45

922 39 0
                                    

KAUNACE SILA
       💖💖
💗💗💗💗💗

AISHA A.BAGUDO (MMN SUDAIS)

Page 51

Yan'sanda  sukace Dole sai suntafi dashi sun koyamasa hankali tunda ya Dakar musu ma'aikaci .
Wayarta taciro ,number dady dinta tashiga nema wanna wani irin tashin hankali ne garin neman gira zata rasa ido, cikin saa tasamu ya Daga bayan sun gaisa tace dady  unguwa mukaje nida rashid shine mukayi dare a hanya muka samu matsala "ta Ga yamishi Duk abinda ya faru cewa yayi ta hadashi da"yansanda wajen ana ta mikawa babban cikinsu waya" nan da nan yakame waje daya Sai cewa yake sorry sir tuni suka kwance shi suna bashi hakuri ,police ne suka rakasu har gida ,cikin nafisa da rashid  babu wanda yawa wani magana suka shige sashen su .

Daga gawassu aka aiko musu malam mamma yarasu kakan rashid nawajen uwa" Washegari suka shirya inna da alhj hasan rashid da aunty sumayya wanda saboda mutuwar ne  tazo ,nafisa tace  Sai taje itama aunty sumayya tace shirya mutafi, da suka  fito zasu tafi ne" rashid ya kula da ita ,sai da kowa yarigasu  shigewa ya jawo hannunta tare da cewa ke kuma INA   zaki ?tayi narai narai da idonu gawassu "da izinin wa ?" Naka "to ban CE ba kikoma tace Dan Allah ta marairaice wucewarsa yayi ya barta a wajen tana kuka da suka shiga mota ne aunty sumayya tace Wai INA nafi ne?
Yace daman daita zaaje ?Auty sumayya ta watsamasa harara fita tayi taje ta taho da ita" kanne maman rashid sunji dadi ganishi tare da iyalinsa bare nafisa wayayyice Sam bata da duhun kai tasaki jikinta dasu sosai" jaka taballe tarinka rabamusu kudi Sam su aunty sumayya basuyi mamakin kudin datake rabamusu ba, saboda sun San halin rashid akwai sakin hannu  shi ma haka rashid yaji dadi  da yadda take yi da yanuwansa har Fita sukeyi tare Sam bata nuna kyama ko nuna ita yar birnice suna sha'awar irin kayan datake sawa ita kuma Duk wanda yanuna yana shaawar su " sai taje taciri tabaka sakina abokiyar wasan rashid CE tare suka shiga daji ta hadawa nafisa magungunan mata, da kanta ta dafa mata tace bai kamata kitafi haka ba zanshiryawa yayana ke da kyau ,dariya tayi wasu maganin  ta damka mata su, sakina kauyen gawassu take aure sana'ar tace magungunan mu na mata "koda nafisa ta tambaye game da maganin cewa tayi zaki kirani dankanki idan kikaga  aikinsa."

kwansu bakwai acan Amman alhj hasan da rashid sun dawo tun Washegari ana gobe sadakar bakwai ,dazasu tafi mutane gawassu sun hada musu tsaraba maiyawan gaske nafisa har kuka tayi .


Kwance yake akan gado hannunsa rungume da pillow idanunshi kyam akan celling sosai yayi zurfi cikin tunani twinss "Daga shi  Sai boxe da singlet fara kal "
kusan kwanaki uku kenna yake  zaune cikin kunci yakasa sukuni Ga kewar twinss dinsa na damunshi hjy da kanta ma takasa gane kansa, tasoma tunanin aje adawo dasu itama dauriya CE kawai ,yadan gyara kwanciryasa yana saka yadda zai kuma koma gidan ya debo yaranshi Dan hakurin sa yasoma karewa" yamike jiki babu kwari Duk boxe dinshi yayo kasa bai damu da gyara ba ahaka  yashiga bayi" ya Dade yana cuda jikinsa da cream bath " best quality bobo Whit" sanna ya fito hannunshi rike da towel yana goge jikinsa "yashirya cikin shadda ruwan kasa dinkin kaftan yayi kyau matuka ya yana feshi jikinsa da turaruka masu dadin kamshi da dagawa Duk wanda yashaka hankali.  INA jerin  takalmansa suke yaje ya dauko wani  Pam Amman kafanin  Gucci ne yasa, wayyoyinsa da mukulli motar sa ya dauka yazo falo inda hjy da Auty saa ke zaune suna hira ya gaida su yace shi zai fita,cikin miskilanci yayi magana  kallonsa  tayi  tace sai kadawo ya dauka ma zatamishi  maganar inya fita  yabiya ya daukosu  tafiya yake cike da jin kai da isa kana ganishi kaga Excellent guy har yaiso farfajiyar gidan inda ya park din motarsa yaje ya bude yashiga yabar gidan

Hjy ta kalli aunty sa'a baki lura da yanayin  kaninki ba sai wani cincin magani yakewa mutane kmr an kwace masa yara ne gabadaya tace kinsanshi da son yara balle kuma nashi tace ai nasan ta yadda zan bullo masa zanyi magani nsa ne dariya suka yi

