✨Najmah✨30 Present Time

65 9 0
                                    

Najmah
Story written by
DielaIbrahim ✍️

Present Time (30)

**************

Mamie ta share hawayen idanuwanta ta kalli Najmah wacce babu abinda takeyi ita da Minal sai kuka

Harta su Fahad xuwa wannan lokacin kuka sukeyi

Awannan halin nee sukaji sallama ba kowa bane sai Ikleemah

Ta karaso parlorn cike da gadara da Kuma kasaita sannan ta kalli Abba Murmushi tayi wanda kallo daya zaka gane murmushin mugunta ne.....tsahon dakika goma kafin ta koma kallon ta ga Mamie tace
Kina son sanin waye uban Najmah?

Dasauri kowa ya dago Ido ya kalle ta Banda Abba da durkusar da kanshi
Tunanin Abubuwan dasuka wakana a shekarun baya yakeyi
Dama ta fada Masa cewa sai ta ruguza farin cikin shi matukar Bai amince dawani buqata nata ba......

Ikleemah ta katse mashi tunanin shi da cewa

Najmah Bata da wani Uba face Alh.Muhammad Adam Misau
Ma'ana shine Biological Father dinta....idan Kuma Kuna da ja
To ku tambaye shi zai Fadi maku komai........tana fadin Haka tayi hanyar waje abinta

Mamie da Jin maganganun ikleemah yasa ta kasa tashi daga durkushewar datayi

Fayrouz ne ya bita waje dasaurinsa....Amma kafin yakai kofar fita Abba ya dakatar dashi

Abba yaqasa furta ko kalma daya ga family nashi baisan ta Ina xai fara ba....... ikleemah ta ruguza komai ayayinda ta furta maganar ba yanda ta Dace ba, Daki kawai ya wuce ranshi Yana Mai matukar suya da Kona.

Mamie ta kalli yayanta babu abinda suke inba kuka ba

Ta umarci kowa daya nufi dakin barcin su ..sannan suyi Shuru sudena kukan hakannan

Dakyar Mamie ta iya tashi ta nufi dakin Abba......tana Shiga ta ganshi gaban mirror Yana zubda hawaye

Wannan shine karo na uku da Abba ya taba zubda hawaye a shekarun da suka dauka Bata taba ganin yayi kuka ba
Sai dai idan wani gagarumin Abu nee ya same shi.

Zama tayi kusa dashi tare da dafa kafadan shi

Abban Yara Nasan maganganun da ikleemah ta fada ba gaskia bane
Saboda na yadda dakai baxaka aikata abinda zai cutar Dani ba dakai da Kuma yayanka
Nasan so take ta Shiga tsakanin mu, bazan taba manta wa ba
Ikleemah taso ka abaya
Sai dai bansan karashen labarin ba Kuma ban tambaye ka ba....sbd bani son hankali na ya tashi....Nayi Shuru nee ba donbani son Jin ba'asi ba sai don Ina son kwanciyar hankali

Ta Dan tsagaita ta share hawayenta sannan ta dora da cewa zaka iya bani labari
Ina saurarenka yanxu

Mamie bazaiyu in Baki lbr yanxu ba sai dai Ina Mai tabbatar maki abin yaxo ne ajuye bani bane mahaifin Najmah

Wannan kullaliya ce ikleemah take son hadawa tsakani na da family na.....sbd ta cimma burin ta .....Mamie ke kinsan bazan taba aikata irin wannan mummunan laifin ba Bayan Ina da ke Kuma Ina tsoron ubangiji na ranar sakamako.......Ina so kiyi yaki da zuciyar ki ki Kori shaytan kada ya xaman Mana matsala a rayuwar mu.

Kukane ya kwace wa Mamie
Abba ya rungumeta Yana lallashinta

*************

Bangaren Najmah suna tare da Minal
Naj ta kalli Minal take me matar Nan take nufi
Tana nufin tace Abba nee mahaifi na.....ga dukkan alamu Mamie Bata San da wanna batu ba......Kuma a iyaa sanina Abba bazai taba aikata laifi makamanciyar wannan ba

Zanzo ace Abba shine mahaifina Amma ta hanya Mai kyau Bata badacciyar hanya ba ....Minal me xaki ce game da hakan?

Minal da kanta ya rigada ya kulle Bata iya gane komai a wannan lokacin.......zare idanuwa tayi ta furta Ilham yes yes
Naj pass me ur phone please!
Hurry up

Naj ta mika Mata wayar tayi dialing number Ilham
Hello! Ilham
We need u now, can you pls come over....yes at our family house.
Ohk bye

Minal Wai me kike Shirin yi ne?

Just wait Ilham to show up....
...............
Minti 40 ilham tayi kafin ta iso gidan Kai tsaye dakin su ta nufa
Zaune ta same su kowa yai jugum Alamar damuwa na cin junansu.......meke faruwa ne girls? Ta tambaya

Ilham samu waje ki zauna pls yanxu xakiji komai

Ilham ta nemi gu ta zauna Ina jinku tohm

Minal ce ta Bata labarin abinda ke faruwa tun daga farko har karshe ,.....kin daiji Koh ilham yanzu taimakon ki muke nema

Taimako wani iri Kuma Minal?

Zaki Mana DNA test....Dani da Naj da Kuma Abba if possible harda Mamie but Naj da Abba shine yafi zama important yanxu

Minal this is bull shit ......kina so ace bamu yadda da Abba bane cewar Najmah tana kuka

Minal Tai saurin tashi ta nufi inda Naj take ta Kama hannunta
Even do we are not twins....ta dan goge hawayenta sannan ta cigaba....Baxamu canja son da muke ma juna ba Don't forget we still blood sisters and the love is still there.......suka rungume juna suna kuka
Minal tace ki bani hadin Kai
Bawai bamu yadda da Abba bane Nothing like that Ina sone muyi clearing any doubting akan wannan issue din

Ilham tace Ina tare daku sisters
I'll make sure that nayi komai yanda ya kamata

Allah ya taimake mu
Ameen

*******************

DielaIbrahim ✍️
Vote and Share
Pls 🙏


BETWEEN US ✔Where stories live. Discover now