48

757 34 0
                                    

KAUNACE SILA
        💖💖
💗💗💗💗💗

AISHA A.BAGUDO (MMN SUDAIS)

Page 55

Hawaye ke silalo mata tanajin radadin zance hajja
Kiyi hakuri da wanna aure bakinsan alkhairin dake ciki ba "nida kaina INA farin ciki da wanda zaki aura Dan babban gida ne kuma iyayensa nada mutunci da datako" kema dazaki San kowaye zakiyi matukar alfahari da  samunshi matsayin miji" nasiha sosai hajja tayi wa diyarta akan zaman aure da rayuwa"  hawaye take har yanzu takasa furta komai tashi tayi jiki ba kwari ta nufi dakin ta" komai yagama kwance mata wayar ta dauka takira kawarta hanna bayan ta dauka ta labarta mata abunda ke shirin samunta ,ita ma din hakuri da nasiha tayi mata tace insha Allahu zan shigo xuwa jibi "alamarin da cazawa mukifat hankalin shikena tarasa komai nata bata da madafan kamawa, gabadaya  Daren ranar bata samu ta runtsawa ba, ga zazzabi mai zafi  daya rufe ta, kafin wayewar gari har karamin rama tayi .

A week later

Shirye shiryen aure mukifat akeyi bakama hannu yaro ta ko INA sai Faso kai akeyi na nesa Dana kusa  mukifat duk ta rame tayi duhu kamar ba amarya ba" tadaina magana da kowa sai dai idan akamata magana bazataki amsawa ba ,kuma cikin sakin fuska zaune take a tsakiyar yanuwanta da sukaxo biki , hajja tashigo da sallamarta ta zauna akan gado Bayan sungaidata suka watse suka dawo falo ,hanna CE  karshe Fita ta rufomusu daki ,ta kalli diyarta da kyau tace INA son kibani hankalinki ki saurareni kiji abunda zan  fada miki ,gyara zama tayi tace hajja inajikin kuma ashirye Nike dayi  duk abinda zaki fadamin ayanxu Banida wani burin arayuwarta sai abinda kukace ,zayi komai batare da gaddama ba ,ko jayayya albarkanku kawai Nike nema ayanzu" zan muku komai koda hakan bazaici karo da raayina ba koda zai zama cuta agareni ta karashe magana muryarta na rawa alamar daf take datayi kuka Amman ta danne......

Insha Allahu bazakiyi bakin ciki da wanna aure ba ba kuma zakiyi Dana sani ba ,nidai ki kwantar da hankali ki" nida mahaifinki ba'abunda zamuce miki sai Allah yamiki albarka" bazamu aura miki wanda mukasan zai iya cutar da rayuwarki ba , INA tabbatar miki cewa sai kinyi alfahari da wannan aure, daman  nazo nasanar dake mijiki ya roki alfarma akan bazaiyi  komai dangane da bi'dia ba "yanxu Bayan daura aure sai taron da yazama na ala'damu ta dole sai amikaki dakin ki" mukuma amince da haka karki saka komai aranki kinji kisaki Ranki takamota hannunta ....

Yake tayi wanda yafi kuka ciwo tace haka yayimin dadi fiyye da zaton ki na amince bakomai ni  yanzu burina  shine nafaranta muku ,Abu daya nikeso shine addu'ar Ku " banji zanyi tsawon kwana nan gaba, wanna karan hawaye take zubarwa...masu ciwo hajja kimin alkawari ko bayan raina duk lokaci da kuka tuna dani kumin add'ua samun rahama gurin ubangiji .....

ciki kuka  tace narasa ya'yana narasa farincikkna ya zanyi da rayuwarta tana kuka jikin  hajja ta rungumeta, itama jikinta yayi sanyi kmr tafito  fili tagamata gaskiya alamarin  Amman bszaiyu ba wanna alfarmar da hjy fatima  tanema ne abarsu kar asanar dasu " anya kuwa mummuki adalci rashin sanar dake dabamuyi ba" tace karki fadi haka tunda Ku kuka haife ni, kungamamin adalnci arayuwa , bacutar dani kukayi ba duk laifi na ne wanna,hajja tace  kiyi hakuri wata rana da kanki zakizo kifadamin farin cikin da kika tsinci kanki ciki , tashare mata hawaye nasiha hajja tamata mai ratsa jiki wanda haka yadan kwantar mata da hankali ,ita yanxu tayi sallama da jin dadi a arayuwarta Daga gobe lokaci da aka daura mata aure da Mr no name Dan  batasan sunnan wanda za'abawa ita ba.

Bayan an daura aure haka akasha biki cikin farinciki da anashuwa sabanin amarya.
Zuwa dare mutane Duk sun watse sai yan tsiraru wanda zasu kai amarya
Bayan anshirya amarya ciki wata dakakkiyar gezner da tasha aikin stone work sai zuba kamshi takeyi ,takalmi da mayafi duk kala daya ne da kayan jikinta,mayafi aka yafamata akai har fuskarta ba'a gani wajen hajja aka kaita tamata fada sosai  .

Da kyar aka bambareta Daga jikin hajja kuka take kmr zata mutu,  akajata Sai filin jirgi zuwa kano ta dabo Allah sarki abun tausayi .

Bayan sun sauka sunsamu tarba ta musamma, Dan  hajiya fatima ba Daga nan ba, wajen karrama baki ta amshi lambar yabo" amanarta aka danka waje hjy tasa hannu takamota tana murmushi ai mukifat diyatace Allah yatayani riko kowa ya amsa da ameen banda Maryam da Khadija dasuka tabe baki sai cika sukeyi suna batsewa, hjy tace akai ta part dinta ta huta.

bayan kowa ya watse Sai it kadai akan gado Dan har hanna bata zauna ba Dan dama anriga da amusu buking din jirgi go and come .
 
Da daddare tana
Tana cikin tunani taji anmurda kofa kmr tasaki fitsari ko ta tashi ta antaya da gudu takeji, sallama taji anyi da murya da tasani Amman bata taba zaton jin Anan gida ba da kuma dakinta  rudani da tashiga yasa takasa amsa sallama karo na biyu da aka sake maimaita sallama tare da shigowa Ga badai....

Ta mayafi ta hagoshi  cak kukanta ya tsaya lokaci daya tayi wurgi da mayafi da take sanye dashi mikewa tayi tsaye akan gado kafin ta sauko kasa  shima  tsaye yayi cak kmr andasashi yana  kallonta Daga  bakin kofa bai karaso ba ....
Takowa yake ahankali ita kuma tashiga ja da Baya cikin tsoro da firgici bakinta nason furta wani Abu Amman takasa furta koda kalma daya, da hannu yake nuna ta dashi daman kece......

Manage pl.......

Muje zuwa

KAUNACE SILAWhere stories live. Discover now