karamin lallashi suka yi ba kafin ta yarda ta hau motar mama suna zuwa gida nafi ta shiga bandaki ta Dada gyara jikinta ,kayanta ta shiga hadawa da ma su mominta suna falo ta fito da jaka momy kutashi mutafi momy kasa magana tayi ,mama tace haba nafi ,Mr yasa ba kyar jin rarrashi ne?tace mama na gama zama auren kawai Ku kirashi ya bani saki na idan yatashi kada yamin daya ,uku nakeso "
Cikin tashin hankali inna Tace nafisatu kiyi hakuri kada kibari aurannan ya mutu badan rashid ba sai Dan ni nasan Ke mai hakuri CE ,nayi miki alkawarin in dai naji me ya hada Ku ni zan wuce dake kafata kafarki zan mayar dake gun iyayenki nasan Ke maijin magana CE Nace Allah inna zamana bashi da amfani
Dr rashid ne yashigo ,momy tace ai wanna shirmene" inna taci gaba da cewa wallahi yarinyar tana da hakuri tunda kikaga nafisatu rayiwa rashid haka da abinda yayi mata ai tana da hakuri
Inna ta nunashi ,yasan me yayi Mata momy da aunty Maryam sukayi musu sallama, Dr rashid shi ne yakai su airport ,inna ta dafa mata magunguna tana kula da ita sosai ganin yawan damuwar datakeyi yasa inna........
YOU ARE READING
KAUNACE SILA
Romancekaunace sila all talk about ,neglect of parent, true love, parental obedience.