KAUNACE SILA
💖💖
💗💗💗💗💗AISHA A.BAGUDO (MMN SUDAIS)
Page 57
Yau kusan watan ta daya Kennan agidan Amman tsakaninta da Khalid sai gaisuwa shima sai yaga dama yake amsa mata" iya kokarinta tanayi naganin tajawo hankalin sa zuwa gareta ,Amman abun yacutura, tarasa yadda zatayi dashi, babu irin shigar da batayi tsirara ne kawai yarage mata dabatayi ba tana mamakin dauriyya irin nasa duk da tasan yana da bukatanta ,sanye take cikin kayan barcci mai shara shara da karamin pat ,tafito Daga daki tana mika gashin kanta ta tufke shi atsakiyar , a falo taganshi zaune sanye da da wando short nika da singlet yana aiki a system dinshi ,kallo daya yayi mata ya kau da kanshi yacigaba da abunda yake yana sauke hadiyar zuciya "tafiya take ahankali har tashiga kicin ta hada tea mai kauri tazo ta wuce ta gabanshi ta juya mazaunata , kayan jikinta basu da mara ba da tsirara , bayanta yabi da kallo , yana lumshe idanu. ," ya Allah" yayi furuncin akasan Zuciyarsa system din ya kashe , ya kwashi wayoyinsa ahankali yamike Zuciyarsa da gangar jikinsa sun masa nauyi , ya nufi dakinsa yanajin wani irin matsananciyar sha'awarta na fisgarsa ya zauna abakin gado hannunshi tallabe da kanshi .
Da Misalin goma na dare tasake wanka tasaka wando bomba shot da yar karamar riga da bata wuce iya cibiyarta ba ana hango rabin nonuwan dasukayi suntuma suntuma "dakinsa ta nufa ta tura kofa tashiga kamshi ne ke tashi ajikinta ta ko ina kwance ta taddashi sambal akan gado" hannunshi a sama kirjinshi ahankali take karasowa gareshi tun shigowarta zuciyarsa ke bugawa yanayinsa gabadaya yagama canzawa sakamakon muguwar sha'awar dake tattaredashi ,runtse idanunshi yayi,gam yana tunani meyakawota yau har dakinshi ,waje tasamu kusa dashi ta zauna tana sauke numfashi "zuciyar ta na wani irin bugawa da sauri da sauri "ta matsoshi sosai cinyarta ta gogarta nashi, hannunsa takamo cikin nata tana murzawa ahankali " jin kusancinsu tare yasashi soma Fita haiyacinsa gashi yakasa raba hannusa danata , tacigaba da shashafa shi sannu sannu "Idannushi dake lumshe yadan bude, ido cikin ido suke kallon juna sun dade ahaka yakasa dauke kansa Daga gareta zuciyoyinsu ke bugawa atare yanason yadakatar da ita Amman yakasa yunkurin yin haka ,meyasa yake jin wannan yanayin muddin tana kusadashi " mikewa yayi ya zauna suna facing din juna gabadaya yasoma sakin layi .kwanciya tayi a saman cinyasa har yanzu takasa furta koda kalma daya ne ,still hannusu na sarkafe da juna ta kafe shi da ido "da kyar tasamu taiya bude baki tace abban twinss ......Dan Allah kayi hakuri ka manta da abubuwan da suka faru abaya ,kabari muraya wannan auran cikin farincikin, Dan Allah kaji " ni da kaina nayi nadama abunda nayi ,ya hadiye wani miyo daya tsaya masa a wuya yana sauke naunauyen hadiyar zuciya shima ita yake bi da kallo gabadaya ilahirin jikinsa ya mutu murus"jikinsa yayi tsanyi ta daura hannun bisa kirjinsa tana shashafa kwantaccen gashinsa mai taushi tace kayi shiru bakace komai ba ,yana zaune yayi shiru kmr andasashi 'ta rankwafo da kanshi saitin fuskarta suna shakar fuskantar juna , hancinsa na gogar nata yanason ya hannata Amman bashida kuzari yin haka , ahankali ta hade bakinsu waje daya tadanna harshenta tasoma tsotsa tana lumshe idanuwanta shima bai San sanda yasoma mayar mata da martani ba , kusan minti 20 suka dauka a haka sannan ya zareta ya mike ya nufi bayi ya watsa ruwa hade da dauro alwala, kwanciya tayi tana sauke numfashi .... bayan ya fito zaton shi ko tayi barcci nafila yayi sannan ya hau gado nisa da ita ya kwanta yana dafe da jijiyar sa da take harbawa , dan taki komawa normal "juyi tayi ta shige jikinsa ta lafe luf yarasa yadda zaiyi da ita ,yace wanna jarabar gabadaya ta kanenayeshi ta hanashi sakat" haka ya hakura har barcci ya dauke ta ,yatashi matsar da ita ya gyara mata gashinta daya sauko saman fuskanta, sanna yajuya ya kwanta yana matse jikinshi.
