47

844 44 0
                                    

KAUNACE SILA
💖💖
💗💗💗💗💗

AISHA A.BAGUDO (MMN SUDAIS)

Page 54

Zaune take akan kujera mai zagaye da makeken table hannunta rike da waya tana magana da wata kawarta dasuka hadu awani group ta what's aap bayan tagama wayar tajiye wayar hannunta tayi shiru idanuwanta na kallon celling office din tayi nisa cikin tunani gibin da tama rayuwarta wanda ta tabbatar da wuya idan mai goguwa ne" yazama dole tanisanta kanta dashi ko bakomai hakan zai sa taragema zuciyarta radadi .

Duk da tasan ahalin yanzu bata cikin duniyarsa gashi ita yanzu take jin wani irin maseefar kaunarsa. bataki ace sunkasance tare ba muddin rai , tana sonshi har batasan yadda zata milsalta ba tana kaunar zama cikin ya'yanta tabbas tayi babban kuskure abaya datakasa fahimtarshi "Ashe ma soyayyar datama rashid ta karya CE basonshi tayi ba sai yanzu take gane haka hawaye masu dumi suka zubomata" bayan hannunta tasa ta goge tashi tayi tamike tadan gyara mayafin kanta tasoma hada wasu copies da yau kusan tsawon kwanaki shabiyar Kenna datayi sing Amman tsoro da fargaba ya hanata kai masa ,cikin tsanyi ta nufi office din tayi nocking ta Dade tsaye sannan yabada izin shiga" koda tashiga tasamu waje daya takame ,waya yake amsawa, yayi kmr bai San da shigowar ta ba " can taji yayi murmushi yace OK hjy kiyi duk abunda yadace tunda kince yarinya takwanta miki nima na amince zan aure da zuciya daya kuma har naji naso sonta " duk saboda yaganta tsaye ne yasashi fadin haka " ya ciza gefen lips dinshi yana yana Shafa fuskarsa fuskarsa " can gefen hjy tace to Allah yayi albarka yace ameen ,ya tambayi twins sunan lafiya yace ok zanturo miki da sako sukayi sallama .

Tsayuwa ne yanemi gagarrata zuciyarta CE keneman tarwatsewa" wayyo Allah na me kuma ke shirin faruwa dani " aure ta furta akasan zuciyarta to aure zaiyi Kenna? inde taji da kyau zance aure taji yakeyi da hjy ,duk da bataji abunda hjyr kece masa ba, da idanu take binshi har yagama wayar bata kuma fahimtar komai ba

Ko takanta bai bi ba ya tsuke fuska yace malama kidainamin irin wanna kallon na munafurci ,in ba haka zan kwakwule wayannan idanuwan naki masu kama Dana agolar nafawa .

Shiru tayi cikin zubda kwalla tare da zamewa kasa ta tsugunna tasaki kuka mai cin rai , tarasa me ma zatayi taji tsanyi aranta saboda tashin hankalin data tsinci kanta ciki shikennan tarasa damar da ta kwallafawa rai " zuciyarta ke beating dum ",dum, matsowa tayi in dayake ,da sauri yaja baya yace meyye haka kuma ,meyasa .....cikin kuka , bazaka yafemin ba Dan Allah Khalid na rokeka kamin sausauci ,ka tuna kataba cemin bazaka taba daina sona ba akowani hali takasance to yasa yanxu ka tsaneni? Ya Daga mata hannu kinga dakata malama me ma nayiki kinzo kincikamin kunne ? tarasa mezatace masa ya fahimce nufinta, tasa hannu ta goge hawaye ta tasake matsoshi wanna karan ko motsawa baiyi ba, tace Dan Allah kace kayafemin ko zanga daidai a rayuwarta yace dakikayi me kenna ai bikimin komai ba ninasan namaka pl....kace kayafemin yace baza'ace ba ke..... me ya kawoki office dina ? cikin tsanyi murya tace Dan Allah kamin algae mar guda daya inde auren zakayi da gaske kabani yarana nacigaba da rukonsu a hannuna ya watsa mata mugun harara inajin kanki yasoma kwance wa ta zuba mishi ido yau ita Khalid ke ma irin wanna cin fuska bakajin koma sai sautin kukanta shi mamaki ma take bashi da alama tasoma samun tabin hankali.

Shiru yayi yamtso yatsaya akanta yakafeta da manya idanunshi yanajin yadda take fidda sautin kukanta mai bugarmasa da zuciya, tsarki yaja cikin lumshe ido ya juya yakoma kan kujera, yayi baya yana jujjuyawa yana kallon ikon Allah yana ganin kamar tasamu tabin hankali akanta, yabata ya'yanshi dayagama shan wuyarsu, alokacin da ta juya masa Baya kai impossible ya kare mata kallo tsab sanna yace kinsa Allah in Duk duniyar nan gatanki ne ,bazanbarmiki su ba ,sudin nawane nikadai banda ke nasha gaya miki ki kiyaye cema yarana ,ya'yanki kije ki haifi naki OK sai yanzu nasan dalilin kuka naki wato maganar auren dakikaji ne zaki zomin da salo, ayya yarinya kin Dade da makara ,takuma fashewa da kuka yace kinga nifa kin cikamin kunne da wani banzar kukanki, inakwa abinda yakawoki pl.....kiyi kifitarmin a office banda lokaci sauraran shirmenki dankinsa kina sonsu kibarsu OK sai yanzu zakizomin da ranin wayo inda nace zan aureki yanxu nafasa,yaja tsarki yarinya da sauranki wlh Khalid fa yamiki nisan da bazaki taba kamoshi ba yakashe mata ido daya "kije ko rashid zai iyayin manage da saurana ya furta yana furza da huci Dan tsabar kishi . sai yanxu taji kwarin iya magana tashi tayi cikin zafi rai ta kankace idanunta tace kar Allah yasa ka hakura kuma komai zakace kace ka dade ,naga Kaine SILA maida ni haka" kuma duk kin ka dani ,baka isa kacanza musu ni amatsayin uwa ba ta nuna kanta ,ni din dai nice uwarsu ko kaki ko kaso,mai mugun hali ta wa tsa masa copies din hannunta suka tatwatse har a fuskar sa ,da idanu yake binta dasu, tun da ta soma magana bai yi mamaki ba , yasan tanada tsiwa amnan Bai dauka har yanxu zata iya abunda tayi ba duba Ga matsayin shi yanxu a gunta idanushi ya runtse yanajin kmr yashi ya tsintsinkamata mari bude idanushi yayi .

