✨ Najmah✨27 Gushewar Farin Cikin Rayuwar Najmah

84 5 0
                                    

Najmah
Story written by
DielaIbrahim ✍️

************

Kasa jiran farfadowanta yayi Saboda ya karanta same text din daya gani a wayanta
Yayi mamaki shin waye yake kokarin tona asirin da tun tuni rufe yake Shin waye wannan Wanda yake son ruguza farincikin iyalan gidan mu

Lallai ana Shirin ballo masu ruwa kuwa
Indai Naj tasan cewa ita ba Yar gidan bace

To mexai faru kenan...????
Haka yai ta tunani acikin ranshi
Doctor ya samu
yayi masa bayanin xai koma da ita gida inyaso xasu Kira Family doctor dinsu ya dubata gobe.....idan babu wata matsala

Doctor yaga rashin hakuri ga yaron Amma Bai matsaba ya ce mashi ba komai yanda kagani
Kaje da ita....kamar yadda na tabbatar maka babu abinda ke damun ta illah gangar jikin ta dayasamu want bakon Al'amari
Wanda a zahiri jikin Bai shirya dauka ba ......toh sai fa kin kula don irin patient dinnan suna da wuyan sha'ani.....tare da Bata magungunan ta akan lokaci.

To doctor inshallah mun gode sosai .

Nan ya koma da ita gida Misalin karfe Sha daya da rabi

Babu Wanda baiyi bacci ba don Haka ya nufi dakin ta ya kwantar da ita....sannan ya fita
Kai tsaye part din Mamie ya nufa
Don azahirin gaskia dole ya tada ta Susan abinyi sbd gobe Basu San wani amsa xasu bawa Najmah ba idan ta tambaye su.

Knocking dakin zaiyi sai ya tarar da kofan a bude take Kuma wutan dakinnata a kunne yake......Tafiya yaji daga bayanshi Yana waigawa yaga Mamie ce

Fayrouz lafia Naga ka dawo da Najmah kamar Bata cikin hayyacinta...shin meya sameta ne?

Mamie...uhm uhmm....Nan fa ya fara in inar dole Wanda yasa Mamie daka Masa tsawa

Meke faruwa ne Ina tambayan ka?

Da kyar ya iya daurewa ya sanar da ita abinda ya faru........ya daura da cewa Mamie a halin yanxu Najmah na iya farkawa kowani time sannan dole ta tambaye mu Mamie shin me xamu ce mata

Girgiza Kai Mamie tayi sannan tace wannan ba aikin kowa bane sai Ikleemah.....domin ita taimin alkhawarin tona asirin mu ga Najmah
Amma ka kwantar da hankalinka kaje ka kwanta Fayrouz
Najmah Yar halak ce tasan abinda ya Dace don Haka zamu iya shawo matsala da izinin ubanhiji.kaji
To Mamie sai da safe

..........
***************

Misalin karfe 10 na safe Naj ta farka Nan abubuwa suka dawo Mata sabo......ji take tamkar ana kida a kanta don tsabagen ciwon da yake Mata......tashi tayi ta fita xuwa parlor

Anan ta tarar da su

Kujera taja kusa da Mamie ta zauna

Sai data gaishe dasu, taci dankali kadan ta kurbi tea sannan ta tashi xata bar wajan

Mamie ta katse ta Naj yata dawo Mana ki karasa cin abincin

Saurin juyowa tayi ta kalli Mamie

Tana matukar Jin nauyin Mamie Kuma tana girmamawa ta.....son da Mamie take nuna Mata wani zubin ma takan ce yayi yawa kamar ita kadai Mamie ta haifa
Ko rashin lafia take Mamie ta dinga safa da marwa kenan har sai taga ta samu lafia.....ko Minal takan ce ba'a shiga tsakanin Naj da Mamie domin soyayyar Naj daban yake Dana sauran yayanta

