✨Najmah✨10 (Asalinsu)

128 10 0
                                        

NAJMAH
STORY, WRITTEN BY
DIELAIBRAHIM

______________________________________

Alh.Muhammad Adam Misau
Hafanfan garin Misau ne cikin jihar bauchi...

Iyayen shi shi kadai suka haifa...
Mahaifinshi ya tsaya mashi sosai don ganin Muhammad ya samu ilimin addini da islamiya.

Mahaifiyar shi tun da ta haife shi Bata kara samun ciki ba......sai da Muhammad yayi shekara ashirin da bakwai......

Ranar da tafa ra naquda aranar Allah ya amshi abinshi da ita da jaririyar.....

Muhammad yayi bakin ciki da rasuwar mahaifiyar shi...gashi mahaifin shi ya kasa hakura da ita
Hakan yasa Shima Allah ya dauki ranshi  wata biyar bayan ya tashi daga ciwon dayayi tun mutuwar matarshi

Mahaifinshi bashi da Yan uwa Duk sun rasu.... shi yasa Muhammad
Ya koma KD da xama don dama a Zaria yayi karatun shi

Mamie .su mazauna kaduna ne...Asalin su fulanin Nijar ne....
Mahaifinta ya na zaune a KD shida mahaifiyarta
Sun hadu da Alh.Muh'd ne
A wani bikin abokinshi da akayi
acikin unguwar rimi

Awannan lokacin ne Abba yaga Mamie Kuma ya yaba da halayenta
Daya ke akwai rabo a tsakaninsu
Sai Allah yasa ya aureta.

Bayan yayi auren ne ya samu aiki yayi anfani da gadon shi ya siya gida ya fara xama a unguwan rimi anan suka hadu da Alh.Ibrahim Salis ,Makota
ne Wanda sukayi xama na mutunci kamar Yan uwa

A tare Mamie suke haihuwa da Ammie.....har sukai kusan she kara Ashirin da Hudu atare kafin
Daddy ya samu aiki a u.s suka koma

Alh.Muhammad Adam baiji dadin rabuwa da aminin kwarai ba kaman Daddy
Don haka bayan rabuwar su
Ya tashi a unguwan rimi yasai babban gida a Malali ya koma da iya lan shi.

Mamie alokacin su uku mahaifiyar ta ta haifa
Mamie (Sa'adat) ita ce babba sai
Khadija wacce Allah yai mata rasuwa bayan tayi aure da shekara biyu.
Sannan Ikleemah wacce take  Sudan ayanxu da xama sbd mijin Dan Sudan ne.

..............,...............,.

Present time👇

Mamie Ni wlhy ki ce ma Minal baxan saka wannan rigar ba ......ya mutun xa ana takura mashi ne.....

Naj wlhy sai kin sa.......cewar ilham
Ita ko Minal ko tanka ta Bata yi ba abinta

Cen dai taga Mamie Tai Shuru ta kyaleta....sai ta janyo rigar
Ta tsaya kallon Gown din, doguwa ce peach🍑 color Mai dogon hannu
Gaskia ko ita sai da ta yaba rigar

Ta dauka ta tafi bayi ta sanya.......

Har makeup a bayi ta tsaya tayi gata dama gwanar iya makeup
Tai Arab rolling
Sai ta sanya cover peach color Mai dauke da design na stone

Ta fito daga bayin
Ta tsaya kaman wata Mai laifi

Minal, Mamie ,ilham Duk sai da suka tashi don su kansu basu San Najmah tana da wannan kyanba

Hakika Najmah tana son make-up Amma Bata yi ma kanta idan xata fita
Sai dai tayi agida ta wanke
Koh Tai ma Minal
Da kawayenta

BETWEEN US ✔Where stories live. Discover now