38

812 32 0
                                    

KAUNACE SILA
       💖💖
💗💗💗💗💗

AISHA A .BAGUDO  (MMN SUDAIS)

Page 44

Khalid dake zaune a babban falon gidanshi  dake  Lagos wanka ya fito" a wanni da agogo yanuna karfe biyar na yamma sanye cikin jallabiya brown color sai Dan karamin stool dake gabansa wanda ke dauke da tiren kayan marmari ,yadauki Koren apple ya gutsura tare da cigaba da kallon tautararon Dan Adam din daya kunna "kararawar falonsa dayaji ana danawa shi yasa dauki remut ya rage sautin TV din" yamike  yaje yabude kofar ,babban abokinsa kuma dan'uwan a gareshi ya iske  tsaye a kofar wato najib wanda Anan yake aiki tare suke tun a kano watannin Baya dasu wuce aka mushi transfer zuwa Lagos "hunnu ya mika masa suka tafa tare da tsakarwa juna dariya najib na cewa Banyi expecting zan sa meka ba na dauka ka wuce yace Aa," kozan tafi dai sai zuwa Gobe ko jibi akwai abinda zai tsayar dani .suka zauna Khalid yatura wa najib Tiran kayan marmari nan gabansa sannan ya nufi frij yakawo masa maltina da ruwa sanyi"  hira suka shigayi najib yace tun kafin namata abinda ke raina  "bari nasoma da maganar da takawo ni ya juyo ya kalleshi yace wace magana Kennan? yace akan zamannan naka ba aure yana damuna" Khalid ya bata rai yayi kicin kicin da fuska yakamata kamanta komai kayi aure shine cikar mutun da mutuncinsa " rayuwa bazata yuwu  ahaka ba,babu tabbas acikin rayuwa nan da kake gani ,akwai rai akwai mutuwa ko baza kayi Dan kanka ba ka dubi mahaifiyar ka tanason taga kayi aure koda yaushe maganarta kenna ya katse shi yanaji zafi  maganganunshi  yace naji zanyi tunani akai kadameni da maganar aure ,kai din yaushe kayi naka ? zakazo kanama mutane salo banza,yace salo ma nikeyi  karkayi kayi ta zama haka  har mahadi ya bayyana " hannu ya dagamai Malam  dakata kaxo  ne Dan kaba tamin rai ko yaya ,yace kodaya shawara CE  "yace to karike shawararka na gode  yanamai hada hannayenshi gu daya   in lokacin yi yayi zanyi basai kazo kana damun mutane da suraitai ba" najib ya bude baki zaiyi magana  yace bason damuwa kabarni kawai Anan yake sanar dashi haduwarsu da mukifat da gaske abokina ",karya zanma ko nataba kawo maka irin wannna zance kai naji dadi fa nadade INA addu'a hakan baki ya tabe "Allah ko"kaga faduwa tazo daidai da zama shikenan ka aure kawai kowa ma ya huta ,tsaki yaja yana zabgawa masa  harara ,najib yadauki apple yasoma ci yana mishi hira Amman Sam hankali shi ,baya tare dashi illa ma wasu takardu da yafi mai da hankalin sa akansu yacigaba da aikin dake gabansa soyake xuwa Gobe ya kammala da komai yabar garin Dan yayi kewar sanyi idanuwansa wato ya'yansa yanajin kwanakin dayayi baya tare dasu ajikinsa daurewa kawai yake" juyowa yayi yakali Khalid kana jina .yace uhm" nidai bazan gaji dagaya maka gaskiya ba " kadubi lamarin yarinyanar da kyau ka sausautawa zuciyarka akan laifinta "kasake dawo da ita cikin rayuwarka Kuyi aure kamanta komai kai ma fa danaka laifin" "shr yayi yana sauraran zatuttukansa marasa ma'ana  yanajin haushi da takaicin hali irin na najib mutun ba control " Malam karabani da maganar yarinyar nan banason ko dole ne "ko zanceta bana bukatar ji a wannan duniyar tawa OK" idan kaga kai kana da muradinta ,why not " kaji ka aureta dariya  yayi sosai har yana buga kafa hade da rike ciki," yanasa ke mai da dubansa Ga Khalid ya nunasa da yatsa yace kai dai anyi munafiki, kaga bar maganar na aure ta ai tunda ta zauna a zuciyarka bazan iya son abinda kake so ba " sai dai naji inaso ganinta  Khalid ya dago ya kalleshi yana maka mishi harara ,yace tashi kabarmin gida idan har shirmen zantuttuka Kane suka kawo ka, ya murmusa yace Allah yabaka hakuri Daga gyara kayanka sai yazama sauke muraba kai anyi Dan iska wlh tashi yayi yashiga yacanza kaya jikinsa zuwa kanana kaya ya fashe jikinsa da turaren masu dadin kamshi" yadawo falo murmushi tsokana najib yayi kaga abban twinss wanna wanka sai INA  kuma?yace yawo Dan yasan halin najib da danbanzar  tsokana kallon yabishi dashi nadauka zamu ,zaku INA kai dai Allah yarabaka   surutu nan naka yadau wayoyinshi da key din matarshi Dan baya bukatar direver .


Yana zaune a office dinsa ranar alhamis ana Gobe zai koma kano yayi bala'in zurfi cikin tunani "gashi dai Gobe zaitafi Amman har yau bai gama abinda yakawoshi ba .

Hannushi yadaura sama fuskarsa zuciyarsa ta taru ta hade kanta  waje daya jiyake kamar jini da ruwa basa yawo cikin jikinsa yadda yakamata" komai da yake cike da tunani haduwarsu yakeyi tabbas yanajin dafin datama Zuciyarsa", so yake tabarshi da tabon da tayimishi a tsakanin kirjinsa koyaji gagarumin gibin dayawa rayuwarsa wanda ya tabbatar da wuya idan mai goguwa ne har abada yazama dole yakoyamata hankali ya nuna mata shi va mutumin da zatayiwa wasa da zuciya ba ne 'kokarin yake ya danne abinda yake ji yana yawo acikin jikinsa babu dalilin da zai sa ya kuma dawo da ita cikin rayuwar sa ba.

Tsaye take kan kafafunta tashin hankali da firgice sun taru sun hade mata GU daya  tuda Daga lokacin da sectary tashigo ta ajiye document akan table dinta,  ji tayi kamar tasa hannun akanta tasoma  kuka saboda tasan dole tasa hannu Saanan tamika zuwa office dinshi da kanta "ita fa bata shirya wa haduwarsu awanna hali tafiso sai al'amura sun dai dai ta, asali ma bata yanke shawarar tun kafarsa ba, tadade tsaye tana tunanin shiga cikin sanyi jiki  hannunta tasa ta bude kofar mayatattacin kanshi turaransa ne ya  tabbatar mata da shi din ne, Duk da idanunta na kasa ji tayi jikinta yakara  tsanyi zuciyar na bugawa da sauri da sauri ," daman mara gaskiya ko a ruwa sai yayi gumi "jitayi idanunsa na yawo akanta kallonta yake yanajin zuciyarsa kmr ta tarwatse ,dauke kanshi yayi " hankalin kwance  ya mai da kanshi kan makeken table din dake gabanshi yacigaba da abinda yake "  Amman da za'abude xuciyarsa baza'atadda komai  baya Ga rikice da tsinkewar zuciya "    dago kanta tayi ta zuba mishi manya  idanunta ........

Kuyi hakuri da wannna

KAUNACE SILAWhere stories live. Discover now