Amma kuma Taya xa'ai Rana tsaka ace ba Mamie bace mahaifiyar ta

To shin Anya wannan mgnr karbabbuwa ce acikin xuciyarta kuwa

Inaaaaa gaskia wannan maganar karyace babu yanda za'ai ace ba Abba da Mamie bane suka haife ta......Wani irin Kara ta saki Wanda Duk sai da ta tsorata su

Kukane ya kwace Mata tayi saurin xuwa wajan Mamie ta rungumeta tsam tare dacewa

Mamie meyasa suke son su raba mu.....meyasa xasu ce bake kika haifeni ba......Anya sun San irin son da kike min kuwa
Mamie so suke su hadamu fada Koh.....ninasani dama shiyasa zuciyata taking yadda da cewa bani da Asali....bayan kune iyayena....bayan ku ban taba sanin wasu ba.....
Ta dago kanta ta kalli Mamie tace
Mamie ki kyaryata zancen su ....karki Bari su cutar Dani don Allah Mamie nah
Ta fada tana Mai tsananin kuka Wanda dole ne ta baka tausayi sosai.

Mamie tace da Fahad ya ja Suhaila da Khaly zuwa ciki.

Sai ya kasance Abba ne da Fayrouz suka rage

Mamie ta ja Naj xuwa daki tana ta lallashin ta har bacci ya dauke ta

Kafin ta fito ta samu Abba
A parlor tace Abba ya samuyi nee
Na fara karaya fah

Kiyi hakuri Mamie Kuma ki cigaba da addu'a

Zuwa Nan da 1week mugani

To Abba Allah ya kaimu....

Ameen

************
A week later

Yau da kwarinta ta tashi...don Haka ta shirye zata shago
Saboda kwanan ana ta kiranta ana bukatan makeup Kuma wasu daga ciki ita suke so taimasu.

Bayan ta Isa shagone
Tayiwa akallah mutane biyar kafin taxo kan wata Mata da take ganin kaman ta San ta.....ita Kam kaman ta taba ganin matar Nan...
Amma ta rasa a Ina ta ganta

Saloon xa'ai mata..,...ta gaji da kallon ta da matar keyi don Haka ta umarci sakeena data you Mata saloon din

Matar Taki Wai dole Najmah ce xatai Mata

Hakanan Naj tayi tagama gyara Mata kenan
Taji Matar zata fita bayan ta biya kudin tace Najmah Yar Khadija
Ungo wannan hoton mahaifiyar ki ce inbaki yadda ba Kuma kije gida ki tambayi Mamie

Bata jira amsan Naj ba tayi waje abinta

Hoton ta tsira wa idanuwanta tana kallo........gani take yi kaman ta taba mafarkin matar

Key din motar ta ta dauka ta nufi gida.

Tana shi ga ta zube a gaban Mamie tana kuka tace

Mamie shin wace ce wannan matar
Da gaske ita ta haife Ni?

Mamie da gaban ta tuni ya yanke ya fadi bayan tayi artabo da Kuma tozali da hoton qanwarta khadeeja mace mafi soyuwa a cikin ranta.....

Dai dai lokacin Abba da Fayrouz suka shigo sun dawo daga sallan magrib
Sukayi kicibus da abinda yake faruwa

Abba yace ke Najmah wake Baki wainnan bayanan

Nan Naj ta kwashe Duk yanda suka yi da matar ta Fadi masu

Shuru sukayi na kusan minti goma babu Mai cewa uffan a cikin su.

Abba, Mamie kunyi Shuru don Allah kufadi min
Ina son sanin gaskiayar Al'amari

Abba yau da safe anmin text Wai bani da Asali ba'asan mahaifi na ba......Abba atunani Nima yarka ce Kuma jininka
Mamie na dauka ke kika zugunna kika haife ni.....sannan ni da Minal dama ba twins bane Mamie?

Abba na roqequ ki Fadi min gaskiyar Al'amari
Kafin zuciyata ta buga......

************************

DielaIbrahim ✍️
Vote and Share
Pls 🙏



BETWEEN US ✔Where stories live. Discover now