KAUNACE SILA
💖💖
💗💗💗💗💗AISHA A. BAGUDO (MMN SUDAIS)
Page 41
Inna da ta dawo Bayan shigewar rashid Duk ta ji abinda suke ,hakika ranta ba karamin baci yayi ba "tashiga dakin inda taga rashid durkushe yana rike da hannu nafisa ,wani irin kallo ta watsa mishi , tanuna mishi kofa da hannunta tashi kafita rashid tacigaba da fada .
Rashid ba bakin bata hakuri " "tukunna ma akan wani dalili ne yasa ka zubar mata da ciki ,haihuwa CE baka so ?kayi magana idan baka son haihuwa sai kaje ka auri juya kaga ka huta Kennan.
haka kawai yara kubi kun dauki dabi'un nasara ,to bari zan sanar da hasan abinda kayi, rashid wallahi Duk kallon mai hankali nake yi maka Ashe kai ma sorry ne ,kuma Dan kaji Gobe goben nan zata bar maka gidanka kamar yadda nayi mata alkawari ."
Zubewa yayi akasa a dai dai kafarta ya daura kanshi akan kafarta kamar wani karami yaro ,hawaye ne suka shiga zarya a fuskarshi sai daya samu suka lafa ya samu bude bakin da ya iya furta wani Abu ,yace "inna don girman Allah kiyi hakuri wallahi bazan iya rabuwa da ita ba ". Tashi inna tayi tana cewa wallahi bansan kaima soko bane sai da ka zubar da danka a rariya ". Fita tayi tana fada shi kuwa cigaba yayi da zubda hawaye, ganin irin yadda ran innarshi ya baci bai taba ganin bacin ranta ba irin na yau kuma idan baba hasan yaji yasan zai ji babu dadi .
Ya juyo gareta yazuba mata idanushi dasuka rikede suka koma tamkar garwashi nafisa Dan Allah kada kitafi kibarni ,wallahi INA sonki ".
Tausayi da son mijinta taji yakamata ganin bacin ran da inna tasa shi , sai taji ba dadi "itama tanason shi km baza ta iya rayuwa babu shi ba" amman tana son yasan ya aikata mata laifi mai girma, jikinta yayi tsanyi ganin halin daya yake ciki hannunta ya riko cikin nashi yana kallon kwayar idanunta yace ki min magana dan Allah Kice kin hakura , tsigar jikinta taji suna mikewa tanajin kmr tafiyar tsutsa yake mata "idanunta " ta lumshe ,takama lips dinta na kasa tana cic cizawa, tanajin hutar soyayyarsa na ruruwa baza ta iya rabuwa dashi ba,ita da kanta tabbatar da haka, akan son shi , murya shi yasa ta jin tsanyi aranta kar ki barni Dan Allah yana sake matse mata hannu ",nidai kasakar min hannu kuma ni bason ka ka sawake min wanna wahallan auran naka ko na hutar da raina" bazan iya ba "ya furta a wahale in dai zan iya rabuwa dake tamkar zan rayu ne banida amfani"OK kasan da haka kazubarmin da gudan jinina Nidai bazan zauna ba , kuma ko kaki saki na ,tafiya ta zanyi ,kabiyo ni da takardata" da yatsunshi guda biyu ya bege wallahi nasake jin maganar saki zaki sha mamaki na" baki bude zatayi kuka yayi sauri yahade bakinsu ,idonunta, ta zaru ta zuba cikin nashi idonsa daya ya kashe mata, sannan yajenye yabar step daya tsakaninsu suna shakar numfashin juna hadiyar zuciya tasauke murmushi rainin wayo yayi yakai bakinsa saitin kunneta yace yarinya da alamar kin kamu da sona sosai, bakin ta motsa zatayi magana ya daura yatsan sa akai yace pl.....karki CE komai nasan kina sona ko ba haka ba ne ,to naji ni dai ki sake bani dama zan canza nadawo yadda kike so ,Amman maganar saki kibar ta dan bazan iya sa kin ki ba , kuma nasan kina sona rigth "kwayar idanunki sununa kiyi hakuri mu mori junan mu pl..... yana dage mata girarsa daya" haushi da takaici yakamata tace kasan Allah sai ka sake ko zan mutu da sanka yace " LA " bazama ki mutu ba muna tare mudun rai kuma zaki so ni fiyye da yadda Nike gani Anan ya nuna idanunta" ya kai bakinsa yayi kiss din idanunta da hancinta yayi kasa da bakinsa yakamo lips dinta nakasa ya tsotsa San ranshi " Sai da yagama birkita mata tunanin ta , gabadaya jikinta yaga ma mutuwa" tana jin da zaiyi fiyye da hakan ma bazata hana shi ba , hadiyar zuciya ta sauke tana watsa mishi harara ,aranshi ya tabe baki yace wannan daka baya Kennan , saboda yasan tana so shi tana dai makewa ne ,cikin kankanin lokaci zai mantar da ita komai sai muradinshi , yafijin inna Dan yadda yaga tayi fushin nan ke tayar mishi da hankali " haka ya tashi ya fita ciki tsanyin jiki har baya ganin hanya ,
YOU ARE READING
KAUNACE SILA
Romancekaunace sila all talk about ,neglect of parent, true love, parental obedience.