✨Najmah✨24 (Biki)

110 11 0
                                        

Najmah
Story written by
DielaIbrahim ✍️

(24)
Bissimillah

***********


6days later

Iyalan gidan Alh.Muhammad Adam Misau ne zaune a katafaren falon gidansu..... Fuskokinsu kawai zaka kalla ka gano zallan farin cikin da iyalan suke ciki....kasancewarta yau babbar sallah.....shiyasa suke ta wasa da raha a tsakanin su.

Fayrouz na hango zaune tsakiyan Mamie da Naj, Minal Kuma na saman kujeran da suke zaune tana Taya su wasan ga su Suhaila da khaleel suna wasan doki akan Fahad.

Kwatsam text ya shigo wayar Naj
Number ba suna Kuma a iya sanin ta ba'a taba Kiran ta da wannan layin ba Kuma gashi an Mata text.....tsaki tayi kawai ta aje wayar agefenta batareda ta bude ba...... Fayrouz ya kula da ita,yace little me ya faru?

AhAh babu komai Yaya ta bashi amsa dauke da murmushi a fuskanta
Shima ya mayar Mata kwatan kwacin murmushin da tai Masa sannan suka cigaba da hiran su.


3weeks later

************

Dama ai na Fadi maki yussy aikin malaminnan jah yakeyi
Yanxu bagashi ba saura sati guda chur ki zama matar Abubakar Sadeeq Salis

Wata irin dariya tayi wacce Bata cikin dariyan da musulunci ya aminta dashi( kunsan ance yawan dariya Yana rage imani)

I knew it Salma na rigada na sani cewa Sadeeq bayada wata matar aure sai ni kadai......ke bama wannan ba kinsan da cewa ya dawo Amma haryanxu Bai sa kafarsa a gidannan nan ba

Rabu dashi zai shiga hannu ne aee.....

Amma Salma Ina tsoro kada na auri gangar jikin shi,Ruhin shi ya kasance baya tare dani

Haba yussy bani so kina karaya ki auri gangar jikin inyaso daga baya xamu samu Ruhin ko a Ina yake kinji share hawayenki....kinji Amaryar Sadeeq

Wani amintaccecen murmushi ne ya subuce Mata....... She can't wait to be his bride.

***********

Yan matan ne su uku suka fito daga shagon telor dinsu

Alhamdulillah yanxu Kam mun gama duk wani shirye shirye na bride da Kuma bridemaid
Cewar Minal

Eh fahhhh Minal ya Sadeeq fah......sai Kuma Tai Shuru ta kasa mgn ilham ce.

Ya Sadeeq meyasa meshi Kuma
Aa babu komi.

Najmah tace Minal da alamu kaman ya Sadeeq bai damu da auran da xaiyi ba don ko shirye2 bayayi..

Kuma kun gano kenan...... Need wlhy naso ace Minal zai aura
Kika ki bamu hadin Kai
Haba Minal miye aibun ya Sadeeq, miye laifin, shin Yana da wani mugun Hali ne?
Nagafah shi yace Yana sonki Kuma dabgaske yake yi nasan ya Sadeeq wlhy baya was da abinda yake so.....To meyasa kika tsane shi ?

Gaskiya ne Minal Duk da bakin Alkalami ya bushe don saura sati guda a daura Masa aure da Yusrah, muna son muji ta bakinki

Xuwa wannan lokacin Hawayen da take boye wa tun sanda aka say Masa Rana da Yusrah sune suka fara ambaliya a fuskanta
Kuka ne ya kwace Mata
Yi takeyi da karfin ta don huce takai ci.........Sai da tayi Mai isarta cikinsu babu Wanda yace tayi Shuru
Sannna ta fara mgn ahankali

Bana sonshi me kuke son ji bayan wannan mgn na roke ku kada ki sake min mgn ya Sadeeq don Allah don son Annabi.🙏
Takai karshen mgn lokacin sun iso kofar gidan su Ilham

Don Haka ta Riga kowa sauka a motar Bata Bari Naj ta shiga da motar ciki ba ta fita...ji tayi bazata iya shiga cikin gidan ba don Haka hanyan titi tabi don komawa gdn su.......Najmah ce hankalinta ya tashi Tai saurin sauka a motar tabi bayanta tana Mata mgn

Naj karki damu kuje xanje gida wajan Mamie ne
To muje tare sai mu dawo
Aa ki koma don Allah xan dawo bada Dade wa ba

Are you sure?

Yeah!Sure! ta Bata amsa
Ohk to sai kin dawo.

Naj ta koma taima ilham bayani sannan suka shiga gidan.

Yamma likis ana ta yiwa Amarya dilka da gyaran jiki Wanda tun ana saura wata daya aka fara shi ....... Fita inba ta mota ba to Bata xuwa ko ina don haka nr Ammie tace daga yau Bata Kara fita.
Najmah ta gaji da jiran Minal don Haka tayi ma ilham da Ammie sallama ta tafi gida.

Event daya zasuyi don ilham take Bata son yawan event din dakeyi KAMU kawai xasuyi inyaso ranar biki sai suyi Dinner bayan ankaita
*********

6days later

Ranar Friday
Shirye shirye sukeyi don yau suna da event KAMU da karfe Hudu

Yanxu misalin karfe 3 ne na rana Amarya ake shirya wa cikin shiga ta Alfarma bawani Mai hayaniya ba (Shigar Atamfah Riga da zani aka lullube ta da babban mayafi na atamfah
Gaskia tayi kyau sosai)

Sai da suka gama shirya ta kafin Suma suka shirya Hudu da rabi Motoci xuka xo aka nufin wajen KAMU

Babban Hall ne ga decorations din yayi kyau Traditional decorations Kuma ko wacce daban daban akai masu... Wanda makil yake da mutane
Event din anyi shine sbd Ilham da Sadeeq to har aka kusan tashi babu shi ba alamarshi....Haka Amarya Yusrah tayi ta zama ita kadai ranta inyayi dubu ya baci.

Antashi misalin karfe Tara kowa yayi gida

Suna zaune adaki Minal tace yau Naga soyayyah karara a ida nuwan ku wlhy

Ilham Tai dariya tace Tabbas ya Shariff Yana Sona Amma ban Isa na kiyasta irin son da yake min ba....Don acikin Kashi dari na soyayyar mu zan iya cewa ya kwashe kaso 70 Ni Kuma Ina da 30.......

Hmmmm masoyin asali kenan cewan Najmah
Allah kabamu masu son Haka
Ameen Wanda ma ya fishi cewar Minal

Dariya sukayi gaba dayansu.....suna ta hira har kusan karfe 12 kafin suka kwanta.

*******

Yau Asabar wasu sukan ce Sati
Kuma yauce ranar daurin auren Ilham Salis da Ahmed Imran tare da Abubakar Sadeeq Salis da Yusrah Abdulhakeem

Bari mu leka sashin Sadeeq
😁

Zaune yake shida Fayrouz..... Fayrouz na Kara jaddada Masa plan din tare da bashi kwarin gwiwar samon nasara a plan din nasu nagode Dan uwa shiyasa nake sonka a kusa Dani ko da yaushe.

Hmmmm it's ohk you re more than a friend to me Sadeeq.

Shin wannan wani plan nee
🤔🤔🤔

Kubiyoni kusha labari

*******

DielaIbrahim ✍️
😜 😜

Comment are always welcome

Vote and Share
Pls🙏





BETWEEN US ✔Where stories live. Discover now