✨Najmah ✨ 36

84 8 0
                                    

Najmah
Story written by
DielaIbrahim ✍️

(36)

*****************

Ta kalle shi tace to Yaya meyasa baka barin kowa ya dauke Ni
Saboda soyayyah little tun bansan wata kalan soyayah nake maki ba har naxo na gane

Little kinsan wani Abu Ni ke maki wanka har kika Kai 4years Amma fa a idon Mamie ban taba maki wanka ni kadai ba
Dayake keda Minal nee
To Mamie sai ta tsaya na maki tukun.....daga baya Mamie tace na Dena Kuma mgn ta zauna

Murmushi yayi sannan ya cigaba
Little tun taso warmu su Abba suka gane Ina sonki nee da gaske
Azahiri Basu so kigane Basu suka haife ki ba sbd tsananin son da suke maki shiyasa suka tura ni karatu Riyadh kina 10years lokacin bansake ganin ki ba sai wannan dawowan da nayi.....

Tayi murmushi tace Yaya ka tuna wata Yar tsohuwa gidan dayake kallon namu
Wacce take bamu Nono kindirmo

Kullin Mamie sai ta Hana mu xuwa Amma sai mu saci hanya muje mu karbo
Minal Kuma inta ganmu taje takai gulma wa Mamie
Hahhhhhh nikuma na make Mata baki

Yeahhh Kuma Duk sanda ka make Mata baki Nike kuka ita Bata kuka

Hahahhah Rayuwa kenan

Minal dashan duka Najmah da kuka......

Tace Yaya an Kira Magrib muje kayi sallah sai mu tafi gida
Kefah
Uhmm Ni sai naje gida

Kin tabbata? Eh tabashi ansa
Ohk toh Mrs Fayrouz babu mishkila tunda kince Haka
Tarakashi har xuwa wani matsaikaicin masallaci tajirashi acikin mota
Shi Kuma Yana fita yace da ita
Little banfah yadda kina sallah ba....Wai Ni Zaki ma wayo kin manta naji sanda kike cewa ilham yau fashi kike shiyasa kikasa wannan kayan

Bude Baki tayi Alamar mamaki daga bisani Kuma ta kulle fuskanta Alamar kunya
Yayi dariya abinshi sannan ya wuce.

.................

Bayan kwàna biyar nee

Sadeeq ya kirawo dukkansu parlor

Fayrouz yace oga angama Binciken nee

Sadeeq yai gyaran murya sannan yace
Nagama Bincike akan Marshal
Results dinmu ya nuna Satin daya wuce Marshal Yana Chad
What !!!

Suka fada dukkansu

Sadeeq yace yes Amma yanxu an bani gabadaya bayanan kasar da yake Wanda ya bani bayanin yace na Bari Marshal Yana aiwatar da wani aiki nee Mai muhimmanci da zaran ya gama zai koma Riyadh da karshen wata lokacin ganin iyayenshi kenan......so yanxu yau kwanan wata 10 muna da sauran kwana 20 kenan
Acikin kwana 20 din xamu je Saudi gaba dayanmu this is our third plan

Then daga lokacin sai mu dauki forth plan don a Saudi xamu samu Daman ganinshi
Cikin danginshi
Ina fatan Allah yasa mu tsaya a forth plan din din
Kowa ya Amsa da Ameen

Naj ta fita waje
Tsahon minti biyar Sai ga Fayrouz ya fito nemanta
Waige waige yake tayi cen ya hango ta tsaye tana kallon ruwa Yana sauka daga kan Dutse
Mgn yake ta Mata Amma Ina hankalinta baya wajan ma

Cen ya taba hannun ta firgigit tayi ta kalle shi
Ohhhhhh Yaya yaushe ka fito

Tun daxu tunanin me kikeyi Haka Naj

Ta rike mashi hannu yaya kana ganin zamu samu ganin shi kuwa
Am scared Kar mu rasa shi kuma
Inshallah little xamu ganshi
Kidena damuwa kinji
Toh ta gyada Kai.
Sannan suka koma ciki

...................

15 days later

Misalin karfe Bakwai da rabi
Gaba dayansu suna zaune a airport din Chad suna jiran sunan su Wanda karfe Takwas flight din zai tashi
Xuwa kasa Mai tsarki

Suna zaune aka fara Kiran sunan su daya Bayan daya
8 dots suka tashi

......... 

Bari muji halin da Yusrah take ciki bayan tafiyar su Minal

Yusrah dai tun Daren farko take jiran Sadeeq ya shigo dakin ta Amma shiro babu shi babu alamarsa tsawon sati daya
Harya Kai ga ta kasa hakuri
Taje ta iske shi part din Minal
Tai mashi tatas

Shiko yai banxa da ita
Tana gamawa yace
Insallameki kikace idan bana sonki Koh

To karki damu kijira dawowar mu xakiga sallama kinji

Sai Kuma tahau kuka tana cewa ita batana nufin ya sake ta
Ta hau magiya tana bashi hakuri
Shigo Daya gaji ya tashi ya barmata parlon

Ranar da xasu tafi
Har sun Shiga mota sai gata ta fito da shirinta Wai xata bisu
Yace aa babu kyau atafi abar gida babu kowa
Don Haka ta koma ciki idan ya dawo xai sakeyin wani tafiyar da ita

Ranar taci kuka ta Kira Salma
Salma taxo tana ta tausan ta
Hakan Kuma ta cigaba da Bata muguwar shawara

Wanda sun anso wani magani
Kusan Kashi uku
Daya suka birne a kofar dakin Minal
Daya Yusrah xatai abinci takai wa Sadeeq ran da ya dawo yaci
Daya Kuma xata yi hayaki dashi
Wai daxaran ya shaki hayakin xaiji Duk duniya babu kamarta

Suna ta hada plan yadda abin xai kasance
Maman ta Bata san abinda take aikatawa ba
..............

Ikleemah taxo wajan Mamie
Tana Mai fada Mata cewa
Najmah baxata taba sanin ko waye ubanta ba saboda Babban soja ne.....Taya ma xa'a barta ta ganshi

Tunda na tafi kasar waje na fara Binciken mahaifin Najmah
Kuma sai da naganshi

Nayi kokarin auranshi Amma Allah Bai nufa ba
Shiyasa abin yamin xafi na dau Alwashin sai na Fadi ma Najmah komai game da rayuwarta

Hmm ikleemah kenan kinyi abinda kike so ai kinji dadi Koh
To meyasa kikace mijina shine mahaifin Najmah

Ikleemah ta yi wata irin dariya wacce ta tsorata Mamie sosai
Sannan tace

Mamie na Dade Ina son auran Mai kudi
Amma tun Ina karaama na kamu da son mijin ki Mamie
Na bibiyi rayuwarshi ya fi akirga
Naso ace ko so daya nee ya kwanta Dani don na haihu dashi Koda shege xamu haifa

Mamie Tai saurin dagowa tace ikleemah anya kina tsoron ubangijinki

Wata Dariyar ta sake yi sannan tace
Mamie ki godewa Allah
Kin kubuta daga hannuna amma abubuwan dana shirya akanki suna dayawa Kuma Allah Bai bani nasaran aikina ba

Mamie ta Dan nemi waje ta jingina da bango Jin abinda ya fi karfinta

............

DielaIbrahim ✍️
Vote and Share
Pls 🙏




BETWEEN US ✔Where stories live. Discover now