KAUNACE SILA
💖💖
💗💗💗💗💗AISHA A . BAGUDO (MMN SUDAIS)
Page 45
Idanunta ta zuba mishi tana karewa mai kallo ,mutumin da tasani mai fara'a da sakin fuska mai nunamata tsantsar kulawa da soyayya mai son farincikin ta ,anya shine zaune agabanta ba gizo yake mata ba ,kamar dai yadda tasaba gani ,numfashi ta sauke sanda ta tuna girman laifin da ta aikata gareshi ta cancanci fiyye da abinda tagani akwayar idanunsa "tajin kmr kasa ta tsage tashiga saboda muzantar datayi ,ahalin yanzu tafi bukatar shi fiyye da komai a rayuwarta gumi ne ke tsaftsafo mata takoina ajikinta, gellenta dake shirin barin kafadar ta gyarawa mazsuni ,tsayuwa ne yasoma gagaranta sannu ahankali take bada step har takaraso gabanshi ,yadda take taku haka zuciyarta ke bugawa ,gabadaya bata da wani kuzari a jikinta "tanajin yadda take tsaye a gabanshi shine kashen muzanta a rayuwarta " da sannu ta tattaro natsuwar ta ta dawo da hankalinta gangar jikinta ts hadeye wani miyo mai daci sannan ta daura decumbent din akan makeken table din dake gabanshi "Duk da tarasa da wace kalma zatayi amfani da ita wajen Neman afuwarsa.
Tun tsayuwarta yakejin yadda jikinsa ya sauya ,gabadaya ji yayi iskar dake dakin sunmasa kadan ,kafarshi daya kawai yake jijjigawa akasa karfin hali ne kawai yakeyi wajen sarrafa ma'ajiyar ruhinsa ,har yanxu datake gabanshi tsaye Bai samu damar dagowa ya kalli yanayin datake ciki ba ,iska ya fesar ta bakinshi sannan ya samu damar mikewa ,ta bayanta ya zagayeta yawuce gaban wata durowa yaja ya tsaya yana sauke hadiyar zuciya hannu yasa ya bude yana duduba file din dake ciki har yaci karo da copies din dayake nema zarowa yayi ya juya bakajin motsen komai sai takun takalmansa gawani mayatattacen kamshi dayakewaye kowani sako na hancinta ,yanzu kam takusa da ita yabi kmr zai goge jikinta yanabinta da wani mugun kallo dayasa taji kayan cikinta sun cure wuri daya kallo daya yamata yadauke kansa yakoma mazauninsa ,numfashin ta yanemi ysayawa gabadaya hankalin ta yagama tashi da kallon dataga ya jefeta dashi jitayi bazata juri tsayuwa ba juyawa tayi cikin sanyi jiki tasoma tafiya dai dai da ta daura hannunta kan handle din kofar bata kai Ga murdawa ba ,taji sautin muryarshi ke..........dawo nan jikinta ne yadauki kirma tsoro da firgice yakamata azahirin gaskiya tsoronshi taji yashigeta ahankali ta juyo Amman still hannunta na kan kofar ,ganin yadda yake aiko mata da wasu matsiyatan kallo yasa ta sauke hannunta ,tasoma dawo wa in dayake taku take yi cikin sanyi Amman tajin yadda idanunshi ke yawo ajikinta , zuciyarta kmr zata tarwatse saboda fargaba abinda zai faru wasu file taga yanuna mata yana mata kallon banza yace jiran mekikeyi dabazaki sa hannu Anan ba cikin tsarkewar murya ta furta am sorry Sir ,ita tama manta batayi sign abayan file din ba ,waje ya nuna mata nabaki gud 10 minute kigama,sannan yajingina da kujera yana jujjuyawa dashi , zamatayi ta dau pen ata kusa dashi tasoma sign cikin rawar jiki "kallon yake tundaga kan kwantattacen sumar gashinta har xuwa point noise dinta yana sake ganin tsantsar kamar dasukeyi da sa'id dinshi har Shep din gira da bakinsu iri daya ne yanajin yadda wani Abu ke bin cikin jininshi yana serrulate hannu yasa yana Shafa sumar kanshi ,
Wanna ba mutumin datake mafarkin haduwarsu bane wani daban ne kama sukayi da yanayi Khalid din datasa ba haka yake ba mutun ne mai tsanyi hali da tausayawa ,
nocking din kofar akayi sai da bata lokacin sannan yabada iznin shigowa ,Mr Mathew ne dauke dawasu file ramkwafowa yayi yana gaidashi ya ajiye file yana jiran ASAmishi signe da hannu yana masa alamar yawuce kawai Dan baida kuzarin iya wani sign yanzu ,
Idannushi gamai da gareta ganin har yanzu da minti 15 ta wuce batagama ko rabin aikinta ba tsaki ya ja yana cizan lebenshi na kasa hannunshi yasa yadan bubbuga akan table ya mike yakoma gefen table ya zauna yana fuskanta ta ,Mrs Musa K.I.P.C ba wajen wasa bane idan baki shirya aiki damu ba kina iya ajiye aiki ki kama gabanki Dan bama bukatar shirme yana tsatsareta da Mayan idanunshi dasukagama shanyewa ,da kyar tasamu ta ambaci Sunan Allah a zuciyarta ta dago dara daran idanunta ta zuba cikin nashi Tanason ta tabbatar wa kan shidin ne furta wa yannan zantuttuka masu radadi gare kokarin boye hawayen ta tayi Amman ta kasa shima ita yake kallo ko daya bayajin zai iya tausauya mata soyake yaganta cikin tashin hankali dayafi wanda yake hangowa a eyes dinta tsawon lokacin tana kuka rokon sa tasomayi Dan girman allah kayi hakuri nasan bankyauta katausayamin batun yau nayi nadamar abinda na aikata ba kullun buri nasake haduwa daka da ya'yana cikin matsanancin kuka Tace INA yarana suke Khalid "tabe baki yayi Dan kuka baida meshi ba ko ajikinshi bai samu damar amsa mata ba Cort dinshi yamayar yana gyara xamanshi da kyau ya dau wayoyinshi ya duba agogon dake daure a tsintsiyar hannushi ya ja tsaki inkingama kuka kya iya wuce wa yabar mata office fitarshi dajima ,bayan taci kukanta takoshi ta goge fuskarta da gefen gellenta tamiki cikin sanyin jiki tabar office din...
Muje zuwa
YOU ARE READING
KAUNACE SILA
Romancekaunace sila all talk about ,neglect of parent, true love, parental obedience.