✨ Najmah✨37

91 8 0
                                        

Najmah
Story written by
DielaIbrahim ✍️

(37)

****************

Ikleemah ta cigaba da cewa Mamie
Har Nijar nabi Abba lokacin daxai kaiwa khadeeja sako
Nayi magiya Amma ya ki saurare na.....sai nayi kakarin sa mashi kayan maye a abin cin shi don na samu yanda nake so

Tabbas yaci abinci Wanda daga restaurant din dayayi ordering
Aka kawo Masa Amma sai da na biyasu kudi kafin suka xuba Masa a juice

Sai dai Kash khadeeja ranar ita ta taimakeshi ganin irin halin dayashiga na maye
Ban samu nasara ba saboda ta dauko likita da Nurse Wanda su suka tsare shi har safiya

Nayi matukar bakinciki da hakan shiyasa na tsani khadeeja na tsani jininta

Uhmmmm Mamie Tai murmushi tace bamu da hakki akanki shiyasa kika kasa cin galaba akanmu Kuma dayardar Allah sai Kinga sakayyar abinda kikayi
Maxa ki fitan min daga gida Kuma Ina horonki da karki sake shigo min gida

Mamie da Bata fada Amma har waje ta fitar da ita sannan tasa masu gadi da karsu Kara Bari ta shigo gidannan

Mamie takoma Taki ta samu Abba tana kuka tana bakin ciki da irin rayuwar da ikleemah ta daukan wa kanta tun tana karama
Abba yaita lallashinta
Yace Mamien Yara kin kasance mace mai hakuri
Mamie Hakika idan mutun yasamu mace irinki to babu abinda xai yi saidai yai ta godiya wa ubangiji

Kinzama uwa Kuma uba agareni sannan kin haifamin ya'ya Kuma kika musu tarbiya Mai kyau

Babu abinda xan iya cewa lokacin da ikleemah tai min sharri acikin gidana, bani son hada ki  da yar'uwarki
Shiyasa ranar da tace nine mahaifin Najmah
Kawai nai Mata Shuru don ban shirya fallasa sirrin ta ba
Amma Alhamdulillah tunda yanxu ta wankeni a wajen mamata mafi soyuwa acikin Raina

Mamie Tai murmushi tace Allah ya qara maka lafiya Abban Yara
I'will remain loyal sir till death

Abba yai Shuru Yana kallon Mamie

Hakika Mamie ta dabance acikin mutane da Kuma mata

..............

Da murnar su suka sauka a qasa Mai tsarki
Sun Isa masaukin su
Kowa ya nufi dakin da yake so

Fayrouz, Sadeeq da Shariff
Suna ta shawarwari akan yadda xasu bullo wa al'amarin

Sunan Wanda ya bani bayanai akan Marshal
Captain-Ibrahim Kuma
Suna aiki nee a qarqashin Marshal

Kuma yace a gobe Marshal xai iso Saudi,don Haka shi xamu bi
Saboda shine tiket dinmu na ganin Marshal
Ba gobe zamu ganshi ba
Ayanda plan dinmu yake dole mu jira nadan kwana biyu

Ina bazai yuwu ba idan yaxo yabar qasar fah
Cewar Najmah da take gefe tana sauraransu hankali a tashe

Su ka kalli Fayrouz
Alamar shi xai kwantar mata da hankali

Fayrouz ya tashi ya riko Mata hannu sannan suka Dan fita waje ta corridor suka tsaya
Yace mi Dil

Calm down kinji
Haduwa da  Marshal ba karamin Abu bane ayanda yake da mukaminnan
Kinsan sojoji in mukaje Kai tsaye wlhy sai sun illata mu
So su suna son respect Kuma suna son mutun yabi order
Shiyasa zamubi komai ahankali kinji

Toh Yaya nagode
Toyi dariya Mana

Murmushi kadan tayi sannan suka koma daki

Ya xauna suka cigaba da shawara ita Kuma ta wuce daki

Ta samu su Minal suna kallo
Guys kallo kukeyi ahh Kuna shanawa

Ilham tace series nee wlhy
Yaya dai sun game plan din

Not yet

Ohk tih shikenan

Itama xaunawa tayi tana kallon Amma hankalinta Yana wajan mahaifinta

.............

Bayan kwana Daya Naj da Ilham+ Minal suka dauki mota suka fita
Yawan shakawa sunje Masallaci Naj tayi addu'a sosai Wanda sun dade suna zagayawa

Yamma likis suka Kama hanyan dawowa gida
Amma Naj taga ana saida wani abin wasan Yara Wanda su Suhaila da khaleel suna so
Abba ya taba siya masu da yaxo makka
Suka lalata Ya Fayrouz so nawa Yana siya su Kuma suyi ta kyauta dashi Wai Yara suna so

Minal kuntsaya insiya ma su khaleel wancen abin tsaraba

Minal tace abinda suke kyautar wa eh sai mu siya da yawa yanda xasu bada tsaraba Suma

To yanxu bamu fito da kudi ba
Ki tambaya nawa ne sai gobe muxo mu siya

Ohk kawai tace ta fita

Ta tambaya tana juyowa kenan ta hango Motocin sojoji suna layi daga dayan bangare want titi
Su Minal baxasu I ganin su ba

Tsayawa tayi tana kallon inda Motocin xasu
Cikin ranta tace kila ma wannan nee Marshal din
Bata gama tunani ba sai taga an bude Masa kofa ya fito
Taku Daya taga ana binshi abaya

Bata da wani nisa dashi don haka tafara tafiya tana son zuwa wajansu
Cen Kuma taga suna Mata nisa
Dabara ta fado Mata

Kawai tayi ihu

Daddy da karfinta

Tsayawa yayi cak Jin Kiran
Dukda yasan badashi akeba
Yace da escort dinsa
Bakuji anyi Kira ba

Zata sakeyin ihun nee wata mota taxo ta banke ta tuni Naj Tai sama ta fado

Ilham ta fito a mota ganin Naj ta Dade waigawan da xatayi taga mota tayi sama da Naj
Ihu tayi sannan ta Kira Minal
Suka nufi wajan da gudu
Jini nee keta xuba
Suka dauke ta sai asibiti

**********

DielaIbrahim ✍️
Vote and Share
Please

BETWEEN US ✔Where stories live. Discover now