💗💗💗💗
KAUNACE SILA
💖💖
💗💗💗💗💗AISHA A .BAGUDO (MMN SUDAIS)
Page 37
Rungumeta cikin tsantsar fari ciki ,tana mai rike hannuta yarta ta har zuwa kan kujera two siter tare suka zauna,,cike da kaunar yar autar ta ,ta fadada fuskarta da murmushi, tace ya dawowa babu sanar wa, miyasa baki sanarwa da yanuwanki ba koda bazaki sanardani ba, tana Jan kunneta " kinsa yadda muke daukin dawowarki kuwa, takamo hannun hajja tahada da nata kimin afuwa basan haka danayi zai Sosa Ranki ba ,dariya tayi tace Aa ni raina bai baci ba sai tarin farinciki ganinki danayi ,naji dadin dawowarki sosai , kiyi hakuri nima tafiyar CE batazomin cikin shiri ba ,, ya karatun ankare lfy tace lfy, kwanciya tayi akan cinyar mahaifiyar ta, tana son tasamu natsuwar datake bukata Dagareta ,hajja tadaura hannuta akan autar har Dan karamin mayafin da ta rufe gashinta dashi yayi kasa gashin kanta take shafawa tanaji dadin gani diyarta domin duk damuwar danike ciki fata ta ta goge yanayin garin ya amshi jikina , hajja sai kallon diyar ta takeyi tayi kyau sosai sai dai ta dan rame kadan ,tana jin farincikin ganinta duk da ta hango tarin damuwa atare da ita gani ta mika hannu ta dauki wayarta tasan mai zatayi tace bari nashiga na watsa ruwa nacanza kafin yan'ukunki su karaso Dan da alamar su zaki kira dariya tayi sosai ai dole nakirasu suzo suga abin mamaki ,murmushi tayi haka ne fa baza'abar hajja ta kadai da abin mamaki ba " tashi tayi tashige dakinta tabar hajja zaune
ita kuwa hajja hannu tasa ta dauki wayar ta , tasoma kiran ya'yanta daya bayan daya
, Amman bata sanar dasu dawowar auta ba sotake itama tayi musu surpriseSannu ahankali yanayinta ya fara canzawa Daga farin ciki da shauki datake ciki zuwa faduwar gaba, takasa fahimtar abinda ke damunta tanajin laifin data aikata shine mafi girman zunubin data daukarwa kanta, tana son su tana tunaninsu ita kadai tasan maitakeji game dasu ta tasan baza taiya mantawadasu ba asabuwar duniyar ta sai dai ba yadda za tayi ,bata da wani zabi in dai ta tuna wannan ne kadai damar da take da ita na canza rayuwarta, kuma zatayi amfani da damarta ,wanka tashiga batajima ba ta fito cikin doguwar riga less datasha stone work sai kyali take zubawa falo ta nufa Dan tanajiyo muryar yanuwanta , taku takeyi ahankali har karaso inda suke cikin tsantsar farinciki take binsu da ido , da kallo dukkansu suka bita dashi Da mamaki ganinta Dan koda wasa basu ran ganinta ba km ko hajja takira su bata cemusu tadawo ba tadai CE suzo tanason ganin su cikin murmushi tace kuna mamaki ganina ne ? Ba dole ba yaushe kika dawo ,hour daya datawuce hannunta salis yakamo ya zaunar da ita kusa dashi cikin sanyi murya mai bayyanar da farinciki awani shashin daban kuma take adana bakin ciki dake zuciyarta ,tace Kuyi hakurin da rashin sanar daku dawo wata dabanyi" tana mai hada hannuyennta guda biyu waje daya dariya sukayi gabadayansu, ya Auwal ne yaja mata kumatunta yace farincikin ganin ki kadai ya goge komai ,hira sukeyi irin ta yanuwan da suke matukar Son junansu ,hajja dakanta ta shirya wa autar ta abincin da tasan tafi so, byn tagama ne tace su taso suci abinci ,dinner suka hau suduka ,hajja tace kowa ya matso Amman banda kai ta nuna Auwal in ka koma gida kaci na matarka dariya muhd Sani yayi yace yauwa hajja da kin kyautamin wlh kinmin daidai yaje yaci na gidanshi saidai salis hankalin shi na waje mukifat suna hira rsu Dan inkagansu suna zaune baza kace sakuwarshi ba CE ,murmushi ya Auwal yayi yace haba hajja kibari naci abincin naki nasan girkin da dadi km ma ai kinsa ni gilashi ne zaki iya hana kowa ki bani ada ba ,ban yaxun yaushe rabonka daka ci abincinmu kullum kazo sai anmaka tayi abinci kace ka koshi sai yau km zakazo da salo , Allah banasan girkin yan aiki ne shiyasa yau kuma naga saboda auta da kanki kikashiga kici dariya suka kyallkyaledashi yace to shi kenan yau kawai kibari naci da Yan 'uwana dariya tayi tace nabari Amman kadan zakaci dariya suke yi gabadayansu abinci tahada musu ta tura tsakiyar suka soma ci , kadan kadan take cin abinci , atsanake take bin fuskokinsu da kallo murmushi tayi tana mai matsar da spoon din da taciko da abinci ta ajiye tace INA jin dadi kasancewa tare daku ,atare suka hada baki muma haka ne muyi kewarki sosai fiyye da tunaninki daba kyana gidan shr babu dadi ,
YOU ARE READING
KAUNACE SILA
Romancekaunace sila all talk about ,neglect of parent, true love, parental obedience.