Ciki zafi fuuuuuuu tabar office tana buga masa kofar da kallo sectary Ke binta Dan tun daxo yake sauti kmr fada fada ,to meyye hadin oga da ita ? office din takoma ,kuka tayi sosai tanajin Haushin kanta ji yadda rayuwa take tangaliyya koda lokaci tafiyar ta gida yayi a parking lot suka hadu yana jingine jikin motarsa hannusa rike da waya kallo daya yamata yadauke kansa,ita ma ko duban inda yake batayi ba ,takasan idanushi yake kalonta gabadaya yagama mika wuya Dan yasa tabbas still now yana sonta yadai kasa yin hakurin abunda tamasa ne " ta gefenshi tazo tawuce"Dan sunyi parkin ne kusa da juna " "taxo bude mota, ta daura hannu Kenna daniyar bude kofar taji yadamke mata hannu jikinta ya dauki kirma saboda tsoro Amman sai ta dake " dubanta yakeyi yana kallon Shep dinta barin ma Dan karamin bakinta jiyayi kamar yajawota ya rungume ta"yayi missing dinta kwarai ,yasake yakamo hannunta cikin nasa yamatse gam har sai datasaki kara kadan mara sauti yace ni kikama rashin kunya yana tsareta da ido ,ke mema kike nufi dani ko ni sa'anki ne "ta tsuke baki yasake matse mata hannu tace zaka ballanine ?koda yake ai ba yau kasa ba OK kima maidani abokin wasanki ,bari na ballaki da tushe kinga sai ki tabbatar , tace nidai kasarkamin hannu, shima yarasa meyasa yake tsaye agabanta , da kyar tasamu ta fusge hannu yana can duniyar tunani da sauri ta juya tabarshi a wajen Dan taga alamar soyake yaga bayanta

Dakafa ta taka har bakin get koza ta samu motar haya , Amman shr tafiya taci gaba dayi cikin tsanyi tarasa INA zata nufa ,gashi unguwarsu da Dan tazara Amman haka tarinka tafiya tayi nisa sosai taji ana mata hon ta bayanta Amman taki ko juyawa taci gaba da tafiyarta, gabanta taga ansha da mota ,taja da baya ta tsaya tanason taga Waye mai wannan karfin hali motarsa tagani warning glass yayi ya kwashe da dariya ,kinga karyar rashin kunya ko , kar ma kiyi wahalar komawa Dan nace kar abarki kidauki motarki ,kadan kika gani ,yamata murmushi mugunta ataka lafiya ,ya fige motarsa da gudu yawuce ta ,ita ma tasan tayi kuskure barin company batare da motar ta ba, Dan da wuya tasamu abun hawa , ba kasafai ake samun abun hawa saboda silent place ne , haka tacigaba da takawa har ta iso gida agajiye liliss......

Da magariba hajja taleka dakinta kasancewa taji motse shigowar ta tun rana ganin bata da niyar fitowa yasanyata shigowa kwance taganta can karshen gado akudundune karasawa tayi gurin tasoma tashinta gabadaya jikinta ke k'ymar tsabar yadda zazzabi mai zafi gaske ya cafketa cikin lokaci guda, sakamakon kuka da wahalar hanya da tasha Ga tunanin abubuwa daya data rasa arayuwarta.

hankali hajja yayi matukar tashi ganin yanayinta batare da bata lokaci ba takamota ta zaunar da ita duk jikinta ya dauki zafi tace baki da lafiya shi ne zaki kashe kanki adaki , maganin zazzabi taje takawo mata hade da ruwa bayan taba ta takamo suka dawo falo suka zauna ta kwantar da kanta akan cinyarta hajja zubda hawaye hajja tace duk zazzabi hajja tace duk kinbi damu kanka da tunani da kuka gashi bikinki sai matsowa yake ta Dan mike afirgice tace wace zata aure kuma tace kimana daman tun jiya nike son sanarda ke mahaifinki yabada ke gawani ,sakada Kenna akabada ni shikenna tawa takare hajja tace haka zakiyi hakuri mungaji da samiki ido zaman ki haka ya ishemu Dan haka sai ki shirya yau saura kwana 7 Ayi biki cikin sauri tace kar ma Ayi bikin kudai kudaura aure kawai tunda kungaji dani ta fashe da kuka hannu hajja tasa tana Shafa kanta kiyi hakuri zakiga riba yin haka sai nan gaba kinji ki amince da wanna zabin bazakiyi Dana sani ba .....


Muje zuwa

KAUNACE SILAWhere stories live. Discover now