Ko ya isa baki get hon yayi aka bude masa waje yasamu yayi parking yaciro wayar sa Daga gaban aljihun rigashi yayi dialing number sani yana dauka bayan sun gaisa yace gashi acikin gidan yace OK INA zuwa fitowa yayi yajingina jikin motarshi yana kar kada key mota tare da karewa gidan kallo ba laifi ya furta  " kmr ance yadaga Idannushi sama ganinta yayi zaune kan kujera a balcony hannunta rike da waya  gefenta kuma stood ne dauke da ruwa da juice sai wani plet wanda bai San komeye aciki ba "Ga Twinss zagaye da ita kowannesu ya jingina da jikinta kallonsu yake yana tunanin abubuwa masu tarin yawa akanta "ko ba komai yasan yanzu yadan rage jin zafinta akan da" twinss suka soma ganinshi dariya sukayi  Abba suka hada baki, Ummi abbbanmu yazo suna tabata da hannusu suna nunamata inda yake tsaye tamkar mashi Dan khalida ba baya ba wajen  tsawo " Allah yamishi kira mai kyau da fasali ,gabanta yashiga faduwa tasa tafin hannunta ta dafe tsaitin xuciyarta batare da tabari yagani ba  sannan  hankali ta daugo fuskanta cikin sanyi ta zuba mishi dara daran idannuta gabadayansu wani shock sukaji ajikinsa, ta tsinci kanta cikin wani moon ,shima hakance takasance tare dashi tsayawa CE taso gagararrasa   wani Abu yaji yana taso masa tunga tsintsiyar kafarshi yanabin gangar jikinsa wani miyo ya hadiye yana  kau da kanshi daga gareta juyawa yayi   Amman bai dainajin yanayin dayake ciki ba  "komai yanemi ya kwance masa meyasa Duk sanda zai hadu da ita numafashi ya sauke  ahankali yana runtse idanunshi ,da idanu take binshi dasu tana kallon bayanshi gaskiya  tayi kuskuren abaya  cikin sanyin jiki tamike tayi ciki yaran nabinta ummi inje  Abba, tace Muje nakai Ku tarike hannayensu "  sani daya fito da faraarsa ya nufi inda Khalid yake  yamika masa hannu jero wa sukayi tare har cikin gidan a zaune suka tadda hajja zamayayi yana gaisheta da faraa ta amsa masa hade da tambayarsa yasu hjy yace suna lfy  tashi tayi tashiga ciki ,dakin mukifat tashiga ta tadda zaune ta tasa yaran agaba tana kallo  hajja tace meyye haka kuma kitashi Ga khalid can yazo kije Ku gaisa  in kuma bazaki ba"   kituramasa yaranshi Dan nasan saboda dasu yazo tace wallahi tsoro zuwa  nikeji"  haka zaki daure kije maza tashi hajja takama hannu yaran sukayo inda yake har yanxu suna tare da sani yadan sake ba kamar farkon zuwansu   ba, dagudu suka kwace hannuwasu sukayi wurin shi  " suka shige jikinsa murmusawa yayi  pick yamusu agoshi yakuke , bayan fitar hajja da kamar minti biyu taje jikin mirrow tana sake gyara fuskarta ta dau turare ta feshe jikinta dashi 'sanna ta nufi main falon din su, shi yasoma ganinta Dan yana facing din step zuciyarsa tabuga, ai she dazu ba komai yagani ba  da sauri  sauri  numfashin sa ke sauka "kallo daya yamata ya kau da kanshi Amman fa Duk step daya daza tayi sai Zuciyarsa ta buga samun kasan yayi rungume yaranshi har takaraso tasamu wuri kusa dashi ta zauna cikin sanyi take gaida shi a dake ya amsa mata shima dan ganin sani ne ,xuwanta da kamar minti 5 hajja da sani suka barmusu wajen " ga juice nan daaka siyaya masa baisha ba "cike da tsoro tace bakasha drink ba shr yayi mata  bai CE da ita kala ba sai tadau cup din da juice din yake tamika masa tace kasha pl..... wata uwar harara ya galla mata wanda tasa kata saurin tsuke bakinta yayi magana cikin zafi Dan Allah Malam kindameni ance miki abunda yakawo Kenna, cak ta tsaya jikinta ne yasoma rawa sosai take binshi da idanu ya lura da irin kallon datake masa, tadauke idannunta Daga kansa zuwa yanxu Zuciyarta tasoma tsinkewa muryarsa ta daki dodon kunneta ki tashi ki  hadomin kayansu yanzu zanwuce dasu ,tace ai Sati biyu akace zasuyi yace da izinin wa zasuyi har sati biyu ,bazai yuwa ba wallahi ya juya ya kalle ta yana watsa mata mugun harara yace yau dinna kuma ayanzu zasubar gidannan" to koma dai manene kayi hakuri kabarsu zuwa wani lokaci ,ya nuna ta da yatsansa  yace baki isa ba, da can kinsa kina son su kibarsu batare da tunani kowani hali zasu shiga ba, Dan haka ko mutuwa zakiyi wayannan yaran bazasu rayu tare dake ba, Dan ya,'yanane, banda ke Kima manta dakin taba haihuwarsu, Dan bazan bariki ki kasance tare dasu ba .

gabadaya maganganunsa sun tsaya mata a kahon zuciya shr tayi Dan intace zatayi magana ,karshe komai yasake  kwabe mata kuma bai zai mata dadi ba ita yanzu sulhu take nena dashi ba futana ba"ta barshi Anan yana jijiga kafa, tsaki yake ja akai akai Duk tunani sa anason arainamasa hankali ne kawai ,hajja dakanta takawo mishi jakar kayansu ba kunya yasa hannu yakarfa yana mata sai anjima  har bakin mota tarakosu   cikin murmushi batare da  nunawa Khalid din komai ba

Koda tashiga daki Bayan tasanarda hajja sakon Khalid tagume tayi yaushe komai zai zama kamar yadda takeso, rayuwa na juyawa da ita kowani Bangaren babu dadi ,hawaye taji yana silalo mata tasa tafin hannunta tana daukewa .


Muje zuwa

KAUNACE SILAWhere stories live. Discover now