Yau kwanan su Naj uku a abuja.
Safiyar yau Minal ce xaune a parlon tsohuwa
Karatun alkur'ani takeyi tun da tayi sahoor take sallah
Don taimaka ma mutumin da tayi mafarki Yana neman taimako awajn ta....tabbas mutumin da ta taba gani a mafarkin ta ne yanxu a karo na uku kenan tana mafarkinshi
Toh Amma meyasa Bata taba ganin fuskan shi ba
Sai dai tana ganin shi da tare da mutane Kuma sanye cikin navy blue uniform daga gani
Uniform din akinshi ne......
Gashi mafarkin nata na jiya ya tsorata ta...."Tana tsaye ne abakin kofar Hospital din da taje, taga wasu tawagar mutane kaman yanda ta Saba ganinsu Koda yaushe in xatayi mafarkinshi
Sun dauko wani mutun wanda daga ganishi Bai cikin haiyyaci shi....sunfi cikin asibitin........Amma direct inda take suka tsayaKallon ta daya daga cikinsu yayi yace madam....oga yace ki taimake shi da addu'a
Don Allah
Ya fada Mana idan mun ganki mu fadi maki cewa
Ke kadai ce xaki iya cireshi a tarkon dake Shirin kamashi.... Shine fah tun da ta farka karfe biyu take ta nazarin mafarkin..Shine take ta yanke shawaran taimaka Masa da addu'a.""
Karatun ta cigaba dayi har xuwa karfe takwas na safe....granny da takai akalla awa daya xaune
Awajn ta na saura ran zazzakar muryar ta, takara zunduma cikin Jin sautin da haruffan yanda suke fita yanda ya dace.Tana gama wa tayi addu'o'inta sannan ta tashi ji tayi ance MashaAllah....Namshi dama haka kika iya karatun alkur'ani
Bude baki Minal tayi tace haba granny Namcy fah ake cewa ba Namshi ba
Yooo ni Ina ruwa na ai ban iya fadi ba....yaushe xaki fara koya min kafin ki wuce...ta fada tana washe baki....... 😁
Duk sanda kike so yhur highness
Minal ta fada tana russuna Kai alamar girmamawaZare idanu granny tayi tace....waya baki izinin fadin wannan sunnan...
Minal tace Alamar girmamawa ce ai....Kuma kin cancanci sunan ai
To Ni dai miji na dan lele na kadai yake Kira na da wannan sunnan( nufinta Sadiq kadai ke Kiran sunan)
Minal tayi kaman Bata gane me granny ke nufi ba tace Ahhh su kakus an tuno soyayyar tsoho an tabo maki inda yake maki kaikayi
Kallon ta granny keyi tana son dago inda mgn Minal ya dosa
Cen tace soyayyan tsoho hmmmmmmm......Allah dai ya jikanshi da rahama habibina kin tunamin rayuwarmu da mijina tana mgn kaman Mai Shirin yin kuka....
Lahhhhhhhhhhh Allah sarki granny sorry ban fada don in saki kuka ba....
Barni nayi Yan nan....wlhy mutuwa tamin yankan qauna
Ki barni don Allah
Kuka granny ta faara wi wi wiIna hankalin minal in yayi Dubu ya tashi...tayi daki da gudu tana kwala masu Kira
Ku fito pls ku tayani bama granny hakuri kuka take wlhy
Ta fada masu hankali tasheMeya same ta ne?
Bata tsaya zayyana masu ba tace ku biyoni pls
Duk suka fito.....suka iske granny tana ta faman rusa kuka
Nan fa suka fara Bata hakuri

YOU ARE READING
BETWEEN US ✔
Non-FictionStory of three sisters that made alot of painful sacrifices to each other Najmah who happens to be the star of the story, Minal ( Najmah's partner) And Ilham the honest friend