61

2.5K 61 1
                                    

KAUNACE SILA
       💖💖
💗💗💗💗💗

AISHA A BAGUDO (MMN SUDAIS)

Wannan shafin naku government girls comprehensive secondary school aliero aisha  bagudo na gaisuwa a duk inda kuke nayi missing dinku  class mate ss3b  2009  ( Lagos,)
I ol miss u guys 😭😭😭😭💗💗🤝🤝🤝🤝

Page 70 

End

Tashi yayi ya nufi sashin nata, da extra key yayi amfani ,yabi dakin da take ciki da kallo ,samunta yayi zaune ta zuba tagumi tana kuka .ya isa kusa da ita ta rufe idanunta tana cewa dan Allah katashi ka bani waje Dr . banason ganinka , banason kasamin damuwa " ya kamo hannunta
Yace  shine  ni kika samin damuwa ,ka dai sawa kanka "na dawo daga office ko ruwa ban Sha ba na hadu da bacin rai ,haba nafisa kidawo hankali mana ,Kuma ki fahimce ni,tunda kike dani kin taba ganin wata alama da zatasa ki zargeni da  Neman  mata ,nayi matukar mamaki da Abu kalilan zai sa ki rufe Ido ki gayamin magana , amatsayina na wanda kike Neman aljanna a karkashina .kinga ni kuwa kome nagani aka ce ke kika aikata bazan rufe ki da fada ba, idan har na tambaye ki tsakananinki da Allah kika ce baki aikata ba.
Wato nafisa idan har zaki yarda dani zan rantse miki Allah ne kadai sheidana , ban aikata abunda kike zargiina akai ba, tabbas nine ajikin hoton nan,sai dai Kuma ni kam bansan hotunan nan ba tunda nike bantaba kebewa da wata ya'mace ba sai ke da Allah ya halitta min,nafisa nafiki tsanar zina ,ina kyamtarta , masu yinta ma shiriya muke  neman musu ,tun asali  ban taba kai kaina ba sai yanzu danake da mata na soma ajiye zuria haba nafisa ai ke ma dai Kya ce tabewata tayi yawa,.
Ya dada  daukar hoton ya Mika mata .
"Kiyi musu kallon tsab sannan ki dauko hotunan da muka dauka lokacin da mukaje England ,Kuma matar da kika ce kinga fitarta daga dakina baki santa ba .?
Bata bari naga fuskarta
ba"
Yace Sai kije ki duba bakuwar mai aikin da kika dauka ,kinmata masauki agidanki kintaimaketa Amman da ita akeson akasheki ,nasan duk abunda da kukeyi .Sam nafisa baki da tunani da wayo kowa ki kawo shi gidanki ,idan bakisan tsakanina da ita ba ,  Itace kausar , kausar Kuma kawar safiyya metro din ce, babu irin yadda bata nuna min so  Amman ni ko ajikina .

Ya dauko wayarsa ya bude mata irin sakonnin da hirarsu da sukayi da   kausar ,sai ta kwashe ta gaya wa safiyya ,ita Kuma ta juya shi ta turo masa.
Bakaramin gigitata sakon suka Yi ba , yadda ta haukace akan son sa da yadda take kushe ta awajenshi  hakika ta nuna wa kausar hotunan har ma kausar din ta dauki wayarta tana cewa sunyi matukar kyau,ta duba lallai kuwa haka ne ,sune  aka sauya su,amman zata bawa kausar mamaki  ,shr tayi tana tunanin wata rana   tayi wanka , ba wata kwalliya tayi ba dan batajin dadi ne Dr rashid yashigo  aunty sumayya tanayi masa magana sam shi Bai jita ba ,hankalinshi gabadaya yana wanjena ,sai kallona yakeyi .
Inna tace ,"ina fa zai jiki yana can yana kallon nafisa ?aunty sumayya sukayi masa dariya ai fa rashid akan nafisa babu dama .
Inna tace Allah dai yabarsu tare , Amman ana kaunar juna anan Dr rashid yaji abin da suke cewa yace Amin dai innata ai kawarta  taki ce babu dama ,Anya kuwa nafisa bata tafi kowace mace ba ? wallahi Aunty sumayya duk matar dana kalla komai gayunta ko kyanta  sai in ga bata kai nafisa ta ba " ni kuwa da  bansan me suke fada ba,hankalina yana waje n kausar da safiyya da suke kuskus ,ya jawoni jikinsa ya manna min kiss a baki da wuyana .
Aunty sumayya tace a gabana rashid?
Ya fita yana dariya ,tuni naga safiyya ta fita hayyacinta har da kuka nida inna muka shiga tambayar ta sai kausar tace ,bazata iya magana  ba yanzu wani abune ya fada mata a ido ,ni kuwa har da cewa Allah sarki  nan tarinka tuna abunda safiyya tarinkayi duk lokacin da zata takawo musu ziyara ,bata dauka da wani Abu ba .durkusa tayi gwiwa biyu tabashi hakuri tana Kuma mamakin halin irin na rashid yanzu duk ya sauya mata ,da ace da ne tayi masa wannan hakan  da sai ta gane kuranta ,nan suka shirya har ma suka karasa dakin rashid suka Lula wata duniya .
Da safe kausar tayi mamakin yadda ta gansu har takira safiyya ta gaya mata kausar me kike son gayamin ne wai har sun shirya kadafa kisa hawan jinina yatashi  ai kuwa sai dai ya tashi don sun shirya duk abunda kausar ke fada a kunne nafisa tana ajiye waya suka hada ido,t  nafisa tasakar  murmushi  ganin yadda kausar din tayi duk ta gigice  tace na gode kausa babu abunda zance miki sai godiya kin rike min gidana da Amana har kullum ina sake gode miki Amman ina son nasanar dake ama Dr rashid canjin aiki zuwa Abuja  zamu koma  can da zama har inna  shiyasa  Kuma cikin satin zamutafi shiyasa zan sallameki dan bazani yuwu mubarki ke kadai agida ba ,jikinta na  rawa tace ai babu damuwa ko yanzu ma zan iya wucewa nafisa tace Aa kibari kishirya a tsanake kinga yafi daman  anbiyaki kudin wannan wata ta kada kanta kmr kadangaruwa nace shi kennan  ,. nagode tabita da siyasa tabita suka rabu lfy da kwana biyu kausar tabar gidan.

KAUNACE SILAWhere stories live. Discover now