Washegari rana
asabar ,da wuri ta kammala ayyukanta tayi wanka tashirya cikin atamfa riga da siket data karfi surarta gyara jikinta tsab "ta yane kanta da mayafi ta nufi shashin hajiya fatima ",da sallamar ta tashiga ta samu waje kasa ta zauna ganin hjy akan kujera" kanta kasa ta gaidata cikin sakin fuska ta amsa mata , tanajanta da hira sama sama cikin ladabi take mayar mata duk har yanxu taki sakewa da hjy tadan jima zaune suna ta hirarsu har dasu twinss tajima sannan takoma part dinta ta dau remut tacanza channel tazauna tana kallo tana tunani hali Irina Khalid ita dai bata taba ganin mutun irinsa ba tarasa meyake nufi da ya tayi kwaliyyar ta nuna masa da ido da gangar jiki Amman Duk a banza yake kallonta da wani ne yagaya mata zai iya shareta haka zatace karya ne sai gashi ya nuna zahiri true colour dinshi sosai tayi xurfi cikin tunaninsa tanajin wani irin maseefar kaunarsa nabin tsansar jikinta suna bin jini da tsoka jitayi an bude kofa hade da banko labule afirgice ta tashi Dan taji tsoro matuka gani su tayi tsaye suna yatsina fuskokinsu kowacensu sai cin magani suke cikin sakin fuska tace sannuku da zuwa kukaraso mana Maryam da Khadija Kenna yau shine zuwansu kusan na biyar kuma duk zuwan dazasuyi sai sun mata rashin mutunci iya son ransu hade dayi mata goregore Amman bata tanka musu sai tabisu da asauka lafiya " dariya tayi tamike tsaye tana nuna musu wajen zama da hannunta maryam tace aiko baki CE ba ,zama ya zama dole acikin gidan nan tunda ba na uban mutun bane ran mukifat yasoma barci taji wani Abu intaso mata Amman tashare taje ta bude firij ta dauko musu ruwan tsanyi da kayan fruit taxo ta'ajiye a gabansu takoma gefe ta zauna, ita dai batada da matsala da kaf dangin Khalid sabanin su maryam tarasa maitamusu fa suke nuna mata rashin kauna,
Amman indan ta tuna hakan nafaruwa daya acikin alumma , sai ta danganta haka da rashin haduwar jinine kawai Dan ba haka aunty sa'a take mata ba Kuma bakowa bane zaiji kayi mishi ba " ganin basu da niyar gaida ita kmr koyaushe insunzo " yasa tace musu sannuku da xuwa sukayi banza da ita suna tabe baki shigowar twinss ne yasake bata musu rai takamosu ta rungume suna ta zuba mata surutu tace bakuga su aunty khadija bane kuje kugaishe dasu ,maryam ta watsa mata wani kallon banza sannan tace Amman dai ke dakiiiyar inace wayan shegun yaranaki zaki koyawa tarbiya bayan basu gada ba, kar kisoma hadasu damu Dan basa cikin lisafin ahlin gidan nan kema da sannu zakibar gidan basai ankoreki ba tunda bana ubanki bane banza mai abun kunya ran mukifat yayi mugun baci cikin zafi tace yadda bana uba bane haka bana naku uban bane, sai kujira randa kukaga kafata agidan alhj Ibrahim mai turare sai kuyi jarabarku dakuka gada awajen gyatumi tsaye yake tun sanda tasoma magana ita kuma sai yanxu ta luradashi sapanin su ,ta kalleshi da kyau ta nunashi tace yauwa ga mai abun kunya nan tanunashi shiya gogamin zunubinsa yazama abun gori kuma abun kunya ai a gindinku yagama yakarewa sauka mari taji akumatunta hagu da dama agigice ta dago fuskanta tana binsa da idanuwa tana zubda kalla ta juyo tana kallonsu daya bayan daya Ga yaranta sun rikece sai kuka sukeyi yace Ashe ke bakida mutunci mahafin nawa kike zagi cike tsiwa tace anzaga kai kasan abunda sukamin ne dazakazo kana marina kan wayan jakuna masu kama da jabaye" ai batayi auni ba tasake jin saukar wani mari yace kimin shiru mara kunyar banza kawai idannuta suka dauki xugi hawaye ne ke zuba wani nabin wani , cikin zafin nama itama tacire hannu ta sinkawa maryam wasu yagwayen maruka da hannayenta biyu kafin kace me dambe ya kauri tsakaninsu da kyar yasamu ya banbare mukifat ya jata kiiiii.... Ya nufi dakin da ita yayi wurgi da ita akangado yanunata da yatsa yana tsareta da ido yace kin ban mamaki mahaifina nawa ne yazama abun zagi awajenki wlh kikiyayeni kuka takeyi har da shesheka wlh sai Allah yasakamin akanku azalumin kawai macuci OK bazakiyi mutane shiru ba ,ta runtse idannuta ganin ya Daga hannusa sama tanajiran taji saukar mari ,shiru yayi yana karewa kyakyawa fuskarta kallo ga sashin yatsunsa kwance a fuskanta wani ja wajen yayi hawaye silalowa a fuskarta shida kansa yaji zafin abunda yamata ji yayi kmr ya jawota ya rungume ,ta furzar da iska ya juya yabar yawa dakin key yakoma falo a tsaye ya tadasu bai tsaya wata wata ba suma ya basu na su mari biyu biyu sannan yanuna masu kofa da hannu oya kowace takama gabanta yan iskan yaran in na sake ganin kafar ku apart dina wlh kukuka da kanku sai na babbala kafarku" bashiri suka kama gabansu suna gunguni yaje yakamo yaranshi rungume tsam ajikinsa yana tarrashinsu sai da ya tabbatar sundawo daidai sannan ya maidasu gun hjy ya dawo yarasa natsuwar sa gani yake bai Kyauta wa Zuciyarsa, ba meyasa meyasa nayi haka yana yarfe hannunshi ....
YOU ARE READING
KAUNACE SILA
Romancekaunace sila all talk about ,neglect of parent, true love, parental obedience.